Babi na sha daya (11)
1st October da ya Kama ranar independence in Nigeria yayi dai dai da ranar da aka San ranar daurin auren Fadila da Najib , three months aka Sa inda ya Kama 1st January kenan, Ranar kuma yayi dai dai da ranar fitowar admission in ABU Zaria inda dukkansu su ka samu courses in da su ke so. Asmau Biochemistry, Fadila Computer science sai Suhaila Mass communication.
Katsina.
Tana murmushin ta ta shigo falon bayan ta gama girki da ke ranar ita ce da yin Amma da ke suna da bako na musamman ya sa dukkansu suka hadu domin yin girkin. takalmin ta kawai ta dauko tayi saurin barin gidan duk da kwala Mata Kiran da Fadila ke yi bai sa ta jirata, gidan Baffah ta nufa direct dakin Goggo Fulani da ta samu tana Sallah. Zama tayi har sai da ta idar tukunna "lafiya Kika shigo kina ta washe baki kaman gonan auduga? Ko dai Angon ne ya Mana albishir" dariya tayi sannan ta ce "Goggo kenan Daman na zo fada Miki na samu admission ne zan tafi jami'a"
Hade rai Goggon tayi "sai kace wani abun arziki ji yanda kike murna, ke yanzu ba za kiyi kokarin sa aure a gaba ba tunda kin samu manema Amma Aa Jami'a ne a gaban ki, me Jami'a za ta tsinana Miki Wanda Sunnar manzo ba za ta Miki ba" dariya Asmau'n ta Kara yi tana fadin "Daman na sa a rina ai ke ma kenan ballantana kuma Hajjah har gwara Mama Amarya ta fiku ganewa" ta Fadi tana jawo kwanon Shan da ke gefen Goggon ta San ba komai bane sai Fura da nono. Saurin dakatar da ita Goggon tayi "Nan kuma fa daya ba ki Isa ba ke ma kinsan Na gauron Yayanki Nan ne da har Mata na samo Mai Amma ya ki aure"
"Haba Goggo kullum Ya Mukhtar kike ajiye ma wa yau sai ki ban"
"In ya shigo in bashi me kinsan duk da gauro ne Ina tausayin shi tunda bai da me Mai"
Turo baki Asmau tayi "Kai Goggo kina fa da wani kuma ni inada mai min in ne?" Ta Fadi kaman za tayi kuka sanin halin Goggon yanzu ta sauko.
"Shknn gashi ki Sha ke da Yayanki ne Kun fi kusa zai zo ya same ki Daman dai Tausayin shi na ke ji saboda shi in Baban shi ba Fulani bane kuma Yana son kayan mu Kinga ke ko Ubanki Ba fulatanin garin Daura ne meye sa bai kawo Miki?" Banza ta yi da ita ta jawo ludayi tana Shirin kaiwa baki taji Sallaman Ya Mukhtar in. Bai jira sun amsa sallaman nashi ma ya shigo ya samu wuri ya zauna sannan ya gaida Goggo. Wani Faduwan gaba Asmau ta ji saboda tun ranar ba ta Kara sa shi a ido ba duk yayi wani iri kaman ba shi ba, walwalan nan da murmushin duk babu. "Yanzu nake Mata maganan zata shanye maka nonon ai" hararan kasan ido yabi Asmau dashi Amma ita ta San sako ya ke son isarwa gareta "Goggo to meye sa kika bar Mata?"
"Saboda na San ko kazo tare zaku Sha"
"Goggo a da kenan, Yanzu Asmau ta koyi rowa ni kuma ban ba wa Mai rowa abu na"
"Ku dai kuka sani" ta Fadi sannan ta cigaba da abinda ke gabanta. Saurin ajiye kwanan nonon Asmau tayi sannan ta mike za ta bar dakin ga mamakin Goggo bai dawo da ita sai ma wani kallo da ya bita dashi sannan ya jawo kwanon ya Fara Shan nonon shi. Tabe baki Goggo tayi "Yau kuma wani irin sabon salo ne kuka fiddo? Daman rufawa maka asiri tayi ai ta auren ai da yafi tunda Kai dai kayi kwantai" Dan murmushin da ya tsaya a labba yayi Jin an hada shi da Asmau "Goggo kenan kullum maganan ki kedai Aure, jikar taki ba rowa kuka min ba kuka ba wani dan bana Nan"
"A toh me zamu tsaya jira tunda ta samu mashinshini ban ma San me ake jira ba da aka ki auren ai kalan a xo a samu matsala kuma"
"Da naji Dadi wlh" bai San cewa maganar zucin da yayi ya fito fili ba sai da yaga irin kallon da Goggo ke bin shi dashi "da ka yi asara kuwa" saurin tashi yayi ya bar dakin sai dai me? Yana shiga cikin gidan su ya hango ta da Umar zaune suna hira sai murmushi su ke suna aikawa juna kallo Mai cike da ma'anoni dayawa, wani irin zafi yaji ya taso mishi daga kirjin shi, ya lura iyakan shi Asmau ke son nuna mishi coz sau uku kenan Yana ganin su a haka, Yana Jin Umar na Kiran shi ya daga mishi hannu kawai ya wuce ciki, furan ma kasa Sha yayi saboda bai da appetite gabadaya, ji yayi duniyan ta mishi zafi gabadaya kanshi juyawa ta ke. Dole ka Nisan ta da ita abinda zuciyan shi ta shaida mishi kenan kawai tsintar kanshi yayi da jawo trolley Yana tura duk kayan da yazo mishi ido. Ummi tana dakin ta ya shiga da Sallama tana ganin shi ta San ba lafiya "ummi Ina son in je Abuja Yau akwai aikin da zamuyi" sakin baki tayi tana kallon shi "Babana me ke damunka ne?"
