page 5

ABLA ADNAN.
NA
CHUCHUJAY
NA KUƊI NE.
FREE PAGE
5.
Waige waige ta fara a lokacin da fito ,babu yawaitar mutane a gurin domin ɗai ɗai haka take ganin gilmawarsu ,
Agogon hannunta ta kalla taga har karfe 9 na dare yayi ,ɗan tsaki tayi dan tasan kafin ta samu abun hawa sai ta gangara babban titi saboda gurin yana chan ciki ne,
Tsaye tayi a babban titin tana Mai addua'r Allah Ya cillo mata bike man.
Hasken fitilar motar dake doso ta ne ya kashe mata idanu wanda har sai da yakai ta kulle idanunta ,
Motar har ta gifta ta sai kuma ta dawo da baya ta tsaya dai dai satinta ,
A hankali akayi kasa da glass din motan wanda ko kallon arziki bai samu daga gurin ABLA ba dan a zafin da take ji a kirjinta zata iya zagin Mai motar babu abunda Ya dameta da dare,.
     Yan mata adon gari idan babu ku babu gari Ina zuwa haka da daren nan kyakyawa ?
Wani tsaki wanda ke zaune a mazaunin Mai zaman banza yayi yace"wai shin yusuf mene matsalarka ,wannan wane irin yarfa kaine kai wai babu dama kaga mace?to ka kalla wannan da kyau da kuma inda ka ganta idan junanka kwadayi zaka kai kanka halaka dan wannan kana kallan idanunta bazata rasa mugun ciwo ba,
Ni idan zaka kaini gida ka kaini idan yaso ita karuwar sai ta jiraka kadawo ku jone inba haka ba kuma wallahi Zan maka rashin mutunci.
    Kamar saukar aradu haka ABLA ta tsinci maganar wanda hakan yasata juyawa taga wannan Mai izzar,
Samari ne a cikin motan masu jini a jika ,idanunta ta ɗauke daga wanda taji ankira Yusuf ta dora su kan wanda Ya zageta cikin fushi tace "kar ka manta idan kaje gida ka faɗa ma tsoho bai gama viyana cikon kuɗina ba sanann ka sanar masa shida gyatuma akan suje suyi gwajin sida dan tamun katutu and yauwa ka tabbata ka sake faɗawa tsoho wai nace yanemi maganin basir saboda nan gaba domin Ya cinyesa."
Da wani zafi Ya buɗe murfin motan yayi kanta gadan gadan yana Mai faɗin"the,fuck you just said? Iyayena kike ma wannan ƙazafin Da kazamin bakinki Mai kama Da toilet"let me just teach you a lesson,
Da sauri Yusuf Yayi kansa yariƙe sa yana Mai faɗin calm down man.
Cike Da wata fitsarar ABLA tace"kar ma yayi calm down ɗin mana Idan ya isa namiji kabarsa Ya dakeni,baisan sharrin Abla Adnan ba duk bala'insa na fishi,ashe kazafi ba daɗi Da zaka kalleni da bakinka kamar bakin akuya ka kirani da karuwa ,sakarai kawai.
    Kara harzukasa ta kuma yi musamman da ta kirasa da sakarai ,kokarin kara kwacewa yake inda jijiyoyin kansa baki ɗaya suka tashi yana wani huci,
Sanin idan ya kwace ɗin Abla zata kwashi kashinta a hannu yasa Yusuf sake rikesa gam yana Mai faɗin"kalla Abla dan Allah ki tafi kiyi hakuri".
    Batare da ta damu da irin abnormal abunda yake ba tace "naji yusufa yaci darajarka wallahi daya kwashi kashinsa a hannun ABLA sannan Ina Mai san ka sani ni ba karuwa bace ,and for once learn how to zip your pants na barku lapia , "Har tayi gaba ta juyo tace "Yes make sure ka sake jadada ma zakin nan ya kiyayeni kuma Ya gudu haduwata dashi idanu na ganin ido dan wallahi sai na yagasa naga wanda Ya tsaya masa,"
Tana kai aya ta tare bike man ɗin da Ya doso su,bata wani tsaya faɗan masa inda zata ba ta haye tana Mai faɗin muje.
    Fuzge jikinsa yayi daga na Yusuf da karfi Ya daki motan da karfin gaske kana Ya saka wani irin ihu Mai cin rai, yana Mai faɗin"why Yusuf Mai yasa ka rike ni ,da ka barni na koya mata hankalin da sai dai a kwashe gawanta gobe da safe anan,."
Wani irin abu Ya fara kana Ya kama kansa cikin ciwon ,
Da sauri Yusuf Ya zaga motan Ya dauko wani karamin container na magani Ya buɗe Ya ciro pill Ya mika masa tare da buɗe masa ruwan gora yana Mai faɗin WASEEMUDDIN please ka karba kasha kar ciwanka yayi triggering anan bansan Mai Zan cema Mai Martaba ba idan hakan Ya faru,
Jikinsa na karkarwa yasa hannu ya karba kana Ya taimaka masa Ya shiga motan ,
Sosai Yusuf Ya tsorata sannan yayi nadama danshi ne silar komai da ace ba tsaya ba da yanzu killan Ya dade da kaisa gida,
Kamar yarda Waseem yafaɗa haka Yusuf yake yana da biye biyen mata wanda sauda dama sunkayi faɗa akan hakan amma still Waseem bai watsi dashi ba matsayin babban amininsa ba kuma ɗan uwansa,shikansa Halayyarsa na damunsa amma yayi nisan da Allah ne kawai zai ƙwatosa,
Koda suka isa gida waseem bai ce da Yusuf komai ba illa yanƙinsa da Ya shiga Ya bugo kofar a fuskarsa da karfi wanda hakan Ya tabbatar ma da Yusuf baya da lokacin magana dashi .

