Babi na Uku (03)
Zaune ta ke a falon makeken gidan su da ke sokoto road cikinsu birnin Kano tana gyaran nails inta. Ko dankwali babu akanta ta bazo gashin ta ya zubo baya sai kyalli ya ke, Riga da wandon jeans ke jikin ta sai kimonon da ke gefen ta in case of emergency. Gabadayan yaran gidan zaune su ke a falo su na kallo in ka cire Muhsin da baya nan, wani American series su ke kallo ita ko ear piece ke kunnen ta tana sauraron wakan Chris brown na don't judge me. Yusuf ke ta Mata magana ba ta Jin shi ganin haka ya sa ya tashi ya je kusa da ita ya kamo hannun ta sai a sannan ta juyo tana Kallon shi, da Ido ta mishi alama da what? Murmushi ya sakan manta sai dai ita fuska nata ba yabo ba fallasa. "Suhaila Wai ina saurayin ki prince?" Sai a sannan ta saki murmushi har sai da dimples inta su ka shige ciki sosai. "Prince na Nan Ya Y" hannu ya Kai Gashin ta Yana shafa ita ko sai Kara shige mishi ta ke "kinsan how lucky he is to have you?"
"Allah ya Y Kama San miye Wai aure ake son a mishi so funny na miji da auren dole he almost cried to me"
"Kuma shine ba ki damu ba baby ?" Ya fada Yana Kara kwanto da ita kirjin shi.
"Me yesa Zan damu I mean am not going to marry prince fa kawai dai am proud to be his girl ya na Kara min class you know"
"Kai baby Allah ya shirye ki halin ki sai ke yanzu ke daman ba son prince kike ba?" Girgiza kanta tayi in denial.
"I can't love him Ya y"
"To ni fa Zaki aure ni baby?" Girgiza kanta tayi "haba dai Kai? Never I told you I love somebody and it shall be secret"
"Ni ma fa Wasa nake Miki baby, I just like you my dear you are rare kin sani ko?" Ya rada a hankali a kunne ta.
Dai dai Nan Muhsin ya shigo falon, kicibus yayi da Suhaila na rungume jikin Yusuf sai faman sa harshen shi cikin kunne ta yayi.
Saurin au'uziyya yayi hade da rufe idon shi ya bude su ko Yan duniya maimakon su yi kokarin rabuwa Aa sai ma kallo da su ka bishi dashi. Tsawa ya dakawa Yusuf da ya firgita Yan falon gabadaya abin takaici Suraj da Sabir na zaune a Falon su n Kallon American series, a zuciye ya Kore su a Falon sannan ya Daga hannu ya sharara wa Yusuf Mari. "Kai mahaukacin Ina ne? Ko muharramakar za ka Mata haka balle wacce ba muharramaka bace?" Tsaki Yusuf ya ja hade da barin Falon Yana kunkuni sai a sannan ya juya ga Suhaila "ke Kuma fitsarar ra kin tsaya kina Mika jikin ki ga na miji, banza kawai Yar iska Allah wadaran halinki"
Kallon rainin wayau ta bishi dashi a fili tace "Ni ba Yar iska bace" wani Irin duka ya Kai wa bakin ta bayan hannu ta sa Kara sai a sannan ta tashi ta nufi hanyar dakin ta "Kuma Allah ya Isa sai na fadawa Mami" tsaki Mai karfi ya ja kana ya nufi dakin shi domin yin abinda ya maido shi gida cike da takaicin halayen Yan gidan su Wanda ba kowa bane silah face Mahaifiyar shi.
As he expects Yana shigowa gidan da dare ya ji Mami na faman kwalla mishi kira. Ba zai iya kin zuwa bane ya je ba wai don yana so ba.
Yana zuwa ta fara mishi fada ta inda ta ke Hawa ba ta Nan ta ke sauka ba.
"Habawa ka bi ka takura wa yarana ka samu su Ido sai kace ba Yan uwanka ba su Daman sakewa, wannan wani irin bala'i ne haka Wai? Toh wlh ka fita Ido na in rufe kana jina."
Ba abinda ya ce Mata har sai da ta sarara.
"Kiyi hakuri Mami, a yanda na tadda su ko kadan bai Dace ba wlh Mami. Gyara na musu"
"Toh sarkin wa'azi, shin Wai Kai kadai ne musulmi a gidan Nan? Yara Basu da daman motsi sai ka sa musu ido daga sun dan zauna kusa da juna shine laifi ba gida Daya su ke ba" girgiza Kai yayi "Aa Mami wlh ba kusa da juna su ka zauna ba, Mami ya za ayi kaman Yusuf ya jawo Suhaila jikin shi ba fa muharramin ta bane"
"Eh lallai nuna Mata gidan uban ka ta ke zaune, wani abun su kayi da ya wuce Nan" cike da takaici Muhsin ya rike kanshi da ke barazanar fashewa, lallai Mami tayi nisa ba ta Jin Kira. Shin Wai Boko hauka ne.
