page8
ABLA ADNAN
NA
CHUCHUJAY
PAID BOOK
FREE PAGE
8
.....Cikin wani tashin hankali Salees Ya zauna kan kujerarsa inda matarsa hajiya bilki ta kallesa cike da fitsara tace,'Ai muddin mutum yace bazai zuge tazugenshi da kyau ba to abu irin haka yanzu Ya fara arba da barazana ,
Na gaji da bi takan kazantar ka ina dannewa ina shiru ,kasan nafi kowa sanin halin ka tunda muma ta hanyar da muka haɗu kenan Sannan nasan matar nan ba karya take ba wannan shegiyar yarinyar taka ce saboda ga jini,
Amma kasani ni Babu abunda Ya dameni,inaso a shafe su sannan a goge babin su daga doran kasa saboda wannan tsinanniyar yarinyar daga gani kasan idanunta mitsiyatane ,sannan kalamanta Babu alamun ja da baya.
Tana kai karshen zancenta ta fice a office din ranta a bace ,
Wata irin ajiyar zuciya Alhaji salees ya sauke,
A rayuwarsa Ya dauki advantage na yara mata da dama wanda Babu wanda Ya bayyana a rayuwarsa face Maimuna,
Ya dauki maimuna kamar ko wacce mace da zai huta da ita bayan Ya gama kuma Ya watsar,a lokacin da ta kawo masa maganar tana da ciki Ya tsorata saboda a duk barikin sa da ita ne kawai baya saka protection saboda Maimuna ta daban ce ,Ya nemi ta zubar da ciki a lokacin da ta kawo masa maganar saboda Bayasan mahaifinsa Ya tsinci labari saboda ba karamun mutum ne da baya san mutuncinsa da kimar sa su zube,
Sanin Maimuna ɗanyan kai ce yasa Ya gudu daga garin baki ɗaya sabida gudun karta basa matsala,bayan komawarsa gida ya haɗu da bilki wadda take killaliyar yar duniya,mahaifinta babban Mai kuɗi ne wanda yake abokin cinikaiyya da mahaifinsa, a lokacin da salees Ya latsa yaji bilki yar hannu ce sai suka kulla alakarsu ta bariki wadda tayi masa dabaibayi dan har ga Allah bashi da niyyar auren ta amma saboda wata samuwa ta iyayensu aka haɗa auren su akan igiyar kasuwanci ,Bayan auren su suka azurta da yara mata uku,xixi,hanifa,da naima.
Bayan rasuwar mahaifin sa Ya gaji babban kamfanin sa dake cikin garin ibadan na auduga wanda cikin hikima da taimakon Allah yake ta habaka ,yana da komai najin daɗin rayuwa da yake bukata amma samun ɗa namiji Ya zamar masa larura ,
Kamar yarda hajiya bilki ta faɗa tabbas a cikin idanun ABLA Ya hango fansa Mai zafi wadda idan baiyyi wasa ba zata konasa ,dole ne Ya dauki babban mataki a akan su,
Wayar sa Ya ciro Ya kira wani yaran sa Ya tura masa Numbern hajiya maimuna yace yana so a yi tracking layin ta a gano masa location dinta sannan a tura yara biyar gidan su gama da ita da duk wani dake cikin gidan.
°°°°°°°°°
.....Bangaren Abla kuwa Suna fitowa a ofishin tayi gaba tana Mai sharar kwallar bakin ciki,hannunta mamanta ta kamo a lokacin da suka zo harabar company din,
Kallan hannun tayi sannan ta kalle ta tace 'mama ki sake mun hannuna kawai,tunda kika haifeni babu rana ɗaya da kika taba nuna min soyayya irin ta uwa da ƴa,illa kiyayyar da ban san hawan ta ba ban san saukan ta ba,menene laipina ?
A cikin dukkan al'amarin nan fa laifin ki yafi na kowa yawa to ni menene nawa,a koda yaushe baki da buri illa ki ga rayuwa ta ta salwanta,haba mama ke fa kika haifeni ,kika dauki cikina na wata tara kika zo kika haifeni sannan kice a zuciyarki bani da wani gurbi ko dai dai da miskala zarratin haba mama,a kullum baki missing damar kirana shegiya wanda a yau ma da nake bukatarki fiye da kowa saida kika kirani shegiya ,amma shikenan mama, tunda mama zinaru ta rasu dama na saka araina bani da kowa sai ni kaɗai ,sannan mama zaki gani sai na zama abun kwatance ,sannan sai na tarwatsa dukkan wani farin ciki dake cikin rayuwar Alhaji salisu Mai kamfanin audiga da yardar Allah ,muddin ina numfashi kuwa.
Tana kai karshen maganarta ta fice a gurin ba tare da ta damu da kiran sunanta da mamanata take ba.
A haka hajiya maimuna taje gida zuciyarta dauke da sabon dafi wanda yake zuciyarta shekara da shekaru,tabbas tanajin soyayyar ABLA amma bata tunanin kwadayi da san abun duniya zai barta ta nuna mata soyayyarta domin itama akan wannan tafarkin ta tashi,duk da abunda Ya faru a yau Ya taba mata wata zuciya sosai,
Tana jin sallama take dauka ABLA ce amma shiru har akayi sallar la'asar,ba ABLA ta dawo gida ba sai bayan sallar magreb,
A compound dinsu ta tarar da ashana tare da wani saurayi wanda bata taba ganinsa ba a duk tarin samarinta ,tana jin tana mata magana amma ta share ta ta wuce cikin gidan ,
Tana shiga hajiya maimuna ta taso tana mai faɗin Abla daga ina kike?
Kallanta tayi tace 'naje lake ne ,akwai abinci ?
Tayi mamakin jin tambayar da ABLA ta mata 'dan ABLA ba wani fiya cin abincin gidan tayi ba,
Da saurinta tace mata "akwai gashi chan nayi faten arish da kifi dama ke na aje ma "
Murmushi Abla tayi tace bari nayi wanka nayi sallah sai nazo naci,
Kai tsaye ta wuce ɗakinta ,
Bayan wasu mintuna ta fito jikinta sanye da rigar bacci iya gwiwa kanta sanye da hula,
Kan dining ta nufa dan bama cikinta abinci,
Plate ta jawo ta zuba abincin a ciki tasa spoon ta fara ci bayan tayi bismillah,
Dago kanta tayi ta kalli mahaifiyarta da ta zauna a chair din dake kallan nata ,murmushi tayi mata wanda yake damun hajiya Maimuna dan tasan akwai wani abu karkashin wannan murmushin,tana tsoran kar tasa kanta cikin matsala itama ta jawo mata,
Cigaba da taunar abincinta tayi bayan ta hadiye ta kalleta tace"mama kar ki damu bazan baki matsala ba ,sannan zaki samu kuɗi a al'amarin da nasa gaba,nasan burinki kuɗin kuma zaki samu insha Allahu."
Shiru mama tayi dan bata san Mai zata cema ABLA ba idan tayi kokarin buɗe bakinta dan yin magana.
Abun Ya bama kowa mamaki ganin yarda ABLA ta zauna a falo tana kallo tare da kowa,
Ba ita ta tashi ba sai guraren karfe goma na dare kan ta musu sallama ta wuce ɗakinta dan kwanciya.
CHUCHUJAY
08130229878
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top