39&40
https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
AHALINA
(Siblings of different fathers)
Book 2 in Aure uki series
By chuchujay
Episode 3⃣9⃣➡4⃣0⃣
Bayan isar Nameer ya aje Sultan a gida kai tsaye gida ya nufa dan ya gaji so yake kawai ya huta dan haka ya barwa Fadil meeting ɗin da zasuyi yaje a maimakon sa,
Key yasa ya buɗe gidan ya shiga , a falo ya tarar da Jamaimah tana cin fried rice &chicken da coke a gefenta tana wani yumm kamar an bata duniya,sallama yayi bata amsa ba dan haka ya wuce
Ganin ya wuce ta ɗinne ya sakata ɗan daga murya tace "tunda ance idan na fita Allah ya isa kaga ai mai kuɗi da kuɗinsa sai abunda yayi niyyah idan kuma yin order tazo har gida itama haramun ne sai a faɗa mun naji ya sheik".
Tsintar kansa yayi da murmusawa ,yasani dama za'azo nan da zata fara online order shiyasa koda Nadiya ta faɗa masa plan ɗinta ya amince babu bata lokaci,
Yana ƙokarin kulle ƙofarsa ta sako ƙafa a bakin kofar,matsawa yayi da ya fahimci jidali take ji dashi.
Shiigowa tayI ciki tace "malam magana nake maka tun jiya amma ka kasa bani amsa,"mene ya saka Nadiya tazo tayi abunda tayi mun jiya,"
Walk in closet ɗinsa ya faɗa yana ignoring ɗinta,
Binsa tayi tana cewa "wai Nameer nikam mai ka ɗauki Aure ne ?"
Why are you treating me this way for crying out loud .
ba tare da ya juyoba ya fara cire rigarsa yace yarda kika ɗauki Aure haka na Ɗaukesa jamaimah,sannan duk yarda kika shirya tafiyar da rayuwar Auren mu haka zan tafiyar dake na tayaki ta yarda kike so,
Takawa tayi garesa a hankali ta saka hannunta tayi hugging ɗinsa ta baya,baki ɗaya yaji wani tunani nasa ya tsaya,
Lafar da kanta tayi a bayan nasa tace"Baby dan Allah mu daina azabtar da rayuwarmu, lets live a peaceful life style ,im hurting bana jin daɗin abunda ke faruwa tsakani na da kai,har wani na shiga,sannan Bazan boye maka ba banji dadin abunda Nadiya tazo tayi mun ba wanda na tabbata da sanenka domin idan babu ba yarda za'ayi tazo tayi girki a cikin gidana domin kai sannan wai tace ta aje mun ƙanzo da wuya,imagine babe,sannan har tana faɗa mun zakayi Aure which idan kayi Aure zan iya rasa rayuwata saboda tunanin haɗaka da wata ƴa mace kawai yana sani shiga tashin hankali,"
Cikin shesheƙar kuka tace"is it a crime dan ban iya giriki ba?
Mata nawa ne basu iya girki ba kuma suke zaune cikin gidajensu da mazajensu cikin soyayya da ƙauna,
Wallahi Nameer ina Mutuwar sanka ,ina maka sanda bana yiwa kaina shi why wont you give us a chance?"
A hankali yake jin kukan nata yana ratsa dukkan wani sashe na jikinsa,jikinsa da ta ƙwanta kuma ji yake kamar ana hura masa wuta a dukkanin jikinsa,tabbas yana san jamaima shima ya sani kuma ya yarda amma bazai iya dealing da yarda take tafiyar da rayuwarta cikin rashin biyayya ba da sanin ya kamata ga ɗan adam,
A barshi ace ya amince da rashin iya girkinta ,zasu dawama ne a cin abinci a waje domin bama ta da niyar koya ,ko kuwa zasu ƙare a yan aikine,
Shin yan aiki ne zasu na kula da ɗakinsa su gyara masa har abada?
A tunaninsa ɗakinsa sirrinsa ne wanda matarsa kawai ya hallartarwa,ko kuwa zasu zauna a haka ne bata ganin mutunci da girman danginsa duk a sunan ita ɗiyar sarautace shin ita sarautar hauka ce?
Kukan nata bai daina sauti ba ,ajiyar zuciya yayi ya juyota tana kallansa ya kamo hannunta a hankali ya zaunar da ita kan couch din dake cikin gurin ya ɗuka gabanta ,hannunsa yasa a hankali yana mai share yar ƙwallar dake idanun ta yace"menene na kukan kuma?"
