Babi na shida ( 06 )

   A hankali Najib ke Kara warkewa sai da yayi three weeks a katsina kafin ya koma kaduna bakin aikin shi. Kasa zama a tsohon gidan shi yayi ya koma gidan su faisal saboda ganin komai ya wuce. Daga baya ma Saida gidan yayi ya siya fila ya tada wani ginin da Faisal ya zana ya mishi tsarin komai da komai.

2 months later

Katsina

Manya manyan gidan Baffah na gani zaune a falon shi, da dukkan alamu meeting su ke yi saboda yanda na ga kowa na tofa albarkacin bakin shi. Yayin da mutane dayawa su ka yanda da shawaran da aka tsaida. Alh Abdulrahman malumfashi mahaifin su Muhsin ne ya Fara magana "Baffah ban tari numfashin ku ba Amma zai fi kyau a ce an Fara tambayan yaran Nan an ji ta bakin su kafin a gama zartar da hukunci saboda kar azo ayi Abu ba dadi azo ana samun matsala" murmushi baffah yayi sannan ya kalli Abban "Banda a binka wannan ai aikin ku ne sai kusa iyayen su Mata su ji ra'ayoyin nasu Ina ga hakan zai fi" kowa ya amince da shawaran kafin aka rufe taro da addu'a. Kowa da fara'a a fuskan shi ya fito falon da alamun dukkan su hukuncin ya musu.

A tsaye ta ke a bakin titi tana faman neman napep in da zai sauke ta unguwan su Goruba road. Har ta tsaida napep in ta ji horn a bayan ta, tana juya su kayi four eyes da MK Yana ta faman jera Mata horn. A tare su ka sakar wa juna murmushi ya Mata alaman ta Zo ta shiga. Da hannu ta Mai alaman ta Riga ta tari Mai napep, da idon shi ya Mata alaman ta sallame shi da dukkan alamu suna jin dadin yaren kuraman nasu. Ganin haka Mai napep in yace "hajiya bara kawai in tafi tunda na ga alamun ana jiranki" ko kafin ta amsa shi ya tada mashin in shi ya Kara gaba. Motan ta nufa ko kafin ta Isa har ya bude Mata passenger seat in. Sai da ta shiga sannan ta gaishe ya amsa. "Ina zuwa?"

"Gida" ta amsa

"Shine ko sallama babu ko?" Shiru tayi Yana jin haka ya gane dalili "Hala fada kuka yi da Fadila" shiru tayi don haka ya tabbatar da zargin nashi ganin irin kallon da ya ke jefan ta dashi ya sa tayi saurin bude Baki "Ya Mk ba haka bane"

"Hey don't lie to me I know you more than you know yourself" tsit tayi jin abinda yace.

"Kin fadawa Ummi?"

"Ba ta gida Amma nace mata Zan tafi dama"

"Me ya sa har yanzu ba za ku daina fada ba, you guys are matured fa yanzu haba"

"Ya MK ita ke ja fa"

"Common shut up ita ma haka za ta ce" tsit tayi Bata Kara magana ba har ya gama fadan shi sai can tace "Wai Ya Mukhtar yaushe za ka koma Florida" rage gudun motan shi yayi sannan ya Dan juyo Yana facing inta "kina so in tafi ne" girgiza kanta tayi innocently "kawai na ga ba ka ce ka dawo gabadaya bane Kuma ka Dade a gida"

"Zan koma sai nayi aure Amma tunda ke kin ki ki bini" da sauri ta juyo tana kallon shi "yauwa Ya MK remember kace za ka nuna min pic in girlfriend inka Kuma za ka fada min sunan ta"

"Ina sane na dauka baki son sani ne Kuma"

"Kaiiii Ina so sosai ma"

"Then sai ran da kika dawo daga gida"

"Mu koma na fasa tafiyan ma"

"Kin Isa bayan mun iso unguwan" magiya ta dinga mishi yayi Banza da ita daga karshe ta Bata rai har su ka Isa bakin gidan ta fita. Har cikin gida ya bita su ka gaisa da mama Aysha da sauran Yan uwanta sannan ya tafi.

