Babi na sittin ( 60 )

Normal su ka koma labari har su ka isa Zarian. Yana fidda Mata akwatin gate man in apartment in su ya zo ya shiga dasu. Nan meema ta gane ta iso Daman ita tun dazu ta iso. Fitowa tayi taran ta ta iske ta tsaye da Muhsin suna magana. Shi ya fara hango ta yace "Ah ah Amarya" sai lokacin Suhaila ta juya ta ganta. Da sauri ta karasa wurin tayi hugging inta tace "Ya meema amarya i miss you"

Gaisawa su kayi da Muhsin yana tsokanan ta da Amaryan Faisal. Kasa shiru tayi tace "Kai Yaya Muhsin Kai ma dai naga alaman kwanan za ka kara zama angon ai" bude baki yayi yana kallon ta speechless. Juyawa yayi yana kallon suhailan alamun neman karin bayanin. Dariya ta mai ta juya kanta. Ita dai meema sallama ta mishi ta shiga ciki.

"I tell her nothing" tayi saurin fada bayan meema ta shiga.

"Za ma kiyi bayani yarinya" dariya ta mai yace "Ni bara in wuce ban son yin dare" ya fada yana shiga motan

"Tou Shkkn, be safe"

"For you?" Ya fada yana kallon ta

Nodding kanta tayi tana murmushi yace "I love you Suhaila" blushing tayi this time sannan ta fara mishi waving.

Tana shiga meema ta fara Mata dariya tace "na rantse da Allah da ki yarda da Kar ki yarda Soyayya kuke da Ya Muhsin"

Bata fuska Suhaila tayi tace "miye na rantsuwan? Na Miki musu ne?" A tare su ka fashe da dariya meema tace "somebody is glowing from a new relationship"

Text ta ma Asmau tace "he confessed" alkawari ne ta dauka and she fulfil it.

Ba a dade ba Asmaun ta Kira ta tana tsokanan ta.

Yana isa Abujan ya Kira ta da azama ta dauka yace "Na Kira in ce wa yar budurwata na isa lafiya"

"What a name" ta fadi tana dariya

Yace "soyayya ce"

Dariya tayi tace "ka isa lfy? Ya hanya?"

"Lfy kalau, ya gajiya?"

"Bbu fa"

"Okay, let me take a rest. We will talk tomorrow"

"Tou Shknn, a huta lfy"

"Sai anjima, love you" da sauri ta kashe wayan ta na murmushi. Tunani ta ke yi Wai daman haka Ya Muhsin ya ke ko kunya baiji? Ta fadi a ranta. Namijin kenan, so free ba ruwan shi.

Ko da ta tashi washegari sai wurin ten ta shiga school. Ba laifi anyi lectures da ke second week in resumption ne.

Karfe daya da Yan minutuna ta fito lectures. Wayan ta da ta sa silent ta dauko domin ta cire Nan ta tarar da msg in shi

"Sorry i couldn't call you in the morning. Text me when you are done with the lectures. Luv you"

Wato he intend to always remind her of the love thing. Ita kam har yanzu jin abun ta ke da gaske. Masallaci su ka tsaya da wata course mate Inta su kayi sallah. Tana wurin printing in course form call in shi ya shigo.

Da sauri ta dauka tace "Ina wuni Ya Muhsin" shiru taji har za ta kara magana a hankali taji yana Fadin "na gaya Miki ban son sunan ko. Not anymore kuma. Ba haka ake yi ba"

Dariya tayi "Afuwa tou. Ya Abuja and conference"

"Lfy am done. On my way back... I want to see you." Jin yanda yayi sounding serious ya sa tace "sai kazo, safe journey"

Da Yamma lis ya iso Zarian. Direct apartment in nasu ya nufa, tun kafin ya iso ya Kira ta.

Wani smiling ke kwance akan fuskan ta sanda ta fito. Ta window ya ke kallon ta har ta karaso. Bude Mata kofa yayi yace "Bismillah Love" kallon shi tayi ganin yanda shima ya bude ido yana maida martani ya sa tayi saurin sadda Kai kasa cike da kunya.

Sai da ta zauna sannan ta dan saci kallon shi. Ya daura kan shi a steering, yana kallon ta gefe, idanuwan nashi sunyi ja kaman Wanda ke kokarin lumshe su haka yake.

"You look tired. No, exhausted suit you more"

Lumshe idanun yayi sannan ya kara bude su yace "am sick Suhaila"

Saurin dago kanta tayi tana kallon shi. Sai dai ya murmusa ganin damuwa kwance akan fuskan ta yace "Calm down baby ba wani serious issue bane. Infact love sick ne. You Know I've gone through confession, proposal and all so imagine the energy"

Rolling eyes inta tayi sannan ta aika mishi harara tace "sai kace Wanda yayi dambe ko shadi. Thank God ba a kauye bane and thank God yanzu ma you are not rejected"

Smirking yayi "To ai ko karkaran ne Wlh sai nayi. Ke kin San yanda nake son ki kuwa? I've gone crazy baby" ya karasa zancen shi yana taba heart In shi.

