page 6

ABLA ADNAN
NA
CHUCHUJAY.
Na kuɗine .
Free page
6
Dafe kuncinta tayi tana Mai kallan hajiya kana tace "mari fa."
Ɗan ajiyar zuciya hajiya tayi da ta fuskanci wasa da damarta akan Abla da take shirin yi,
Dafa kafaɗarta tayi tace"look Ably na kiyi hakuri banso marinki da sane na ba,bana san faɗan ku yafi haka ne ,kiyi hakuri,"
Kallanta da kyau Abla tayi kana tayi wani murmushi dan tasan dole akwai abunda take bukata daga gareta ,
Gyara zaman kalbarta da Ya zubo gaba tayi takalli mahaifiyar tata da kyau tace "Mai kike so yau kuma ƴarki jarinki tayi maki mama?"
Murmushi itama tayi dan bata jin wani nauyi ko kunyar Abla wurin nuna mata bukatarta tasan zuciya da ƙwadayi,
Kamo hannunta tayi tace zo zo zauna nan muyi magana,
Zaunar da ita kan kujera tayi tace 'wani deal ne Abla zai yi falling kuma za'a samu kuɗi sosai ke dai kawai ki bani wuƙa da nama sannan ina Mai tabbatar maki da cewa zaki samu kuɗi masu numfashi idan abunnan Ya faɗa,
    Murmushi Abla tayi tasa hannunta ta ɗauke na hajiya daga kan nata a hankali sannan tayi wani murmushi na rainin wayau tace"mama kenan ,na tabbata a baya na faɗa maki ,yes na yarda ni shegiya ce kuma bada aure aka sameni ba ,amma hakan bashi yake nuna zanbi turbar wadda tayi silar shigowata duniya ta kazamiyar hanya ba ,ni ba karuwa bace ,sannan bazan taba neman kuɗi da karuwanci ba,yes Ina san nayi kuɗi amma bata hanyar da kike so ba mama ,dukkan wani kwaɗayi da buri da kika dauka akaina wallahi haƙar bazata taba cimma ruwa ba.
Tashi tayi zata bar gun amma hajiya ta kamo hannunta ta zaunar daita tace "look Ably na zauna nima Ai ba karuwancin zan tura ki ba tuni na fita da wannan tunanin ,wannan wani babban kamun aikine da na maki wanda nasan tabbas yafi inda kike aiki sannan kar ki manta kina bukatar kuɗin makaranta".
    Zurfin tunani Abla tayi ,tabbas tana bukatar kuɗi sannan babu yarda za'ayi mama tasata abunda batayi niyya ba koma menene dan haka tayi wani makirin murmushi tace "shikenan mama bari na kintsa muje."
Wani sanyi taji aranta tana Mai kimanta irin adadin kuɗin da zata samu indai Abla tayi wannan aiki ,sannan tasan Abla zatayi tunda ba abunda ta tsana din bane aikine Mai kyau a tunaninta.
Mintuna kaɗan Abla tafito a ɗaki da kcn gyalenta wanda ta yafasa iya kai,hannunta kuma dauke da karamar purse inda bakinta yasha jan janbaki wanda signature dinta kenan a kullum,sai kafarta dauke da flat shoe.
Wani irin murmushi hajiya Maimuna tayi tare da tafa hannayenta biyu tace "woo ni maimuna shegiya ma na haifa da kyau inaga na halak,
Murmushin yake Abla tayi kana tace"zamuje ɗinne ko na tsaya ki kara tuna mun shegiyace ni."
"A'a muje yar mama".
Gaba hajiya Maimuna tayi abla na binta a baya tana Mai kaɗawa yargwal kugu wadda a da wannan fitar da ita za'ayi amma saboda tsabar san zuciya irin na hajiya ta zabi Abla.
    Da sauri hajiya Maimuna ta zagaya ta buɗema Abla gaban motanta wanda zata iyacewa wannan ne karo na farko da zata fara shiga ,
Dan Murmushin gefen baki tayi tashiga bakinta dauke da bismillah wanda yake sabonta a duk abunda zatayi,
Tunda hajiya ta fara tuki Take jan Abla da wasu labaru wanda bama ta gane inda ta dosa illa abu daya da take hangowa a Al'amarin mahaifiyar tata wato fake concern,
Jin adadin surutun Ya dameta ne yasa tace "mama we both know better,kinsan hira tsakanin ƴa da uwa ba namu bane so mudaina pretending ,,its business so please lets mean business".
