page 2

ABLA ADNAN 2

PAID NOVEL
NA
CHUCHUJAY.
WATTPAD AC:CHUCHUJAY.

FREE PAGE.
2
Asalin su abla mutanen jos ne ,mahaifiyarta maimuna harka wadda inkiyarta kenan tun yanmatan taka ,ta tashine a lokacin babu mai sata babu mai hanata ,
mutane da dama sukan yi kuka da halayyar maimuna karma ace magidanta amma da zarar ka kai kararta gidasu yanzu zakaji iyayenta sunce kana masu bakin ciki ne sabida Allah ya azurta yarsu,

maimuna Mai kyauce ,kama da kirar halitta har ya zuwa kan kyau na fuska ,
maimuna bata da kawaye a unguwansu saboda ko wanne iyaye gudu yake ace yau yarsa tana hulda da maimuna ,
hakan baya damun maimuna ko kadan dan acewarta dama mai zatayi da kawaye akan layi wadanda baki dayansu gayyar tsiyane babu wanda iyayensa ke sa masa albarka akan hanyar da zai samu kamar ita.

wacce irin sana'a maimuna take yi?
to maimuna dai sana'a ce take wadda babu wani uba ko uwa da zai so ace yau an wayi gari dansa ko yarsa yana kan wannan tsari,
wannan sana'a kuwa ba kowacce sana'a bace face sana'ar bin maza,a tara a debe.
a koda yaushe akwai hamshakiyar mortar da zatazo ta faka maimuna a kofar gidansu,
saboda irin karbuwa da albarkar da ke cikin sana'ar tata ta banza "a cewar mahaifiyarta"
yasa maimuna cikin lokacin mara yawa tasa aka rushe mata gidansu akan masu sabon gini na Zamani.

iyayen maimuna mutane ne masu kwadayi da san duniya da san zuciya ,a wasu lokutan mutane kan ce Ai zaiyyi wuya idan maimuna yarsu ce da suka haifa da cikinsu ,
amma abu daya da basu Sani ba shine "iyaye irin haka suna nan da yawa cikin al umma ,waddanda suka dauki yayansu mata jarinsu saboda kwadayi da san zuciya da suka saka a gabansu.

kwatsam ana zaune sai Wani saurayi ya shigo rayuwar maimuna ,
wasa wasa sai adadin rashin kunyar maimuna yafi na da amma fa sai adadin samunta ya nininku wanda hakan ko kadan bai damu iyayenta ba ,su dai burinsu daya a basu suci,

Saless irin yarannan ne marasa jin magana,
mahaifinsa mai kuɗi ne na gaske ,duk da cewa bakone shi cikin garin jos din hakan bai hana arzikin iyayensa ƙara ba a cikin garin,
duk da bautar kasa yazo amma sai kace shi din dan asalin garinne dan gida guda mahifinsa ya kama masa sannan ga bodyguards ɗinsa,motoci kuwa Sai kace yana aiki a kamfanin mota dan baya wata da guda,

ba karamun hure ma maimuna kunne Saless yake ba wanda daga baya ma gaba daya ta koma gidansa da zama kamar matarsa,.

Ana haka kwatsam maimuna ta samu ciki,a lokacin da ta kaima salees labarin cikin sai cewa yayi taje ta zubar ,
kuɗi masu yawa Ya bata amma da yake abun cikin nata rayayyene duk yarda taso ya zube sai yaki fita,
karshe da ta matsa sa jini ya balle mata ,
ta wahala sosai ,
iyayenta suka yi jinyanta ,
tun suna hakuri da ita har suka fara gazawa musamman dayake babu kuɗi.
sosai maimuna tayi jinya wanda duk cikin jinyar da take salees bai bi ta kanta ba dan karshe ma daina samun layi kansa tayi.

daga bisani da ta warke ta nufi gidansa dan suyita ta kare, amma ga mamakinta sai ganin bakin fuska tayi a gidan ,
tayi bakin ciki sosai musamman da yake bata san asalin inda salees ya fito ba sabida ita ba ta wannan take ba ta kudinsa take,

kara komawa asibiti tayi a karo na ba adadi amma abu daya likitan ke kara faɗa mata wanda shine idan har ta kuskura ta zubar da wannan cikin to zata iya rasa rayuwarta.

haka nan ta hakura har ta haife yarta macce wadda ta dauki tsanar duniya ta dora mata duk da a badini takanji Yar tata a rai amma idan ta tuna cewa shegiya ce sannan mahaifinta ya gudu ya barta duk da yasan da ita sai taji tsanarsa na shafar Yar tata,

lokacin da za'a saka mata suna fafur maimuna tace ita bata da sunan da za'a saka mata ,duk sunan da su kaga yayi mata su sa mata ita ba damuwarta bace.

Daga bisani da da ta kare ma yar tata kallo sai kwadayi yadarau aranta dan ɗiyar da ta haifa mai kyauce mutuka sannan tasan zatayi arziki da ita sosai nan gaba dan haka koda aka kara tambayarta suna tace ABLA(ma'ana mace kyakyawa Mai kyawun kira).

