Babi na sittin da takwas ( 68 )
A gajiye likis ta fito daga ma'aikatar da ta ke siwes. Two weeks kenan da ta fara IT in, 8:00 am to 4:30 pm haka ta ke fama kullum. Wuni suke suna aiki, a hakan ma Wai don IT student in na dayawa... Fatan ta daya Allah ya sa an zo daukan ta, don kwannan haka Suraj ya ke barin ta jira. Ba Daman tace za ta tafi Abbah ya hada su duku biyu ya musu tatas. Ilai kuwa ba ta ga motan Suraj in ba sai dai wani hadadden motan Ash Avalon ta hango. Kaman jira ya ke ya hango ta ya fara zuba Mata horn. Mamaki ne ya kamata ta tsaya tana kallon motan. Daya daga cikin wacce su ka fito tare ne tace ma ta "Suhaila wancan fa ke ya ke wa horn" tabe baki tayi tace "Ni kam ban San kowa da motan Nan ba"
Wata ta kara cewa "kika sani ko sabon kamu ne"
Dayar tace "da rana akan ta" dariya tayi tana mamakin yanda aka yi su ka San an sa mata rana. Ita dai ba ta fadawa kowa ba.
Horn mai motan ya kara yi Amma sai ta yi juyawan ta ma kaman ba ta San anayi ba. Ganin dai da gaske ba za ta zo ba yasa yayi giving up ya bude motan ya fito. Ta gefen ta ne ta juya ta kalle shi. Ji nayi suna furta "wow! Kinga handsome in da kika share kuwa"
Kaman ba za ta juya ba sai kuma ta juya. Ware idanu tayi tana kallon shi cike da mamaki. "Suhaila" ya Kira sunan ta da karfi.
Wata ce tayi saurin cewa "ko dai angon ne?" Murmushi tayi sannan tace "My brother" sallama ta musu sannan ta karasa inda ya ke. Kafin ta isa har ya shiga motan. Tana shiga tace mishi "Yaushe kazo?"
Hararan ta yayi yace "ba gaisuwa sai yaushe nazo?" Ita ma wani kallo ta mai tace "remember ni fa yanzu Antyn ka ce"
Dariya yayi yana reverse yace "Su beauty manya Amaryan Ya Muhsin. I still can't believe this Allah, I mean tun yaushe aka fara ban sani ba"
Siririyan dariya tayi tace "You were in Lagos remember"
"Ba wani Nan. I've been suspecting the both of you tun can daman na Sha fada Miki Ya Muhsin yana ciki Amma you never believe me"
Hannun ta tafa "well, Yanzu na yarda Angon Fati"
"People thought we were dating kin tuna?"
Nodding Kai tayi yace "Ni kuma nasan i can't go for my brother's Choice"
Hararan shi tayi tace "as if Shiri kuke da shi a da"
Zaro idanu yayi "nasan ba mu dasawa dashi but I've always see him as a good figure, I love him in my own ways. Yanzu dai please alfarma mu ke nema, za ki taya Fatima wasu siyayya ne pls, you have a Good choice.
.....
Tana kitchen ta fara jin knocking sanin ba kowa a wurin ya sa ta nufi kofan. Ba tare da ta duba ba kawai ta bude, sake baki tayi tana kallon Wanda yayi appearing a gaban ta. Sakaka haka ta tsaya tana kallon shi, ita ba ta motsa ba kuma ba ta bashi wuri ya wuce ba. Abu daya ne ke yawa a kanta shin yaushe ya dawo? Tafi ya Mata a saitin fuska, sai a lokacin ta gane bashi kadai bane. Saurin basu hanya tayi tana fadin "sannun ku da zuwa"
Murmushi Rahma da ke bayan Muhsin ta ke. Cikin ta ya fito sosai, duka duka bai Kai one month ba EDD inta. Kallon Suhaila tayi tace "Yauwa mun same ku lfy?"
Shi dai Muhsin ciki ya nufa yana fadin "Mami na gida kuwa?" Ba Wanda Suhaila ta amsa a cikin su sai dai ison da ta ma Rahma a kujerun Falon.
Dai dai lokacin Yusuf ya shigo falon yana fadin "maraba da babban Yaya"
Hannun ya bashi su ka gaisa sannan ya juya su ka gaisa da Rahma cike da tsokana ya kece Mata "Sannu maman babyn mu" hararan shi Muhsin yayi yace "Mami fa?"
