Babi na hamsin da shidda ( 56 )

Tun Suhaila na sa ran Muhsin zai neme ta har ta cire. Yau kwana uku kenan da yin case insu na mahmud. Kokarin mantawa da lamarin shi ta keyi Amma Sam Ina abun ya ci tura.

Da sallama ya shiga cikin gidan nasu. Kasancewar week day ne ya sa ba kowa a gidan. Mami da Abbah duk suna aiki. Yaran sun tafi school sai Suraj da yake kyautata zaton baya gidan. Kamshi da yaji na busowa tun daga kofa ya sa ya gane Suhaila na gida don ko ba su da cook a gidan.

Direct kitchen in ya nufa. She is very busy tana hada kayan salad in da ke gaban ta. Ko sallaman shi ba ta ji ha saboda ear piece in da ke makale akan kunnen ta. Da karfi ya buga kofan kitchen, hakan ya sa tilas ta waiwayo. Tayi mamakin ganin shi Amma sai tayi kokarin boye hakan. Kasa magana tayi kawai tayi still tana kallon shi.

Siririn murmushi yayi yace "Sannu da aiki princess" kallon mamaki ta bishi dashi coz shi can't remember ya taba Kiran ta da wani suna makamancin hakan.

"Fushi kike da wani dan na koran Miki prince?"

Sai yanzu ta gano kan zancen. Tabe baki tayi tace "Ina wuni? Ya aiki? Ya sister Rahma?"

Idanuwan shi na kanta. Ya karasa dinning in kitchen in ya zauna.

"Tana lfy, tace in gaishe ki"

"Ina amsawa, ta warware?" Ta fada a ranta tana fadin ba sai ka nuna min kana son matar ka ba by choosing to ignore the rest gaisuwan.

"Ahh ta warke sosai. Let me help you"

Kallon shi ta danyi. Kaman za tayi objecting sai ta basar ta dauki salad in da ta ke yanka wa da tumatir da cucumber da sweet pepper ta ajiye mai kan dinning table in.

Dauka yayi ya cigaba da yanka Mata ita kuma ta fara kokarin hada stew.

"Yanzu ki daina kiwuya ne?"

Kallon shi tayi kaman za tayi kuka tace "I don't have any choice, zama gida da maza gabadaya"

"In kinyi zuciya kiyi harama ki bar gidan mana"

Girgiza Kai tayi tace "bayan ka koran min saurayin"

Ba ta fuska yayi yace "me yace Miki?"

"Nothing"

"You are lying"

"He said he couldn't come kuma nasan akwai abunda ka fada mai ne shiyasa"

Hararan ta yayi yace "ke dai yi min sharrin kawai"

Shiru tayi ta cigaba da aikin da take yi.

"So yanzu har ignoring questions Ina ake? In yi magana a share Ni"

Kaman za tayi kuka ta kalle shi. Don har ga Allah shi is not in the mood of talking. Ya ma barta da halin da ya ke saka ta Amma zai zo ya cika ta da surutu.

"Na ishe ki koh?"

"Wai what happen ya Muhsin? Da baka da surutun nan."

Shiru yayi na Dan seconds kafin yace "You happen" a hankali ya fada Amma he is very sure taji shi.

Cike da kunya yace "Nine kike cewa na cika magana ko? Thank you and don't worry i won't talk again" yanda yayi maganan a hankali ya sa jikin ta yayi sanyi duk da ta San tsokanar ta ya ke.

Bai ko kara maganan ba har ta kammala girkin ta amshi salad in ta hada. Shi dai yana zaune a kitchen. Fridge ta bude ta dauko zobon da ta hada since, zubawa tayi a jug ta ajiye mishi akan dining in. Bai ce komai ya dauka ya Sha, Daman ta San yana son zobon.

Yana zaune har ta gama tattare kitchen in sannan ta ce "are you eating?"

Yi yayi kaman bai jita ba sai can yace "ashe ke marowaciya ce?"

Wato dan tace he is talking too much shine ya koma Mata miskilancin nashi kenan.

"Ban so in zuba ne kuma you are not hungry"

"Bar abinki ban so zanci na matata" ba tace kala ba ta tattare komai ta ajiye shi wurin shi.

Sallaman Abbah da Mami su kaji. Kusan tare su ka fita kitchen. Daman dai Abbahn ya ke jira, wurin shi yazo.

.....

Ya dade yana knocking a door in gidan Amma shiru kake ji. A tsorace ya je ya amso spare wurin Guard in estate in. Yana addu'a a zuciyan shi ya shigo gida yana Kiran ta Amma shiru kake ji. Dakin ta ya nufa ba ta nan har toilet. Tuni ya kara birkice wa gashi tun dazu ya ke Kira phone inta switch up. Dakin shi ya nufa da azama, a hankali ya saki ajiyan zuciya ganin kayan shi baje akan gadon. Ita kuma tana gefe sai kwasan bacci ta ke yi.

