Babi na sha bakwai ( 17 )
A kwana a tashi ba wuya wurin Allah, yau har an wayi gari saura sati day cur bikin Fadila, shirye shirye ya kan kama da kyau su Asmau ba zama gabadaya an zama busy ba matsaka tsinke, to kusan haka ne ya kasance a cikin gidan baba kabeer da ma Baffah gabadaya. Baban ma da ka ganshi kasan akwai sha'ani a gaban shi kasancewar wannan ne karon farko da zai aurar da ya nashi na kanshi haka ma ummi. Fadila kam sai Sam barka don ko ta ga gata daga ko ina, don kusan 1 month to bikin aka hana ta fita in ka ganta a waje to tabbas gidan Baffah ta Shiga, an dauke mata komai da yakamata ace an yi, tayi fresh ta kara wani kyau, ga gyara da ake mata kala kala kana ganin ta kaga Amarya, tayi fes abinta daman gata fara tas.
A bangaren ango kam, uban gayya ba wani shiri ya sa a gaba ba illa iyaka ya tabbatar ya wadata su da komai da yakamata ace ya fito daga gun shi, sabon gida ya siya Dan madaidai ci a kaduna a malali, dakunan bacci uku, 2 parlors sai store da kitchen sai dan filin tsakar Wanda mota bai wuce uku ba za su iya parking, a yanda tsohon gidan shi ya ke ba ayi tsamman yanda tsohon gidan shi yake zai iya zaman a wannan ba amma toh ba abinda rayuwa bai sa wa. Anty meena ya ba wa kudin lefe da ke sunje Dubai ita da mai gidanta, kaya ta hado na gani na fada set daya, akwatunan kan su abin kallo ne komai ya ji, ko da ta sanar mishi ya zo ya gani, CE mata yayi kawai kar ta damu kai tsaye gidan Baffah ya sa aka aika ba tare da ya ganin ba. Aiki ne yasa shi a gab sosai, yanzu haka wani course ya ke a Lagos so bai da lokacin zama, bikin ma squeezing zai ya zo sai da duk bayan kwana biyu ya kan kira Fadilan su gaisa ba tare da wani dogon hira ba, ko ya tambaye ta abinda su ke bukata ba ta fada mai ya lura kunyan shi ma ta ke ji yanzu don haka kai tsaye ya ke kiran Asmau ko kuma Suhaila.
A Kaduna duk a ka mata dinkunan ta, Anty meenan ce za ta tafi dasu komai dai is ready, snacks, event centers, outfits and ol. Wasu kayayyaki ne na gidan Amarya da yayyinta su ka mata order daga china su ka iso kano, kayan su wallpaper, flowers, labule, bedsheets, rigunan throw pillows da kayan show glass, sai wasu electronics. Mukhtar ne yayi placing order in, za a iya sa mishi a motan katsina but he is insisting on ya je ya dauko da kanshi, so yana so su je tare da Asmau. Yana fadawa Ummi ta balla mishi harara "kai kadai zaka je" ta fadi tana hade rai, fuskantar tana son gano wani abu ne yasa yayi saurin chanza zancen "Ummi fa kayan da yawa ne mai saida su yayi order sai na hada mishi da kudina so shiyasa na ke so naje da Asmau ta zabo na fadilan"
Tabe baki tayi sannan tace "Allah ya kiyaye" da murnar nasara nan ta ke ya kira Asmau ya sanar mata tafiyan, ba tayi kasa a guiwa ba ta hau shiri, wurin ukun rana ya biya gidan su ya dauke ta. Bin ta da kallo ya ke har ya tada motan ya bar layin gidan nasu. "Kai Ya Mk" ta fadi cike da tsarguwa ganin yanda ya ke ta faman tsare ta da idanu ya sa duk ta tsargu. "Kin rame" ya fada yana kara kallon ta "ba ki da lfy ne? Stop stressing urself kina wahalar min da kan ki." Murmushi tayi cike da kunya, zuwa yanzu kam ta matukar sabawa da duk wani sabon salon da Yayan nata ya fiddo dashi.
Ba Wanda ya kara magana a cikinsu har su ka bar cikin katsina, ganin haka ya sa Asmau fiddo wayan ta tana yan dube dube bata ankara ba taji hannun shi akan nata suna gogan juna, wani irin shock ne ya ratsa su a lokaci daya da sauri ya fisgo wayan nata domin daman aim in nashi kenan sauran kadan sitiyari ya kufce mai yayi saurin sai ta kan shi "za ki samu accident ko?"
"Za dai ka samu" ta bashi amsa kai tsaye sannan tace "da ka kwantar da hankalin ka ma ajiye wayan zanyi don ban iya danna waya cikin mota"
"Sanin hakan ne ya sa na amshi wayan ai don kar ya saki ciwon kai" sake baki tayi tana kallon shi cike da mamaki, ba ta iya tuna labarin ya taba shiga tsakanin su da wani mahaluki a duniya. ita dai tasan duk sanda ta shiga motan za tayi tafiya kasa tabuka komai ta ke wala Novel ko kuma danne danne ways inta matsa sai tayi ko idanunta sun dinga mata nauyi daga karshe ya sa mata ciwon kai. she fall sick on a journey, zuciyan ta ya dinga tashi kenan jikin ta duk yayi wani iri.
