page 9

ABLA ADNAN

PAID BOOK

NA

CHUCHUJAY.

Normal group 400N,

One PAGE Mon-fri

Vip700N

2pages per day mon-sat

0264267657

Gtbank

Amina jamil adam

Shaidar biya ta whatsapp

a 09058191213.

FREE PAGE

9.

Wuraren karfe daya na dare tana kwance taji hayaniya a harabar gidan su kasancewar window ɗin ɗakinta yana ta harabar gida,

Kasaƙ tayi a lokacin da taji ɗaya daga cikinsu Na faɗin "Alhaji muna cikin gidan Sannan  kana daf da jin labari Mai daɗi dan duk wanda ke cikin gidan nan sai ya mutu yau,"Wani ras gaban ta Ya faɗi ,ko kaffara ba zatayi ba tasan Alhaji salees Ya aiko masu da yan daba,a hankali ta koma ta zauna tama rasa mai zatayi,

Wani police dake  santa ta tuna and tasan shine kaɗai zai taimakesu a yanzu domin station dinsu nan kasa take ba nisa ,ringing daya Ya dauka ,a hankali tayi sallama inda ta katsesa daga kirarin da yake mata,.

    Tana jin shigowar su main falon da suka balle kofa cikinta ya kara kugi ,

Dakin hajiya Maimuna suka fara shiga wadda tana tsaka da bacci taji saukar kulki a kanta,

A zabure ta miki ganin mutane masu fuskoki a rufe a kanta,da duka suka rakata falo dan ga order na Alhaji yace a musu dukan da sai sun daina motsi kafun a kaisu har lahira,

Bayan fitowa da ashana da yar gwal ne ogansu Ya kalle su yace "dan ubanku wacece Abla a cikin ku,"

Da sauri yar gwal tace tana ɗakinta wallahi,

Ba gida zata kwana ba "hajiya maimuna takara tana Mai rawar jiki"

Wani mari mai kyau ogan Ya kwashe ta dashi kafun yamaimaita cikin fushi ,wacece ABLA ?

Ƴatace 'hajiya Maimuna ta faɗa a tsorace.

Zumbur yar gwal ta miƙe tana Mai faɗin,oga muje na kaika ɗakinta ,

Gaba yar gwal tayi ogan yana biye da ita a baya har bakin kofar dakin Abla wadda dama siyan lokaci ya hanata fitowa dan inspector sadiq Ya faɗa mata yana nan zuwa ta tayashi siyan lokaci,

Jin muryar ogan tayi inda yake faɗin ,Abla kafun na irga goma ki buɗe kofar nan ,idan kuwa ba haka ba ,zaki dauki gawar babarki a hannu.

Key din daƙin ta murɗa ta fito tana Mai faɗin ba ma sai ka irga goma ba,

Batayi aune ba Ya ɗauke ta da mari wanda sai da yasata tuntsurawa ,

Dafe kuncinta tayi tana Mai kallansa kafun tayi wani murmushi wanda Ya kara harzuƙasa Ya watsar da ita kan kujera yana Mai balle belt ɗinsa yana faɗin ,bari na fara yi miki fyaɗe tukunna in yaso na kasheki yarda zaki mutu cikin bakin ciki tunda dama anyways dole ki mutu,beside Babu wanda zai rayu cikin gidannan,ba wai munzo ɗan wani gold ,kuɗi ko diamond ba ,munzone dan rayuwarku .

    Wata irin dariya Abla ta kece da ita wadda ta shammaci kowa,kallan belt dinsa da Ya fara ballewa tayi tasa hannu ta janyeta baki ɗaya tace 'hala wanda ya baka kontargin kashe mu bai faɗa maka nan gidan masu zaman Kansu bane ,to bari na sanar dakai ,ka daina mun baraxa da fyaɗe a kyauta ma idan kane ma zan baka dan dama ina neman abokin mutuwa ne kaga idan ka kasheni kaima zaka biyo ni saboda HIV/AiDs shine karamun ciwon dake jikina ,kar akai gasu STD ni da kaganni nafi miciji dafi,

Kara matsawa gabansa tayi tana Mai wata kwarkwasar da bata san tana da ita ba,

Hankaɗa ta yayi da jaraba yace ,dan ubanki karki tabani,

Karkuzo fara kashe waccan ramamiyar su san da gaske mukai,

Kafun kiftawar ido karkuzo Ya sakarwa ashana bullet a kai wanda a take ta baje bata shura ba,

A tare suka saka ihu ,karma ace yar gwal wadda harda fitsari a jiki,

Zai saki kunamar bundigarsa a karo na biyo ,yan sanda sukai raiding gidan,

    Ku aje makamanku sannan duk abunda kuka faɗa zai iya zama hujja akanku ,you're Under arrest,and ku sani kimanin yan sanda ishirin suna zagaye da gidannan kar wanda yayi kokarin gwada shirme damu domin duk wanda ya gwada zai mutu' muryar inspector sadiq ta karaɗe ɗakin,

Alamu yayi ma ya sanda huɗun da yazo dasu akan su sa musu handcuff,

Ogan nasu ne ya juyo Ya kalli ABLA  Ya nunata da hannunsa sannan Ya nuna idanunsa ,Alamun yana sa mata idanu.

