Babi na daya (01)

Babban gida ne sosai da aka mishi ado irin na mutanen da. Amma Kuma a kayate ya ke da furanne ko ta Ina daga waje har cikin gidan. ya kunshi sashe Uku a jere in aka hada da na Mai gidan ya Kama hudu kenan sai Kuma sashe daya da aka ajiye musamman don Baki kawai.

Alhaji Abdullahi Malumfashi Babban mutum ne da aka mishi matukar sani a cikin jahar katsina da ma kewaye gabadaya, Kai ko kwatancen Unguwan da ya ke za ayi to tabbas da gidan shi ake yi. Ba komai ya jawo hakan ba sai dan kasancewar shi shaharraren Dan kasuwa da Allah yayi wa ruwar arziki tun yana Dan saurayin shi ya baro Malumfashi gun wan baban shi da ke Nan cikin katsina. yayi suna ba kadan ba.

Allah ya azurta da yara da dama har manyan su kayi aure su ka haihu ba a daina haihuwa cikin gidan Alh Abdullahi ba domin kasancewar shi Mai son zuri'a sosai. Har ma cikin jikokin nashi akwai wadanda su ka girme yaran nashi.

Duka gidajen Yara mazan a jere yake sannan wasu na Kallon wasu, duk da akwai Wanda ba garin su ke da Zama ba Amma duk da haka Alhaji Abdullahi sai da ya musu gini saboda su sauka in sun Zo garin. Ko kadan ba sa wasa da zumunci tun suna kanana su ka taso da hakan saboda tarbiyyan da mahaifin su ya daura su a Kai. Yawancin hutu a katsina su ke dawowa su yi ko basu so ba zasu turo yaran nasu.

A takaice da kullum gidan cike ya ke da mutane. Yaran, jikoki, Yan uwa da abokan arziki gabadaya. Hakan ne ta kasance a Rana irin ta yau sai dai wannan ma ya zarce na kullum. duk girman gidan Nan sai da aka yi occupying in shi a sanadiyar auren Yar shi mace da ake yi wato Aminatu. Biki ake na gani na fada irin na manyan mutane masu fada aji a kasa. Amarya dai sai dole gidan Babban yayansu Kabeer ta tare da kawayen ta saboda gidan nasu ya cika dam kuma yafi kusa da gidan su. Jikokin gidan ma yan Mata duk suna tare da ita don ko sun kasu kamo ta da kadan za ta girme musu.

••••

Sauri sauri gudu gudu Fadila diyar baba Kabeer in ta shigo tana kwalawa Asmau Kira wacce ta ke diya ita Kuma ga Mami Aisha babbar dakin Hajiya fulani. Suahila da ke kusa da Asmaun ne ta ja tsaki tana fadin "Deela Miye Haka sai kace ba Yan Mata ba?"
Gabadaya kwashewa da dariya su ka yi har da Amaryar, inda ta ke fadin "Yan ya'ya' na Kun girma"

Meema ce ta kalle ta cike da mamaki "Kai Anty meena sai dai kace Kinga yarintan mu, I think mommy cewa tayi da 2 years ki ka girme ni su Asmy kuwa 3 ko ba Haka bane"

Hararan ta Aminatu ta yi tana fadin "oho dai ko ma miye ku dai Ya'ya'n yayyina ne"

"Ku bar wannan maganan tukunna" Fadeela ta katse su "Asmy kinsan me? Ya MK ya dawo"

"What? Allah ya sa ba Wasa kike ba right? Shine ko ya fada min"

"Wlh am not lying a waje na gansu tare da su Ya Muhsin da Ya Faisal har ma mun gaisa" Ai Asmau ba ta jira karshen zancen ba ta figi takalmin ta da dankwali a hannu.

"Ke dawo dawo" Fadeela ta kwala Mata Kira "Ya Zaki fita Haka, Kinga mazan da ke waje har da Ya Umar fa" turus tayi Jin an ambaci ya Umar, ba lakka a jikin ta ta dawo ta zauna. Nan fa su ka hau Mata tsiya Wai Daga Kiran sunan Umar gabadaya jikin ta ya fara rawa.