Kwatsam lokaci guda maimuna tace Zata bar garin dan fita neman kudi ,iyayenta ne suka nemi tabar abla gida tunda neman kudi zataje amma ta goga ma idanunta toka tace Ai yarda take jarinsu haka Abla take agunta tunda sun riga sun nuna mata diya mace jarice.
Basu mata musu ba tunda suma da wata niyar suka so ta barta din,
Kai tsaye Ibadan Tayi inda ta kafa sabuwar rayuwarta a wata unguwa Mai yawaitar hausawa,
Kamar wasa ta Fara girka barikinta wadda ta habaka har ta samu wanda ya siyan mata gidan da suke ciki,
Kafun kace me tayi suna dan har yara ke gareta wanda a shekara takan yayesu daga bisani kuma ya rage mutum uku wato "ashana ,Yar gwal da zinaru."

Haka nan idan ta tuna salees sai taji daukar fansarta akansa na ruruwa wanda ta kudira aka diyartata,
Haka take rainan Abla dan ta gama sa rai duk inda girma yazo mata to zata fanshe dukkan wata dawainiyya,
Haka Abla ta Fara girma cikin kulawar ubangiji,
Koda tana Yarinya idan ka kalleta zaka gane yarinyace mai kyau,
A lokacin da ta shiga matakin shiga makaranta fafur maimuna tace bazata sata ba dan ba karatu ta haifota tayi ba.
Kamar wasa zinaru tayima wani alhajinta magana yace zai daukewa Abla nauyin karatun har ya zuwa ta gama primary ,
Sosai zinaru taji dadi dan atleast idan ta gama primary sauran bazai wahala ba,

Duk da zinaru karuwace amma hakan Bai hanata zuciya mai kyau ba,haka nan Allah ya dora mata kyaunar Abla wadda uwar dakinta ke kudirar abubuwa marasa kyau akanta kamar ba ita ta haifota ba,
A rai zinaru Tasa Abla bazatayi karuwanci ba sannan zata taimaka mata tayi ilimi.

Ille Kuwa hakan akayi ,Alhajin zinaru ta daukewa Abla karatunta harta kammala primary,sosai zinaru ke nuna kulawarta akan Abla wanda sau da dama maimuna zatace "saikiyi Tayi Ai yarinya dai shegiya ce kuma sana'ar uwarta zata gada".duk da haka zinaru bata fasa ba ,da taimakonta Abla ta shiga makarantar gaba da primary ,
Lokaci daya Abla na tsaka da karatunta ciwo ya kama zinaru wanda ya kaita ga rasuwa ,kuka kam.Abla ta shashi domin a da tunaninta duka zinaru ce mahaifiyarta ba maimuna ba ,sai bayan Tayi hankaline ta fahimci komai,

A zuciya Abla ta kudiri niyyar cigaba da karatunta ko da ta cika burin zinaru sannan ta saka a ranta bazatayi karuwanci ba ,a haka da taimakon Allah ta samu aikatau a gidan wasu masu kudi inda anan ne take samun yan kudin da take cigaba da daukewa kanta dawainiyyar makaranta duk da yan karancin abunda zinaru ta mutu tabari wanda sai da tabbatar ta damkawa "Abla".

Bayan kamalawar Abla secondary ne ta nemi aiki a wani club inda take bartender nan cikin garin Ibadan,
Tasan rashin dacewar aikin amma babu yarda zatayi dole ne yasata dan mahaifiyarta ta murje idanu akan itakam bazata dauki nauyin wani karatu ba ,Ai tana da abun badawa abata kudi har ta sammata amma ta gagara saboda bakin ciki.
Abla ta fuskanci hare hare wanda take kai har yanzun amma tasama kanta tsaurin rai ,abu dayane take yi wanda ita kanta yake damunta wato rashin kunya,
Bata jin kunyar taka mutum indai ya shigo gonarta ,
Duk da bata da Mai Fada ma dai dai a Yanzu amma tasa dai dai kuma tasan idan tayi abu mai kyau ko tayi mara kyau,

Rayuwarta take babu wani a gabanta sannan tsaurinta yana taka muhimmiyar rawa wajen cecenta .

A Yanzu tana shekara ta biyun karshe a jami'a inda take karantar business administration.
Tayi kokarin wajen nema ma kanta ilimi na addini duk da kuwa da irin cin kashin da take fuskanta wajen nema amma bata sare ba.
"ABLA ADNAN"
Sunan ta ya faro mafari ne a matakinta na shiga makaranta inda da sukaje da zinaru aka tambayeta Ya sunanta tace Abla ,sunan baba fa ?
Tayi shiru haka zalika zinaru dan hajiyarsu bata hirar mahaifin Abla balle ma su san sunan sa jin zinaru Tayi shiru ne yasa Abla saurin Fidin "ADNAN"
Idan zaka kasheta bazata fada maka inda ta tsinci sunan ba kawai yazo kanta tafada kuma ya bita "ABLA ADNAN"
Yarinya Mai bawa kanta uba "ikirarin mahaifiyarta".

CHUCHUJAY.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top