Da dare Yana zaune cikin dakin shi ya samu kanshi da kiranta. Suna zaune da kanwar ta Maijidda tana jiran Umar ya Kira ta as usual call in nashi ya shigo. Kaman ba za ta dauko ba sai Kuma ta kasa. "Hello" ta fadi a hankali.

"Asmauuu" ya Kira a hankali daga ita har shi sai da su kayi feeling yanda ya Kira sunan.

"Naam" ta amsa

"Are you still angry with me?" Turo baki tayi kaman yana ganin ta sannan ta ce "eh mana" cike da shagwaba.

"Am sorry kinji da kin dawo Zan nuna Miki pic in. I just hope koma wacece Zaki bani support right"

Gyada kanta tayi kaman yana ganin ta sannan ta ce "eh Ya MK"

"Toh kin hakura"

"Ehhh"

"Yauwa my Asmeey. Ya su Mama da su Maijidda duk"

"Duk suna lfy"

"Ya kasuwa?"

"Alhmdlh Yana tafiya yanda yakama, Toh yaushe za ki dawo"

"In three days"

"Toh Shknn Allah ya kaimu. Sai da safe Koh?"

"Ehmmm a gaida Anty nah" murmushi kawai yayi Mai kayatarwa sannan yayi ending call in.

A birnin Kano

Zaune ya ke a tsakar gida Yana Shan iska Yana duba littafan da ke gaban shi. Ya Dan dade yana karatun sannan ya ji Karan tsayuwan mota a kusa dashi. Dam! Ya ji gaban shi ya Fadi a sanadiyan hango wacce ke Shirin fitowa daga mota sai dai abinda bai sani ba shine a tare kirjin nasu ya buga. Shin me ke damun zuciyoyin guda biyu? Abinda na tambaya kenan. Cigaba da duba littafin yayi sai dai ko kadan ya kasa fahimtan komai gabadaya hankalin shi ya kau, tunanin shi ya gushe sai wani irin bugawa da kirjin shi ya ke, he is trying to avoid everything but his hearts keeps pushing him. Yusuf ya Fara fitowa daga motan gimbiyar ko sai da ta Kai kusan 2 minutes kafin ta bude ta fito. Karan takalmin ta ya sa shi dagowa Yana kallon direction inta, four eyes su kayi yayi saurin dauke kanshi jin Abu na ratsa kwakwalar shi nd ba zai iya kallon ta a irin shigar da tayi ba. A hakan ma yau ta danyi modest dressing. Pencil jeans ne da yayi matukar Dame ta don ko ba abinda ya boye daga shape in jikin ta sai ko Dan karamin shirt da ta daurawa BF denim jacket a Kai da kadan ya rufe Mata baya sai ko uban heels da ta Sha kanta Kuma wani Karam scarf ta sa gashin duk an zubo shi baya. Ear piece ne manne a kunnen ta as usual. Har sun Zo shiga falo Yusuf ya Mata alama da fuska ya na nuna mata Muhsin da ke zaune a can gefe. Winking ido ta mishi Nan ta ke ya gane manufarta. A tare su ka Isa gun shi ba ta yi wata wata ba ta zuba fingers inta kan table in da ya ajiye littafin shi. Sanye ta ke da zobe kala biyu gold and silver hannun ko ya Sha lalle sai sheki yake har ta fingers in Suhaila abin kallo ne. Bai dago ya kalle su illa hannun na ta da ya zubawa ido sai dai in ka kalle shi ba za kace su yake kallo instead littafin shi. "Barka da warhaka" ta fada cikin siririyar muryar da bata San tana dashi ba Sai ranar, ita kanta sai da tayi mamakin kanta like all her body is reacting because of him. "Sannu da hutawa" Yusuf ya fada Amma sai dai gogan shiru ya musu abinsa, ita kam Suhaila gabadaya jikin ta yayi sanyi. A hankali ta ji yace "Sannun ku please ko za a Dan iya rage min nauyin da aka daura min na mutum biyu a kaina?" Ai Suhaila tsaban gudun ya kunyata ta ma Bata jira ya Karasa ba tayi saurin shiga cikin gida Yusuf sai dai biyo ta yayi a baya Amma ya tadda har ta shige dakin ta. Sa Rai ya gane abinda ya Bata Mata Rai Kuma ya San she is blmaing him for what happen saboda ita rayuwar ta ta tsani a wulakanta ta.