"Mami na falon ta bara na Mata magana" Yusuf ya fadi yana tfy. Dauke da tray Suhaila ta fito daga kitchen ta ajiye akan stool in da ke gaban Rahma. "Nagode Sister" Rahman ta fada, murmushi kawai tayi ta juya, unfortunately su kayi four eyes da Muhsin. Kasa Fassara kallon da ya Mata tayi don haka kawai ta basar. Kitchen in ta koma tana mamakin dalilin da yasa bai fada ma ta dawowan shi bayan sun yi waya. Yanzu ta gane dalilin da yasa ta Kira numban shi bai shiga. In har tace ranta bai bacci ba to tabbas tayi karya. Tana iya jiyo maganan Mami daga kitchen tana fadin "maraba da bakin turai" sannan su ka gaisa da Rahma tana tmbyn ta jikin ta.
"Ba dai wani damuwa ko Rahma?" Muhsin ne yayi wuf yace "Mami damuwa fa akwai shi kala kala, yanzu ma Wai kafafun ta ke kumbura ita kuma ba ta son motsa jiki shiyasa ma na matsa Mata ta rakoni"
Dif! Haka Suhaila taji network inta ya dauke. Nan ta ke taji abu na taso Mata a kirji, wato damuwan da yayi da matan shi yasa ma bai bi ta kanta ba kenan? Allah ya gani ba ta da wani mugun abu akan Rahma sai dai in tace ba ta jin kishin ta wasu lokuta to tabbas tayi karya. Sau da dama in taji irin haka akan Rahman tana saurin kauda abun a zuciyan ta yayin da ta ke jinjina wa Muhsin akan yanda ya damu da lamarin matar shiz tabbas tana kyautata mishi zaton yin adalci tsakanin su.
"Ai motsa jiki ya zama dole Kuwa Rahma. Kama ta yayi kullum da safe da Yamma ki dinga yi Amma asibitin sun tabbatar mu ku da komai lfy ko?"
"Eh Mami ba wani matsala" ta amsa.
Karan shigowan Sms ne ya shigo wayan ta. Show your face baby, I can't miss it anymore.
Siririn tsaki ta ja bayan ta gama karanta wa. Ba ta fito in ba har sai da ta gama abinda ta keyi. Kyam idanun shi kan kitchen, shi ya fara ganin fitowan ta. Tana ganin sun hada ido tayi saurin dauke na ta tana fadin "Mami am done"
"Sannu kinji Yar Mami, Allah ya Miki albarka My daughter ya baki masu Miki" Ameen ta amsa sannan ta karasa gun mamin ta zauna.
Bude baki Yusuf yayi yana fadin "Mami kina ji da Yar nan ta ki sosai gashi ta kusa tafiya ta barki"
"Diya mace ai rahama ce Yusuf"
A tare da Muhsin Yusuf in su ka ce "Kai Mami" dariya kawai ta musu. Amma har zuciyan sun San Mami na matukar son diya mace Allah bai bata amma kuma Suhaila ta share Mata hawayen komai shiyasa ta ke matukar ji da ita.
Suraj ne ya dauko sauran brothers insu daga Islamiyya gidan ya zama full house. Sun Sha hira sosai har da Abbah da ya dawo. Amma fa Sam Muhsin bai ga sakin fuska daga gun gimbiyar ta shi ba.
.....
Washegari misalin karfe Sha biyu na rana ya isa gidan. Kaman yanda ya yi ta addu'a yana shiga ya iske ta a falo ta fito daga gun mami. Sama sama ta gaishe shi ya amsa sannan tace "Mamin na ciki"
Kallo ya bita dashi sannan yayi folding hannuwan shi kan kirji yace "You know am here for you. Why is my baby not happy to have me back?"
Kallon shi tayi sannan tayi saurin sadda Kai kasa. Hawaye ne taji ya biyo idanun na ta, saurin sharewa tayi sannan tace "I will enter" in a cracky.
"Don't in ba so kike in biki ba" yayi saurin fada. Kujera ta samu ta zauna tana kara goge hawayen da ke fitowa daga idon ta.
Cike da mamaki ya samu wurin ya zauna ta yanda ya ke fuskantar ta. "Lfy kuwa? Me ke faruwa pls talk to me mana"
Kara kuluwa tayi jin bai ma San abinda ya bata ma ta rai ba, tuni hawayen ya fara fitowa sosai har da shesheka ta ke.
"No please Suhaila Kar mu yi haka da ke. Wlh kina sani a damu, am so eager and excited to see you Kar ki sake min guiwa mana. Ko dai akwai abinda ke damun ki ne? Please let me know"
Kin magana tayi sai ma kara himman kukan da tayi. Har sai da attention in Mami ya je wurin. Da sauri ta nufi falon sai dai tana ganin su tare ta hade rai maimakon damuwan da ta taho dashi.