A hankali ya karasa ya gyara Mata kwanciya, a ranshi yana tunanin wannan baccin lfy kuwa? Hakura yayi ya jira ta farka. Gyara Mata kwanciya yayi sannan yayi wanka yaci abinci. Har ya gama ya karasa gyara kayan da ta bari ba ta farka ba.

Ganin abun ba na kare bane yar anyi magreeb ba ta farka ba ya sa yayi niyyan tada ta. A hankali ya dinga tapping inta yana Kiran sunan ta Amma shiru. Dabara yayi ya hura ma ta iska a kunne, a firgice ta tashi da addu'a a bakin ta tana kallon shi ta turo baki kaman za tayi kuka tace "shine za ka tashe Ni" hade hannu yayi kaman mai neman gafara yace "afuwa babe kinyi missing magrib fa" kallon shi tayi kaman mai doubting abinda ya fada tace "magrib kuma? Ko dai Azahar"

"Don't tell you have been sleeping since" wayan shi ya ciro ya nuna Mata time.

Ware ido tayi tace "I missed all the prayers fa kenan. And school, innalillahi Ina da text" kaman za tayi kuka ta fara laluban wayan ta ta kunna. Mssgs ta gani na shigo na course mates inta.

"Why did i sleep that long? Ya mukhtar please ka kaini asibiti" ta fada kwalla na zubo Mata.

Jawo ta jikin shi yayi yana lallashin ta "Don't cry babe its okay. Kiyi sallah sai muje" ba musu ta tashi ta nufi bayi. Jikin shi gabadaya yayi sanyi don tun dawon su daga trip in da su kaje ya lura da ita tana so bacci sosai, ko da safe da kyar ya ke iya tashin ta. Two weeks su kayi suna zagaye America. Ya kaita countries dayawa for a tour.

Tana idar da sallah ta juyo kaman za tayi kuka tace "wlh Ina jin sosai kaman zanci bbu"

"Let me get you Yoghurt a fridge kafin mu fita" tsaf ta shanye yogurt in sannan ta shirya su ka tafi asibitin.

Suna zaune suna hira aka ja Mata jini su ka tsaya jiran results. Bai yi wani talking long ba lab scientist ya gama ya turo su wurin doctor in da suka gani.

Doctorn ne ya fara musu bayanin result in "I think everything is normal. We check The FBC, Bp, Lp and then pt which shows a positive result. So congratulations madam" in a confusion su ke kallon doctorn yayin da ya ke musu maganan yawan baccin is due to the pregnancy.  Shawarwari ya basu sosai sannan ya rubuta Mata wasu pills.

Murmushi kasa daukewa yayi a fuskan ta har su ka isa mota. So ta ke ta karanci yanayin fuskan shi ganin yayi shiru. Sai da ya tada motan ya kalle ta yace "babe are you happy?"

A tsorace ta kalle shi tace "are you not? Me kake nufi"

"I thought you are not ready for it" kallon shi tayi sannan ta hada rai ba ta kara cewa komai ba har su ka isa gida. Ko abincin da su kayi order ma ba ta kalla ba.

Tsaf ya karance ta burin shi daya Kar tayi misunderstanding inta. A dakin ta ya shiga ya samu ta kudundune cikin bargo, kokarin dago ta yayi surprisingly yaga hawaye a idon ta. "Babe me yasa ki kuka?" Cike da damuwa ya ke maganan yana kokarin karantan ta.

"I thought you love me..." In confusion ya kalle ta "don't tell me you are doubting"

"Right now i have no other option"

"Kinga Asmy you are misunderstanding. Subhanallah! Ta ya zan ki karuwan da zan samu daga gareki. Taya zan ki kyauta mai girma gun Ubangiji na. Kawai nayi tunanin we have never talked about it shiyasa nayi tunanin you are not ready ne. Knowing me kinsan i will go with everything you want kuma na ga ko na fara Miki maganan murmushi kawai kike"

Kallon shi tayi ta girgiza Kai "meye sa zan ki haihuwa Ya mukhtar bayan Mata dayawa na nema ba su samu ba. Ni har Ina da wani zabi? Am so scared right now if you are not appreciating it" murmushi yayi ya riko hannayen ta duka biyu sannan yace "Ina son ki sosai Asmau da ke da abinda ke cikin cikin ki, Ina mai godiya ga Allah da ya bani wannan kyautan." Ita ma murmushin ta mai tace "Ya mukhtar i already loves my baby more than anything in this world" kallon cikin ta ke tana jin wani farin ciki na ratsa ta kaman ta tsaga cikin ta fiddo dan tun yanzu.

"Har Ni?" Without any doubt ta mishi nodding kanta.

"Oh am jealous. Ta so kici abinci maman baby." Ba musu ta sauka ta bishi zuwan falon. Jin ta take a wani sabon duniya na daban. 

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top