Duk fa abunnan bai kai ga nayin kuka ba,look jamaima i want a romantic simple life with my wife,ni da kika kalleni a tsari na babu Auren mace biyu saboda babu yarda za'ayi na haɗa sansu guri daya nayi adalci saboda nasan kaina,so i choose you duk da Aurenmu was nothing close to okay amma a haka nake san ɗaukan responsibility ɗina na kula da dukka hakkinki da Allah ya dora mun amma baki san bani dama domin kuwa a hadurwaki ta farko da iyayena kin basu expression a kanki mara dadi wanda yayi leading da ni kaina aka koreni daga gida ke shaida ce,
Im a family man jamaimah AHALINA suna gaba min da komai sannan a shirye nake na bata da duk wani wanda zai kawo mun matsala cikinsu,
Ni dake ba soyayya mukayi a baya ba mun tsinci kanmu ne kawai a cikin san juna bayan wannan abun na Aure ya faru.
Cikin shagwaba ta katsesa tace "sai dai idan kai amma nikam i loved you since day one,idan ba haka ba taya zan involving kaina a komai so don't speak for me".
Murmushi yayi ganin yarda ta wani shagawabe fuska yace "to naji i wont speak for you, amma ki sani ina sanki sosai amma kina san bani matsala wajen nuna miki ina sanki,so na kike yi amma baki san ni wanene ba,AHALINA nada tarihi da history wanda bazaki taba tsammani ba,na tabbata a maganar da nake baki san ina da kanne yan uku a America ba sanann baki san cewa ni dasu da Nadiya da Abdallah dukkan mu Siblings ne daga different fathers amma same mother,amma still we fight for each other and love each other ,i love them da dukkan rayuwata,
Sannan aje kan Mami na ,itace komai Nawa,ita ta bani uba a lokacin da nake mutukar bukatar daya wanda shine Papa mijinta a yanzu,ya bamu rayuwa mai kyau sannan yabada babbar gudunmawa wajen ganin mun zama abunda muka zama yanzu ,badan kuɗi ba saboda muna dashi,dangin mahifiyarmu kuɗi ne haka zalika mahaifiyarmu kuɗice amma ya bamu gudunmawar da kuɗi bazasu bamu ba,
Ko kinsan mahaifina dana Nadiya suna nan a raye?
Amma mene amfanin rayuwarsu garemu bayan munada wanda yafiso sau dubu wanda a koda yaushe zai zabemu sau babu iyaka ya bamu gudunmawa rayuwa kamar yarda yake kan bamu,
Tayaya kike tunanin zan zauna na kalle ki kina disrespecting ɗinsu?
Abun da kikayi ranar was awful and very bad .
I can help you wejen ganin kin iya duk wani abu da baki iya ba amma fa sai kin taimakeni tukkuna kin taimaki kanki zan iya taimaka miki ,muyi rayuwa mai kyau da inganci abun sha'awa ga kowa.
Narai narai haka idanunta ke kallan nasa kana ta sake damƙe hannunsa tace "da gaske nake bazan iya rayuwa babu kai ba and tunanin wata mace tare da kai yana sani cikin mutuƙar tashin hankali domin duk ranar da ka kawo wata cikin gidan nan matsayin matarka to zan mutu ne,mai zai saka bazamuyi rayuwarmu daga ni sai kai,i left everything for you cant you do the same for me?
Bazaka iya mun hakan ba please honey,i will try and adjust naga na fara yi maka girki koda ba daɗi a haka har ya fara yin daɗi,rayuwata tunda aka haifeni bayan iyayena babu wanda nake ma kallan sama cos ina kallansa matsayin ƙasƙanci a haka aka raine ni wanda bana tunanin zan iya chanzawa zuwa wata daban,abu daya na sani shine ina mutuƙar maka soyayyar da zan iya saudaukar da kaina domin kai amma bazan iya chanza kaina ba ,kazo muyi rayuwarmu mu biyu please".
Bai san lokacin da wata dariya ta ƙwace masa ba ,sai da yayi mai isarsa ya dago yaga tana kallansa cike da confusion ,baki iya wa kowa kallan sama ba ,ni ma kenan bazaki taba iya mun kallan sama dake ba right?
Snipping tayi tace "ni da kai ai abu guda ne"
Tashi tsaye yayi yana kaɗa kansa yace "yanzu na ƙara tabbatar da baki da ilimin addini isashe,"
Magana kuma dake muddin baki fahimci wadda namiki yanzu ba bata da amfani,
Rigarsa mara nauyi ya ɗauko da sweat pants ya kalleta yace "ki shirya zama da kishiya dan bazan taba iya zama da jahilar mace ba Ita kaɗai ,sannan kuma ki sani kina nan matsayin matata amma baki da wata power akaina domin bazan taba kusantar mace kamarki ba saboda ina gudu da takaicin haɗa zuria da wadda bata san menene Biyayya ba."