Bata tsaya kulasa ba tayi kan ashana tana Mai jin hawaye na bi mata kunci,inda hajiya da yar gwal suke ta kuka da salati,

Bayan an kama yan ta'addan inspector sadeq Ya tako gurin yana Mai faɗin kuyi hakuri sannan insha Allahu sai na sama mata justice ,

Tashi ABLA tayi tana Mai masa godia yayin da take jin girmansa da kimarsa na kuma karuwa a zuciyarta ,

Ya daɗe yana santa kuma yana bibiyarta amma bata taba bashi dama ba sai sau daya shima dan zai mata amfani wajen kama wani ne,tun fari amfani kawai take dashi wanda gashi a yau dinma amfanin tayi dashi,

Idan har tace zata auri sadeeq shine yaci baya domin shidin mutum ne kamili da Ya Chanchanci mace kamila yar babban gida .

    Hotunan gawar ashana yan sandan suka dauka kafun yabarsu da guda uku su tsaresu kafun safiya.

Suna nan zaune kan gawar ashana wayar daya daga cikin yan ta'adan tayi kara,

Da saurinta ta tashi ta dauki wayan ta kara a kunne,

Muryar Alhaji salees ta tsinta a daya bangaren yana faɗin 'ina fatan aikin Ya kammala?

Tayi zargin shine amma a yanzu ta tabbatar kuma dole zata koya masa hankali ,bazata so yan sanda su kamasa ba saboda bata. ma tunanin zai kamu ,alkawari ta kuma daukawa kanta akan sai ta wulakanta shi sai ta tozartashi.

Kashe wayar tayi ta kai daƙinta ta aje dan zata mata amfani,

Washe gari bayan an haɗa ashana Abla taje nemo masu mata sallah amma kowa sai yace bazai ba ,haka koda taje majalisar da liman ke zama magana dayace wadda ranta ke kufula da ita,

Cike da balai ta kalli magidantan tace "yau Allah yayi ma asiya(sunan ashana na gaskiya) rasuwa amma roƙon ku nazo inayi akan kuzo kuyi mata sallah kun gagara saboda kawai tana zaman kanta,naji nayarda ashana tayi rayuwar da bata kamata ba amma kunsan menene tsakaninta da ubagijinta,

Ta iyu hatta kai liman da kake zaune kake nuna kafi kowa sanin Allah tafika mu'amala Mai kyau da ubangijnta ,ni shaida ce bata taba barin lokacin sallah Ya wuce ta ,wani abu da baku sani ba a kullum sai ta raba dare tana nafila ,azuminan na nafila duk da tana karuwanci bata bari Ya wuce ta duk alhamis da litinin,bata kashe kowa ba ,menene matsalarku, "?

Mutumin daka kusa da liman ta nuna da yatsa tana Mai goge kwallah tace "nan kullum sai kaje siyan doyanta ,ko kana tunanin ban taba ganinka ba ,Mai yasa baka kyamaci abunda take siyarwa ba sai yanzu da tazama gawane ,inace kaima liman kana aikawa a siya maka ,har ji nayi kwanaki kace baka gajiya da doyarta a cikin wannan majalisar",

Nunasu tayi da yatsa baki dayasu tace 'dukkanku munafukai ne,Allah kadai yasan abu mafi muni da kukeyi a bayansa idan kuma ni nafara maku tone tone kowa sai ya gudu.

Bata tsaya jin abunda zasu faɗi ba tabar gurin dan bama ta tunanin akwai abunda zasu faɗa din dan dukkansu basu da shi.

Tayi mamaki ganin tana isa gida liman din Ya taho da zugarsa akan zasu mata sallah su kaita,

Haka nan aka mata sallah wadda yawancin masu siyan doyanta sun hallata kana aka kaita makwancinta,

Dama bata da kowa dan ko da tazo hajiya Maimuna ta dauke ta ta shaida mata ita marainiyace bata da kowa a duniya .

Haka nan shafin Ashana yar rufe wanda Ya firgita hajiya Maimuna sosai.

CHUCHUJAY ✍🏽

08130229878

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top