"Bakomai Ummi Kinga wani abu ne?" Girgiza kanta tayi sannan tace "to miye ma ban gani ba Mukhtar, Banga laifin ka dan ka boye min damuwan ka ba sai dai Ina son ma sani dukkan tsanani Yana tare da sauki, Ka mikawa Allah lamuranka kaji" gyada kanshi yayi kawai domin ya San dole ta gano damuwa a tattare dashi duk da ba San takamaiman me ke damun shi ba "ka gayawa Abbanka ne"
"I will call him"
"Yanzu ne tafiyan Wai? Da ka tsaya na tanadar maka wani Abu" murmushi ya saki sannan ya ce "bakomai Ummi ai dake ma zan biya gidan mummy a Abujan"
"To ma Sha Allahu ka gaishe ta Babana, Allah ya kiyaye hanya ko ya Kare min ka, ka Kula da ibadunka" sunkuyar da Kai yayi Yana sauraron ta ya Saba duk tafiyan da zai yi sai ta mishi irin addu'oin Nan hade da tunasar da shi addinin sa. A cikin gidan ya hadu da su Fadila da sauran kannen shi, duk zaro ido su kayi suna kallon shi cike da mamaki, waving hannu ya musu kawai ya nufi waje har lokacin Umar da Asmau na waje, Umar in na ganin shi ya bishi cike da mamaki coz bai tuna ya ambato zai yi tafiya ba. "Kamawa tayi danuwa" abinda Mukhtar inya fada kenan kafin ya shiga mota, ita dai Asmau tayi rau rau da idanu domin ta San duk abinda zai sa ya bar gidan ya na da nasaba da ita. Ita bata son tashin hankali da karya alkawari shiyasa ba zata iya amsan tayin Mukhtar in ba gwara ta hakura da Wanda ta Saba Kar ta jawo musu matsala dukkansu ukun. Yana ganin tana daga mishi hannu idanun ta sunyi ja kawai ya kauce ya bar wurin. Dai dai kwanan Lady M su ka hadu da Najib ya iso, sai da suka gaisa kafin kowa ya wuce.
Najib na isa straight gidan baba kabeer ya yi bayan ya dawo daga Sallah kenan. Nan da Nan ya samu tarba daga wurin Asmau da sauran kannen su sabanin da da Fadila ce kan gaba wurin mishi komai, shi da kanshi ya sa Asmau ta Kira mishi Fadilan bayan sun gaisa da Ummi. Cikin dar dar Fadila ta karasa side in Ya Mukhtar in da ke daman a can ya ke sauka, shi kadai ne a falon saboda Umar ya fita, gabadaya wani iri ta ke ji she don't Know the right expression to put, she is totally confused ne kawai saboda tunda aka Fara maganan auren su ba abinda ya shiga tsakanin su. Kanta na kasa ta gaishe shi ya amsa Yana Mata murmushin shi da ya Saba. "Kanwata fada mu ke ne? Da saina nema sannan za a zo a gaishe ni?" Saurin girgiza kanta tayi wani Sashe na zuciyan ta kuma Yana mamakin how he is acting normal kaman ba wani abu a tsakanin su. "Ya su Arif?" Ta Fadi tana wasa da yatsun hannun ta "Arif na nan he is eager to see his Aunt once again." Murmushin yake kawai tayi cause everything seems odd to her. "Oya serve me food yunwa na ke ji" Nan da Nan ta hada mishi abincin ya Fara ci yana Dan janta da hira sama sama, a Nan ya mata congrats in admission in da ta samu. Raffan kudi ya ajiye Mata Yan dari biyar biyar guda biyu da leda bayan ya gama "bara in je in gaida Baffah Fadila, I will call you sai ki fada min komai ake ciki na auren Koh, ba lallai mu Kara haduwa ba saboda gobe da safe zan koma ina da aiki" godiya kawai ta mishi sannan ya wuce, ita ce dai tayi acting weird Amman shi ta lura ko a jikin shi. Ya dai amince da auren ne kawai ba Wai don Yana sonta ba, abinda ta fahimta kenan. Sai dai muce Allah ya sa alkhairi aka kulla.
A/N: so na ga comments complaining about not updating frequently. Okay! Am sorry about that but is like i have no option, school and all sai a hankali, the semester is really going fast but still i will be trying In my free time In Sha Allah... So please bear with me.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top