Yana ƙai karshen zancensa ya fita yabarta nan zaune maganar tayi mugun dukanta musamman maganarsa ta ƙarshe da kuma kiran ta jahila da yayi .
Wani irin ihu ta saka wanda yana bayi yana jinta ,rufe idanunsa yayi ruwan dumin na ratsa ko ina na jikinsa ,a haka ya jiyo fitarta ta hanyar buga ƙofarsa da tayi tana kuka.
***************************
Kai tsaye Nadiya na ganin message ɗin Evans ta fara kiran layinsa wanda har ta katse bai ɗauka ba,sai da ta kirasa a karo na biyu kana aka ɗauka wanda ta tsinkayi muryar mace tana mai faɗin"come to SAMMY GUEST PALACE ,im Evans mom and i wanna see you right now ".
Da mamaki Nadiya ta cire wayan a kunneta kana ta sake mayarwa tace"is everything okay Ma?"
Cikin yanayi wanda Nadiya bazata fassara ha tace"its not,room 2009 is the room number"
Dit taji an kashe wayar,
Wata zuciyar ke gargadinta da kar taje,har fara tafiyarta inda tayi niyyan zuwa kuma taga ƙin amsa kiran nata kamar wulaƙanci ne da kuma rashin girmamawa gareta dan haka ta tura Abdallah saƙo kamar haka"na tafi Sammy guest palace,incase kunji ban dawo gida ba har gobe something is wrong,dont call me yanzun"
Yar dariya tayi da tayi realizing abunda ta yi,
Amma ai gaskiyarta ne cos tone din matar was not pleasing sannan bata santa ba bata kuma san menene zata iya yimata ba,sanin ƙabilancinsu yasa haka,
Juya kan motarta ta tayi dan amsa kiran,mintuna marasa yawa ne suka kaita hotel din,ta jima a parking lodge tana Sake sake kafun taf addua ta fito domin shiga ciki,ta dai san komene baza'a kashe ta ba.
Tsaye take bakin kofar tana mai danna door bell,
Sai da tayi sau uku kana akazo aka buɗe mata,da mamaki Evans yake kallanta jikinsa sanye da rigar da buttons ɗinsu ke bude wanda ta bayyana shafaffan cikisa mai ɗauke da 6 packs, hannunsa kuma ɗauke da towel yan goge jiƙaƙen kansa wanda hakan ya tabbatar mata da ya fitone a wanka,
Cike da mamaki da kuma alamar tambaya yace "babe?"
Saurin ɗauke idanunta tayi ta juya masa baya tana mai fadin"im sorry and mene zaka buɗe kofa jikinka a buɗe?
Idan kuma bani bace bafa?
Murmushi yayi inda yana ƙokarin magana mahaifiyarsa ta jawosa baya tana mai faɗin"i can see someone is jealous,welcome"
Dam gabanta ya faɗi,da sauri ta juyo inda idanunta suka sauka kanta ,dattijuwace amma hakan bai hana kyanta fitowa sosai ba sanann uwa uba haskenta wanda baya da alamar disashewa ,cike da dan duburburcewa Nadiya tace"Good afternoon ma".
Kallanta tayi da kyau kana tace "its evening come inside".
Riƙota Evans yayi yace "mommy please why do you call Nadiya here i thought we talked about this?"
Cikin inyamiranci tace"bazan iya jira har sai ta bamu izini ba,na kosa naga wadda take da guts ɗin da ya saka yarona yayi converting ba tare da kiftawar ido ba,"
Cikin rashin sanin abunda suke faɗi Nadiya tabi bayansu suka shiga ɗakin ,
Alamu mommyn tayima Nadiya akan ta zauna kan couch wamda babu musu ta zauna tana ɗari ɗari yayinda cikin yare tace"kai kuma zaka rufe kirjinka ne ko sai ka gama hargitsa mata tunanin?"
Sosa kansa yayi kana ya fara balle maballansa,
Sake gaidata Nadiya tayi yayinda ita kuma take binta da ido kamar zata cinyeta,
Cikin harshen turanci tace mata "shekarar ki nawa".
Cike da girmamawa Nadiya tace"29"
Ɗan bude baki mommy tayi tace"bana san wasa 29?"
Ƙasa Nadiya tayi da kai tace yes ma"
Da mamaki ta sake kallanta kana tace zaki iya haihuwa kuwa?
Da sauri Evans yazo ya zauna kusa da ita yace mommy mana?
Wani irin kallo ta bashi kana tace"bana so fa ,kar ka shiga mun,bansan mene yanayi na haihuwa hausawa ba amma ni nasan yarinya yar yarenmu idan takai 29 ana kwana biyu kan tayi ciki shi yasa muke gwadawa tukkuna,inajin wannan ma sai mun gwada."