Asmau da Umar da ya kasance da ga kanin Maman su Fadeela wato Matan baba Kabeer kenan. Soyayya ce tsaftataciya a tsakanin su, gabadaya iyaye duk sun sani Amma an bar maganan akan sai ta fara makaranta zuwa 200 level za ayi auren da ke shima Bai gama settling ba. Already ta gama secondary school tana jiran admission ne. Shakuwar ta da Mukhtar ko ya samo asali ne tun tana karama, yawancin hutu ta na gidansu da ke baban ta ma abokin baba Kabeer in ne don Haka zumuncin sai ya Kara kulluwa. Tun tana karama jinin su ya Zo Daya da Ya Mukhtar in nasu, ya matukar nuna Mata gata Wanda ya cigaba har zuwa yanzu hakan yasa ya samu babban wurin a zuciyan Asmaul Husna.

Tun bayan azahar aka fara Shirin kamu da za ayi a nan cikin gidan su Amaryar. Babban wuri ne sosai a ta gefen cikin gidan har ma yafi cikin asalin gidan girma. Wurin ya kayatu sosai yayi irin na al'ada yanda ya kamata sai ya saje da yanayin ginin gidan ya bada amazing colours sosai komai na gargajiya ne a wurin. Kawayen Amaryan ne su ka dauko ta zuwan wurin bayan an gama makeup su ko Ya'ya'n nata su ka biyo su a baya. Gabadaya Kan su a kasa su ka taho gudun kyara da ga gun yayyin su maza da ke waje, a cewar su zasu bada su gaban samari su dau kwalliya, gabadaya yayyin nasu miskilai ne Wanda da Basu daukan raini ko kadan, shi dama Ya Mukhtar Asmau kawai ya ke sakarwa fuska sosai, Ya Muhsin ko ustaz ne tuni ya tsare ka da wa'azi, Ya Faisal ko in za ka cinye kanka ko kallo ba Ka ishe shi ba, miskili ne sosai don ko cikin Yan uwan shi maza ba magana ya ke sosai ba ba uhmm ba Aa, Meema dai ta ce gidadanci ke damun shi. Sai Ya Najib shi ko fada gare shi sosai shiyasa su ke tsoron sa, Amma Kuma Yana da kirki over ma ga kyauta sai dai shi ko bikin ma bai Kai da zuwa shiru dai ake jin shi har yanzu. Su ne kadai Daman mazan babba cikin jikokin sauran duk Yara ne.

Ta kasan ido Asmau ta hango Ya Mukhtar Yana ta faman waya, ta yi kewan shi sosai kaman ta je ta yi Mai magana sai dai tana tsoron Yayyin nata don wasu ma ke ta watso musu harara tunda su ka fito ga Kuma Umar na wurin Kar ta je ya basar da ita.

Cikin birgewa aka fara events in da ya samu halittar manyan mutane kala kala, ba wata matar Babban mutum na ci katsina da ba ta Zo ba, da ke akwai zumunci sosai a tsakanin su.

Sai da aka fara daukan hotunan sannan mazan su ka shi shigo. Suna cikin daukan hoto da Amarya ya hango ta tare dasu Abakar, direct ya nufi wurin su "Babban Danmu" Khalipha ya fada cike da tsokana. Dakuwa Mukhtar ya mishi "dalla go gefe dukkan ku ukun ban iyayen da ku tunda Kun Bari na girme ku"
"Ah ah Babban Da ba gashi ka hangomu ka Zo gaishe mu ba" Usman ne yayi magana wannan karon. "ALLAH ya kyauta ga gun wacce nazo Nan" Ya nuna Asmau da ke ta faman musu dariya, hannun ta ya ja Yana hararanta "Fushi na ke dake Asmy in dawo ko ki Zo ki gaishe ni ko"
"Sorry Ya MK, hayaniyan biki ne sai ma dazu Fadeela ke fadan min ka zo"
"Shknn let take a picture with the bride" "oya dauke mu da Asmy da Anty Meena" yayi ordering camera man in. "Au yanzu na Zama Antyn kenan" Aminatu ta fada tana dariya bayan an gama pic in "ya zanyi tunda kin Riga ni aure" dariya ta dinga Mai tuna yanda ya dinga musu da ita sai ya riga ta yin aure.