Rasa yanda ma za tayi reacting to action in shi tayi. Sai kawai tace "baby huh!?"

"Yeah! You are my baby. My baby love"

"Ya Muhsin Wai Daman haka kake?"

"Ai nama fi haka baby love"

"All the ustazanci?"

Hararan ta yayi yace "Wato su ustazan an Raina su ba. To ai wlh bara in fada Miki irin mu mun ma fi iya soyayya. Thank God you have one now. Za ki gane because you are never gonna love someone else kuma"

"Stop bragging, am not doing kuma" ta fada tana turo baki.

Dariya yayi "Don’t ever for a minute think that I don’t see all the love and affection you shower on me. I know love when I see it and you are the best image of love I have ever seen."

Blushing tayi sannan ta kara turo bakin kaman za tayi kuka.

"Stop it please wlh it a torture. As it if we are married i should have known how to deal with the  cute lips but now please let not go there"

Widening eyes inta tayi tana kallon shi shima ko ya kifa Mata brown eyes in shi. An Sha fada Mata kaman su ya baci da Muhsin. Yau ta kara yarda da hakan domin har cikin idanuwan su Kama su ke. "You are unbelievable!" Ta fada hade da sighing.

"Kin San me ya kawo Ni?" Shaking kanta tayi.

"In na koma Kano za muyi magana da Abba about us. So what do you think?"

"Bangane ba"

Hararan ta yayi yace "Are you not planning on marrying me?" Bai jira amsan ta ba yace "Then start it. Akwai course in da zanje Nan da one month. Six months course ne so ya kike ganin in nadawo sai ayi ko"

"Six months course?"

Dariya yayi yace "I have to go sorry. In ma Abban magana akan haka?"

A hankali tace "ehmmm" jin yanda jikin ta yayi sanyi ne yasa yace "Chill babe not like am leaving now"

Ba ta kara cewa komai ba ya kalli agogo "bara in je Masallaci daganan zan wuce. As you said am exhausted"

"Ba ka jin tsoron driving in dare?"

"Na saba ai"

"Then safe journey, a gaida su Mami da kowa da kowa"

"Kowa zai ji, sai munyi magana" a haka suka rabu.

.....

Bayan anyi auren su meema da three months aka sa na Su Suhaila da ma Yusuf gabadaya.

Sha'anin meema da Faisal kam kwata kwata bai yi Kama da ba wadanda za suyi aure cikin kwanaki kadan ba. Ba communication, nothing nothing. The last time da su ka hadu shine tun maganan da su kayi a hut in Daddy. Ko da yake a cewar su auren bogi ne so no needs for all these. Ko mama ta mishi maganan yana hadu da meema kuwa. Ce Mata ya ke suna waya kuma yana zuwa Zarian. Da ke Abuja ya ke zama ba ta wani fuskan ci wani abu ba. Alakan shi da mummy yana Nan kaman da domin kwata kwata bai ganin ta a matsayin surkuwa.

Suhaila tasa sa ta a gaba tana tmbyn ta Wai wani irin aure za suyi da Faisal Amma da ke Suhailan ba mai damuwa da harkan mutane bace da ta ga take taken meeman ba ta so a sani sai ta barta kawai.

A haka semester ya kare aka fara Exams. "Wani Event za a mana?"

Kai tsaye meeman tace "none"

"In ba baki isa ba. Ai ba zaman makoki za muyi ba sai dai kace bikin Asmau"

Hararan ta meeman tayi tace "Miye na tashin hankalin ba sai kiyi ana ki ba in angon zai bari"

Ba Shirin Suhaila ta saki murmushi tace "ai dole ma Ya Muhsin ya ajiye ustazancin shi. Biki daya dai a rayuwa ta dole na cashe. Kin ma tuno min bara na fara mai maganan ba"

"Tou Ni dai ba zan ba"

"In ba za ki iya ma Ya Faisal in magana bane sai Ni in mishi ko kuma in Kira Mummy ko Mama ba shknn ba.

"Wai ke yaushe kika zama chatter box?"

Dariya tayi tace "komai kamawa ya keyi. Yaya meema kinsan me za ayi? Please all Ladies events muyi Mana na friends kawai. Ai Kinga ba sai kin mai magana ba"

Dariya tayi ganin Suhailan dai ta dage. Wani tunani tayi to makes the wedding looks real bara ta hi shawaran suhailan.

"Let have a slumber party"

Da sauri Suhaila tace "Yeah sai Musa Pyjamas" a tare su ka kwashe da dariya. Suhaila tace "okay on a serious note. Muyi Tea party a Nan Abujan"

Shrugging shoulders Meema tayi tace "plan for everything then and by everything i mean everything"

"Trust me Mana "

Nan da nan ta hau IG ta nemo Favorite make up artist inta, numban ta ta dauka ta fara kokarin booking, Fashion designer da za tayi bridal gown da wacce za tayi na set in friends,  Event planner, photographer and Baker. 

Shirin biki ya kam Kama gadan gadan. Komai a Abuja su kayi deciding za ayi saboda Kar a ba mutane wahala. Tana gama Exams Daddy ya turo Mata Driver ta koma Abuja.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top