Murmushi ya sakan mata sannan yace "dama kin rufe bakin ki baiwar Allah, you don't need to tell a me a thing about yourself kafin in Sani, I know everything about you" yana gama maganan wayar ta dake kan cinyan shi ya hau ringing, a tare su ka kai idanuwan su kan fuskar wayan sunan Umar ne ya nuna hade da emoji in heart a gefe. Kallon shi ta ke ta ga ko zai bata wayan sai dai tuni annurin fuskar shi ya kau, ya hade rai kaman bai taba mata dariya a haka wayar ta katse kafin ya dau wani ringing in wannan karan switch in ya danna volume in ya dauke. A hankali ta fara mishi magana "kayi hakuri Dan Allah ya MK ka barni in dau wayan nan kaga fa gabadaya na mata yace min Yau zai dawo daga Lagos zai biyo Katsina direct yana so mu hadu, kar ya ga kaman ina mai wulakanci ne" tsaki ya ja hadde da daukan wayan ya kashe gabadaya sannan ya tura cikin aljihun jeans in shi, idanuwan shi sun rikida sunyi ja nan ta ke jikin ta yayi sanyi saboda ba ta tuna ta taba ganin shi a haka ba. Shiru tayi ta koma jikin kujeran ta kwantar da kanta sannan ta sa gyalen da ke kanta ta rufe fuskan ta kirif. Tunanin yanda za ta fuskanci kalubalen da ke gaban ta ne ya fara fado ma ta. Ta ya za ta kalli yan uwa biyun tace ta zabi daya daga cikinsu? Na farko Umar Wanda ko ya San da maganar su ko kuma Mukhtar da tunda ta taso ya ke nuna mata gata da kulawa, tun tana karama ya ke dauko ta daga gidan su ya taho gidan baba kabeer wai ya tazo hutu wurin shi, kusan shi ya yaye ta lokacin da Ummi ta dauko ta yaye wurin mama, ko don kaunar da Ummi da baba ke mata sun cancanci taso dansu tabbas ta San ummi za tafi so ace Dan ta ta zaba ba Dan dan uwanta ba, ta tuna farin cikin da Ummi tayi lokacin da taji zancen su da Umar. Shin zai fi haka in taji Mukhtar ma na Neman ta? Ko ba za ma taso abun ba? Shin ba za ta hada Ummi da yan uwanta ba? Anya ba fitina ta dauko ma kanta ba domin Ummi ba ta kamaci wannan sakayyan daga gareta ba... Ba ta San lokacin da hawaye ya fara biyo idon ta ba sai ma sheshekar kukan da ta fara ba ta ankara ba sai ji tayi yi alamun an daina tafiya. Sai a sannan ta dago kanta cike da mamaki ta na kallon shi, yanayin da ta ganshi abun kwata kwata ba kyau don gwara ma dazu gabadaya ya rikida kaman ba Mukhtar in nan ba fuskar nan gabadaya ba alaman dariya sai wani huci yake hade da ajiyan zuciya "in maida ki katsinan ne ki ganshi?"
"Ni ban ce ba" ta fada zuciyan ta na dar dar dan har gani ta ke kaman zai iya zabga mata mari yanda ya zuciyan nan, daman ta San zuciyan shi kwata kwata ba kyau amma na yau ya kazanta, ita abun ma mamaki ya ke bata dan bata ga abin tashin hankali ba, inda laifi to shine ma ya mata.
"Kar ki kara min kuka a mota Saboda Namiji in son ganin shi kike sai in maida ki" ya fadi yana huro iska, kala ba tace ba hakan yasa yayi kwafa sannan ya tada motan.
Ba ta kara magana ba sai da yake ta wani irin kwafa, ita abun ma dariya ya bata da ta gaji da shirun daga baya bacci ya kwashe ta. Wani irin gudu Mukhtar ya zuba tsabagen yanda ya ke a zuciye, sai dai farkawa tayi kawai ta ga sun iso garin kano, Direct gidan baba Muhammad ya nufa da ke sharada kaman tace mishi ya kai ta Sokoto road wurin Suhaila sai dai ba ta ga Fuskan hakan ba.
Dai dai kofar gidan su kayi parking, ga mamakin ta Suhaila ce ta fito daga motan fuskan ta a daure saurin fita tayi tana kwala mata kira shi kuma Mukhtar ya karasa wurin Muhsin da ya hango yana fitowa daga motan ya bashi hannu suna gaisawa. Da fara'a Suhaila tayi hugging inta tana fadin "Yan mata zuwa ba notice" dariya tayi sannan ta ce "ai ban ma dauka kina nan ba Ina niyyan Anjima in sawa Ya Mukhtar rigima sai ya kaini" dariya Suhaila tayi tana fadin "iyyeh kice tare da saurayin ki kike" kyabe baki Asmau tayi kaman abinda Suhaila ta fadi karya ne da ke daman ta dade tana tsokanan ta da hakan tun kafin Mukhtar yace yana son Asmaun daman abu ne Wanda kowa ya dade yana expecting... "Kya ji dashi Suhaila ke mai ya hado ki da naki Saurayin" tsaki Suhaila ta ja tana fadin "Ya muhsin ya sa min ido amma zan yi maganin shi" ita dai Asmaun murmushi tayi mai cike da ma'anoni sannan ta ja hannun suhailan domin ta je ta gaida Muhsin in.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top