Abba ne ya karaso falon sai bambami ta ke. "Mami lafiya ke da dan naki?"
"Wlh Abba Muhsin ya ishe ni sai kace ba jinina ba ya bi ya takura wa ya'ya' na. Har zai daga hannu ya Mari Yusuf da ke NYSC Fisabillahi ai ya wuce duka da ba dan Yana da tarbiyya ba ai ramawa zai yi ni ban San Ina ka dauko bakin hali ba."
"Ai ko Muhsin Bai da bakin hali" Abba yayi caraf ya tari zancen "ki dai bincika ki ji me sukayi ya hukunta su don nasa ruwa bai tsami banza"
"Haba Abba ya za kace haka?"
"Ehm ehm Mami" ya tare ta "ki bincika Mana Muhsin me ya faru"
"Abbah samun Suhaila fa nayi kwance jikin Yusuf Abbah ba fa muharramin ta bane"
Girgiza Kai yayi sannan ya kalli Mami alamun he is disappointed in her. Nan fa ya Kira Yusuf ya mishi tas sannan ya Mai warning Kar ya sake ganin ko Jin irin haka ya faru. Mami dai sai hararan Muhsin ta ke Kaman ta shake shi.
Shin wannan wani irin rayuwace, Mahaifiyar ka ta daura ma ka karan tsana don kawai halayen ku ya banbanta, a kullum Yana cikin nema Mata shiriya don ko Mami mace ce da boka ya cinye tsab. Lecturer a BUK ta ke koyarwa.
Suhaila yarinya ce Mai takama da ji da Kai musamman da ke ita din kyakyawa ce ajin farko, hakan ba karamin daga sama ya ke ba, Ga ta da shegen fadin rai da Kuma girman Kai sannan In fa tayi niyyan Abu ba Wanda ya Isa dakatar da ita. Tun tana JSS3 idanuwan ta suka bude ta San Mai duniya ke ciki bakomai bane ya jawo hakan sai irin yawan ziyartan wuraren haduwa da samari da Yan Mata da ta ke yawan zuwa irin su get together na school da kuma fun fair. Tun farko ba ta ajiye kanta kusa ba shiyasa ko wurin get together ba cika hulda da mazan class ta ke ba, a cewan they are too small for her class. A wani fun fair da su kaje ita da Yusuf ta hadu da prince Muhamud Dan sarkin Zaria. Tana ganin shi ta San shine dai dai class inta sai akayi Sa'a shima ya kyasa ko ba don komai ba kyawun ta kadai ya Isa ga iya kwalliya, Jan aji da takama. Rawar da tayi da jikin ta cikin natsuwa Wanda ya fita unique da na kowa ne ya fara Jan ra'ayin shi gare ta da ya kula da babyn is classy ya gane yayi Babban kamu. Sai dai shi soyayyan gaskiya ya ke Mata don shi har ga Allah ya fi kaunar mace wayyaya Wanda ta San duniya sosai ita Kam kawai tana tare dashi ne saboda matsayin shi, kyaun shi da kalan shi ma. Duk abun Nan Mami da Abbah ba su San fandarewar Suhaila ya Kai Nan ba illa iyaka Mami tasan Suhaila na yawan fita ba Amma ba tasan Ina ta ke zuwa a tunanin ta wurin kawayen ta take zuwa Wanda hakan ne Amma ta daya bangaren tunda har nasarar zuwa clubs clubs su ka Kai. In ko ka ganta a gida ka rantse ba ta iya zuwa saboda magana ma ba cika yi tayi ba.
Shi ko bawan Allah Muhsin gabadaya gidan shine ya fita daban, Doctor ne currently Yana Housemanship in shi a Asibitin malam Aminu Kano, Yana matukar kokari gun kare dokokin Allah tare da tsanar halayen Mahaifiyar da sauran Yan uwan shi, Suraj ma kusan Haka yake sai dai Sabir da sauran shi tukun kuma duk Mahaifiyar tasu ce silah tunda su ka baro katsina, su kayi watsi da islamiyya da sunan za a kawo musu malami. Ko yazo ba abinda su ke ganewa ba ma sa maida hankalin ne sai dai ya gaji ya tafi karshen wata a biya shi kudin shi. Muhsin ne kadai Mai ilimin addini a gidan cikin yaran kenan.
Abbah ko karfin shi aka Fi, yayi fadan yayi wa'azin ya dau mamakin duk yaki yi daman dai ance uwa it ce gida. Gidan Mami saudah Kam sai addu'ar ubangiji domin ko ta yi nisa ba ta Jin Kira duk a sanadin Boko, ba shakka irin su Mami ne ke sa ana kalubalantan Boko a na kinshi, ita dai ta wa bokon ta ta mummunar fahimta.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top