"Suhaila lfy?" Mamin ta fada tana isa gare ta. Kaman jira ta ke mamin ta zo ta fada jikin ta sannan ta saki kuka mai karfi har numfashin ta daukewa ya ke.
Don mamaki Muhsin saakin baki yayi yana kallon su har sai da ta fara shesheka. "Muhsin me ka ma diyata?" Mami ta tmby.
Kallon yanayin fuskan ta yayi ya ga ta Sha mur. "To ai Mami tmbyn da na ke Mata nima kenan." Harara ta maka shi tace "me ma kake a Nan? Tashi ka fitan min daga gida" tana rufe bakin ta Sallaman Abbah ya karade falon. Muhsin ne yayi saurin tashi ya amso bag in hannun shi baya sun mishi Sannu da zuwa.
"Mai Dana yayi ake koron shi Mami?"
Murmushi tayi Daman ta San Abban dole sai ya tanka, in dai akan Muhsin ne to fa Abbah bai san kawaici ba. "Kai Abbah to tsakanin Da da Uwa ne in kuma za ka shiga Bismillah."
"Rufa min asiri, sai dai yar taki ma na ga kaman ba lfy ba, me ke faruwa Suhaila?" Kakalo murmushi tayi kawai ba tare da tace komai ba. Mami ne tayi caraf tace "Abbah ka fada wa Muhsin ni fa ban son takura don ma ka dage ne in ba hakan ba Ina jituwa tsakanin Suhaila da Muhsin"
Kallon ta Abbah yayi yace "Mami rigima, to ba dai a shiga don in kika ji kunya to fa ni kam bbu ruwana" ya karasa zancen hade da mikewa. Ita mamin mikewa tayi ta bi bayan mai gidan ta. Murmushi Muhsin yayi yana kallon su. Hakika soyayyan iyayen nashi ke nunawa juna na matukar burge shi.
Yan sakwanni ya dauka yana kallon ta kafin yace "my queen" saurin dagowa tayi tana kallon saboda ba ta taba ji ya kirata da sunan ba. Shi ma ya gano hakan murmushi yayi kawai yace "what our prblm please?" Yanayin kallon da ya ke Mata ne ya sa ta sakin murmushi ba shiri. Shi ma murmushin yayi yace "tell me please"
Hade rai tayi tace "you can't even tell me za ka dawo ko?" Yanda tayi da fuskan na ta ne ya ji ta burge shi kaman wato baby. Zaro idanu yayi yace "I don't know that you aren't a fan of surprises Amma am sorry ba zan kara ba kinji" kunya ta ji ta Kama ta. Ashe abinda ta ke tunani ba haka ba ne. "Ba ki ce komai ba"
"It okay" tayi saurin amsa shi. "Meyesa ba ki fadawa Mami tsakanin mu ba" kallon shi tayi cike da mamaki yace "better you tell her in ba haka ba gani ta ke kaman an takura ki ne" murmushi tayi kawai ba tace komai ba.
.....
Gadan gadan aka fara shirye shiryen bikin. Muhsin daukan kudin duk wani kudin abinda ake bukata yayi ya damkawa Mami. Ita ko sister inta ta ba ma wa da ke harkan business, gabaday aka hada Mata da na Yusuf. Sai dai akwai specific abubuwan da su mazajen su ka siyo da kan su. Musamman Muhsin ya je dubai har kayan baby ya hado dasu.
A month to bikin Rahma ta haifo bouncing baby boy mai kama da baban shi sak. Suhaila na bacci karfe Ukun dare ringing wayan ta ya tada ta. Abun ya bata mamaki da ta ga sunan shi because it very rare suyi waya in 10 ya wuce. "Sorry na tashe ki ko?" Ba tace komai ya kara cewa "na Kira numban Mami a kashe daman Rahma ce ta haihu"
"Really? Me aka samu? Lfyn ta lau ko? Bara in fadawa mamin" kit ta kashe wayan ba tare da ta saurari amsan shi ko daya ba. Mamin ta samu ta fada ma wa. Ana idar da sallan Asuba su ka nufi asibitin. A ranar ma aka sallame ta da ke komai lfy kalau.
Su Muhsin kam an kasa zaune wuri daya sai washe baki ake an samu baby. Sai a lokacin Suhaila ta gane yana son Yara sosai.
Abbah ya samu takwara wato Abdulrahman Muhsin Abdulrahman ana mishi lakabi da Daddy. To Ubangiji Allah ya raya mana...
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top