Shi dai Muhsin har bayan tafiyan su ya kasa fahimtan komai na daga research inda yake son yi daga karshe ma Dole ya tattara littafin ya tafi dakin shi sai dai still kasa komai yayi in ba tunanin ta da ke fado Mai ba daga karshe Bari gidan ma yayi gabadaya ya nufi gun abokin shi Faroukh, At least shi zai debe mishi kewa. Kai tsaye dakin Faroukh in ya nufa bayan ya gaida mahaifiyar shi, samun shi yayi Yana kallo a system yayi saurin jawo laptop in ya kulle. "Malam Muhsin ya dai za ka Zo ka kulle min kallo?"
Tsaki Muhsin ya ja "am Bored ne Nazo wurin ka kaga ko dole ka rufe kallon ka"
Dariya Faroukh yayi kafin ya kalli Muhsin "haba Malam Muhsin yau Kai da kanka kake cewa you are bored. Ba ku bane ma su wa mutane wa'azi"
"Au isgilanci zaka min?"
"Am sorry friend ya ake ciki, kwana biyu ya kowa da kowa?"
"Kowa lfy"
"Hala mutuniyar ce ta tabo min Kai" harara Muhsin ya watsa ma abokin nashi "kaga Faroukh nifa ban son iskanci ya zaka dinga hada ni da wannan yarinyar?"
"Ah ah ba yar'uwar ka bace na tabbatar halin ta ne kawai bai maka ba Amma 100% ta cika na choices Inka"
"That isn't enough reason, Manzon Allah (SAW) da kanshi yace mu nemi Mai addini" dariya Faroukh yayi "Amma kar ka manta za fa ka iya gyarata kaga Lada biyu kenan"
"Wa ya fada maka? Yau na Fara Mata nasiha irin wannan sun yi nisa ba sa Jin Kira. Wlh Faroukh Ina matukar bakin cikin wannan abin saboda a kullum gani nake Mami ce ba'asi da ta tsawata musu tun farko da ba Haka ba"
"Aa Muhsin Kai ba mamin bace ta Raine ka? Tabbas da laifin Mami Amma Kuma Suma in da laifin su they are matured enough sun San miye dai dai da Kuma akasin ta. Addu'a kawai zaka dinga Taya su dashi ka tuna cewa ba abinda yafi karfin Allah And ka daina barin Abubuwan Nan na bata maka rai Muhsin har kana sa damuwa a ranka, ka San illan da yake ma ka as a doctor ko baku ke Mana wa'azi ba?"
"I will try to Faroukh nagode"
"You love her right?" Faroukh ya fada Yana kallon reaction in abokin nasa, idon sa kadai ya kalla ya tabbatar da abinda ya furtan sai dai ga mamakin shi Kokarin Musa wa yake yi "Haba Faroukh? Me Zan yi da Suhaila? I deserve more than her" zaro ido Faroukh yayi Yana kallon shi sannan yayi murmushi hade da girgiza Kai "so ba ruwan shi da wannan Muhsin, So gwara ma kayi accepting abinda na ke fada ma kullum, am your friend kallo daya Zan maka na karance ka besides Kai ma da kanka ka sani you are just trying to ignore it" shaking Kai Muhsin yayi duk gabadaya yaji jikin shi yayi sanyi "please Faroukh mu bar wannan maganan am not interested" tabe Baki Faroukh yayi "okay let's talk about Medicine tunda can kafi Zama Interested"

We gonna get a lot of Suhaila and Muhsin... What are your thoughts? And by the way who are your favorite couple? Why am I even asking are they even couples? Okay we will get to see that later on... And please let's tag our friends.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top