Babu wanda Ya kuma cewa komai har suka isa wani babban building na company ,dan tabe baki Abla tayi dan bata taba tunanin wai akwai ranar da mamanta zata sama mata clean aiki ba ,
Daga kai tayi bayan fitowanta a motan taga sunan company din a rubuce "S'S WOOL COMPANY "
Kallan hajiya tayi tace"kamfanin auduga?"
Kaɗa kai mama tayi alamu Eh kana tace maza muje nasan yanzu wanda zasu baki aikin sunzo,
Babu musu ta bita tana Mai faɗin 'kin sansu ke nan,
"Inafa ,wata ƙawata ce tasansu saboda matar mutumin kawarta ce so shine ta haɗa ni da mutumin a whatsapp muka gama komai "mama ta bata amsa.
Babu wanda Ya kuma cewa koma har sukaje reception.
Mama ce tayi gaba ta gaisa da receptionist ɗin inda take faɗa mata tazo gun president na company ɗin,
Wani kallo tama hajiya Maimuna,duk da kuwa shigar keca raini ke jikinta amma tayi mamaki da tace kai tsaye President zata gani,
Sake gyara glasses receptionist ɗin tayi tace "madam you're talking about the owner of this company fa " .
Jin rainin wayau a maganarta yasa Abla matsowa kusa tace "yes sweety guess you are not deaf,we are talking about him not your father".
Wani kallan banza tama Abla, tana Mai kokarin magana amma Abla ta katseta ta hanyar dukan table ɗinta tace "abegi hold it there just give the man a fucking call mama inace yasan da zuwanki?
Kwarai kirasa kice hajiya Maimuna.
    Kallan gurin Abla take cikin nutsuwa a lokacin da aka musu iso zuwa inda office ɗin da zasu samesa yake,
Nervously Abla take rubbing palms dinta Cos she cant blv wai yau itace zata yi aiki a wannan ka tafaren company din wanda in her wildest dream ma a wannan karnin bata taba tunanin zata samu aiki anan ba .
Bayan shingansu office din "wata hamshakiyar mata suka tarar zaune tana taunar chew gum"Kallo ɗaya zaka mata kasan kuɗi Ya zauna sannan an buga bariki koma ana kan buga ta,fatar nan tasha bleaching wanda ba dan kuɗi ba bazata ganu ba,
A sahu na masu kyau za'a sata a tsakiya ,hancinta dauke yake da bulin hanci gefe da gefe wanda tabi da pins,
Kitson kalba na attach  dake kanta ya zubo yana reto ciki kalar ja inda kafafunta ke sanye da gold anklet da toe ring .
wani kallo abla ke binta dashi a ranta tana tunanin" dama za'asamu macen da tafi mamanta bariki,domin wannan matar ta ko ina ta kera hajiya maimuna ,kyawu ne  kawai zata nuna mata ,dariya ce ta kwace ma Abla wadda ta jawo hankalin matar kanta.
Tashi tsaye matar tayi tana mai takowa garesu da rangwaɗa ,
Zagaye Abla tayi da kyau tana Mai bin kirar jikinta da kallo kana ta kalli hajiya Maimuna tace "ƴar ce zatayi aikin ko uwar?"
    Haɗiyar yawo hajiya Maimuna tayi tana Mai san saita fushin ta duba da irin rainin wayan da ta tsinta cikin muryar matar,"ƴar ce  ,sannan idan zan tuna da namiji nayi magana ba da mace ba ,ko yana ina".?
Wani murmushi Mai sauti matar tayi tace "sure 'haka ne"
Komawa tayi mazauninta ta zauna tace"bismillah ku zauna ku bashi mintuna kaɗan yana zuwa".
Babu musu suka zauna kowa da abunda yake saƙawa inda matar ta zuba ma Abla idanu wanda yafara damun Abla ,
Tana kokarin faɗa mata na cikinta sukaji sallamar mutumin wanda kamshin turarensa kawai shine abunda Ya fara musu amshi.

CHUCHUJAY✍🏽
08130229878

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top