    Isar ABLA gida kai tsaye ɗakinta ta shige musamman da taga babu kowa a parlour wanda yake tabbatar mata da akwai waɗanda bazasu kwana gida ba,
Wanka tayi kana tazo ta kwanta tana Mai tarayo abunda Ya sameta a yau ɗinnan she's really unlucky .
    Asubar fari ta miƙe da taimakon kiran sallah da taji a kunneta ,
Bayan ta idar da sallah ta zauna kan abun sallah tafara karatun alqurani cikin murya mai sanyi har gari Ya waye kana ta mike ta gyara daƙinta ta shiga bayi tayo wanka ta fita dan zuwa gun ashana ta damfareta doya ,
A'a yau ba mashayar kenan?
Juyawa tayi ta kalli yargwal wadda ke faman tsantsara kwalliya kamar zata biki,
Kallanta ABLA tayi da kyau yayinda abunda tayi mata jiya Ya fara dawo mata,
Dan murmushi tayi ta shiga kitchen ba tare da tace mata kala ba ,
Container ɗin manja ta dauko tana murmushi ,bata tsaya wani tunani ba ta watsa jikin yargwal wadda ta ci bafu har bafu,
Wani irin ihu yar gwal tasa tana Mai yarda eyepencil din dake hannunta ,
Pouting baki Abla tayi tace"no sweety wannan ihu kamar na watsa maki acid ,manja ne fa Mai sanyi".
Wani kukan kura yar gwal tayi ta chakumo ABLA wanda nan take dambe Ya kaure masu,
Da sauri hajiya wadda taji zage zagensu yayi yawa ta fito tana mai faɗin lafiyar ku kuwa ,
Ganin halin da suke ciki yasata shiga tsakaninsu tana Mai rabasu amma ABLA taki sakin kwalar ta, hannu tasa ta dauketa da mari wanda yasata ganin wuta.

CHUCHUJAY.✍🏽
08130229878

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top