Dariya Evans yasa yace mommy mu musulmai ne and sex kafun Aure haramune ,
Wani banzan kallo ta bashi tana mai faɗin kar ka fara mun maganar musulinci kafin kashiga kai Christian ne and babu laifi idan zaka gwada ne kaga matar da zaka Aura zata iya haihuwa ne ko kuwa bazata iya ba ba haramci a al'adarmu.
Ɗan ƙaramun murmushi Nadiya tayi da ya zamana ba da yare suke maganar ba,cikin rashin san tafaɗi maganar da bazata ma mommyn dadi ba tace"mahaifiyata ta sake Aure tana da shekara 29 amma shekaran da ya zagayo ta haifi yan uku."
Da mamaki mommy tace "yan uku?"
Washe baki tayi tace"kilan kema ki haifa wa Evans so ke virgin ce"?
Sake kama hannunta Evans yayi yace"mommy ki bari mana its embarrassing."
Hannun nasa ta ture tace biko rabu dani,ina so na san wane yarona zai Aura,
Cike da kunya Nadiya tace"im a virgin mommy".
Kaɗa kai tayi tace ina zuwa,
Tana tashi Evans ya sauko a akan gadon da suke zaune yazo inda Nadiya take yace "Nady baby im sorry about this please,mommy mean no harm".
Ɗan yake tayi tace "ba damuwa Evans im good"
Zai sake magana sai ga mommy nan da tape dinta tace "oya tashi,"
Da mamaki dukkansu suka kalleta,takowa tayi ko ajikinta ta janye gyalen Nadiya wanda tazo mata a bazata,
Evans zai magana tace"ka koma ka zauna kafun raina ya baci da kai,inayin komai ne dominka,"
Tape ɗin ta bude taje daidai kan Duwawun Nadiya ta saka tape ɗin tana mai fadin "zan Auna girmansa ne naga zaki samu ciki da wuri sannan zakiyi qualities din da igbo girls suke dashi,zaki iya ɗaukar bukatun Igbo man,".
Cike da rashin jin daɗi Evans yace "im Ghanian for God sake ba inyamiri ba".
Dakuwa tayi masa da hannu tace "amma ai kasha nonon igbo woman bazakuma ka ƙaryarta hakan ba"
Janye tape din tayi tana mai kallan measurement ɗIn kana ta saka hannu ta kamo duwawun tace hope baki saka ciko ba,
Ɗan ja da baya Nadiya tayi a ranta tana mai mutuƙar rashin jin dadin wanann iskancin amma ta danne tace "No mommy ban saka ba and boobs size ɗina 37 ba sai kin Auna ba i mean it".
Dan kallanta mommy tayi tace "i know you're not happy with me ,nasan baki jin dadin abunda nake maki amma a matsayin uwa dole na damu musamman da ya zamana soyayyarki nada farashi,har yanzu na kasa yarda SABODA ke Evans ya karbi musulinci,ina sone kawai nasan kina masa san da yake maki"
Da mamaki Nadiya ta kallesa domin ba faɗa mata ba ,kaɗa mata kai yayi wanda lokaci daya taji hawaye na bi mata kuncita,saurin gogewa tayi ta kallesa cikin harshen hausa tace "dan me ka karbi shahada"
Sanin bata san mahaifiyasa ta fahimci mai suke fadi ne ya saka cikin hausan yace"domin na yarda kuma na gamsu shine addini na gaskiya,sannan soyyarki ta sake bani kwarin gwiwa wajen yin hakan."
Faɗaɗa murmushi ta tayi tace "mene sunan ka,"
Licking lips dinsa yayi yace "ke na ajewa wannan gurbin".
Murmushi tayi sosai kana tace"AHMED"the praised sunnan Annabi Muhammad,first person to present imperfect!
And na shirya Aurenka a ko yaushe ,indai ina numfashi babu wani ɗa namiji da zan mallakawa soyayyata bayankai,wannan alkwarine daga musulmar da ta saka ka fara shawa'awar musulunci har ka samu shiga.
Gyaran murya Mommy tayi tace"meke faruwa dai?"
Baki ɗaya ma Nadiya ta manta da ita,
Goge hawayenta tayi ta rugume Mommy babu zato babu tsammani tace"mommy i love your son with every fibre in me and i promise to treat him like a king and insha Allahu i will give him beautiful kids insha Allah ."
Da gudu ta juya tabar ɗakin.
Kallan kofar tayi kana ta kalli Evans tace"kai mai kukace da wancan yaran and mai ya shigeta".
Daga kafaɗarsa yayi ya mara mata baya yana dariya.
School dey give me woto woto kuyi hakuri oo,weeks to exams,kuna ɗagan ƙafa na zama yar jaridar nan already mu huta.
Xx
Chuchujay✍🏽
TBC
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top