Ko da aka gama daukan pictures in hannun ta ya rike "za ki raka ni Unguwa"
"Ya MK akwai abubuwan da za muyi fa su Suhaila za su ta jirana"

"Yanzu za mu je mu dawo" Ba musu ta bishi saboda Bai kyaletan zai yi ba. Abinda ta ke gudu shi ya auku Yana hango shi ya fara kwala mishi Kira "Ina ka shiga Ina neman ka, I need the car key"
"Okay" kawai ya ce ya ciro key in ya bashi Yana ta kokarin hango fuskan Asmaun sai dai gabadaya kasa ta ke kallo, ga jikin ta da ke rawa Tsabagen tsoro. Bawan Allah Umar Bai ce komai ba har su ka fita daga gidan.

Wurin wani friends in shi ta raka shi ya amso sako, abinda ke Bata mamaki duk inda suka hadu da abokin Ya MK to tabbas sun Santa zaka ji suna wannan ce Asmau right? Basu dawo gida ba sai da ya biya Royal su ka siyo snacks da ice cream. Ya San ta ba gwanar cin abinci bace.

Ranar ko dadewa su kayi suna Hira da MK Yana Bata Labarin Florida.
Ko da Umar ya Kira ta da dare gaisawa su kayi kawai ta je tana Jin bacci don dole hakanan ya kyale ta.

Washegari da safe tun kafin Karin kumallo Hira ya kaure tsakanin su. "Oh Ya Najib dai Anty Sumayya gabadaya ta dauke mana shi" Meema ke maganan tana kokarin hada tea "ke dai bari Meema ace gabadaya ana taro Amma ba Kai a ciki" Asmau ta amshe zancen tana tabe Baki "shi Kam dai bai yi sa'ar Mata ba wlh" hararan ta Fadeela tayi sannan tace "Wai na ga ikon Allah ku dai ba ki son matan Nan Kuma wlh ba laifin ta bane kadai Shima har dashi ai Amma gabadaya kowa ita ya ke daura was laifi baiwar Allah gashi tana da kirki" saurin katse ta Asmau tayi "kice dai tana Miki kirki"
"Ni Fadee bansan me matan Nan ta ke Miki kike yabon ta ba wlh, Mata sai iyayi da ji da Kai gani ta ke kaman ta fi kowa" Meema ta yi maganan tana yamutsa fuska ta Kara da cewa "ni yaran ta ma nake tausayi wlh" Suhaila dai kala ba ta ce ba musu yanda kasan ba ta San kan maganan da ake yi ba ma gabadaya. "Wlh ku dinga Mata adalci ko don yaran ta after all ma Dan uwan naku ba karamin sonta ya ke ba a hakan"

"Opportunity in da ta ke using kenan ai ba ta maida kowa wani abun tsiya ba wanda ta ke gani da gashi, inda ta arziki ce ai sai dai ta Kara hadashi da yan'uwan shi Amma Aa ina, nata kawai ta sani, jifa yanzu Dan Allah biki ake yi ko alamun su babu. Sai yafi one year bai zo katsina ba. Wannan wani irin rayuwace toh?" Asmau ta fada cike da takaicin lamarin.

"Kyale Fadee Asmau, ni nama Lura ke kadai ta ke sakar wa fuska ko da yake ke kadai ma ke jure zuwa wurin nata" Meema ta karashe zancen hade da hararan fadila.

"To a biye Mata ne? Ko dan Ya Najib da yaran ta ai, da ta nuna halin ta ai da sai aci maganin zama da ita Aa sai kowa ya guje ta Kinga ko ta samu abinda ta ke so kenan Kuma wlh zaki Sha mamakin kirkin ta at times Allah"

"Aa Fadila ke fa kadai ta ke ma wa Kuma don taga Shirin da kike da Ya Najib in ne kawai Amma its Kam tun Yana neman ta aka samu matsala wlh. Ya je wurin ta ta mishi karyan Bata Nan fa alhalin ba ta San ya ganta da wani a waje ba ko kin manta Labarin da ya bamu lokacin da ya Kai ta Kano makaranta tace za ta ga wani Dan uwanta a hotel. Ya fa ajiye ta suka Dade suna magana a ciki sannan da su ka fito Wai ya Bata wuri a mota su shiga su Karasa maganan su, yace ba zai yiwu ba wannan Kuma ba ta Isa ba ya tuka motan shi ya tafi. Abubuwa fa kala kala a gaban ki Goggo tace Mai bai yi Mata ba Amma so ya dibe shi ya ki ji" Asmau ta fada tana kallon fadila. "Ai matsalan da aka samu kenan soyayyan da ya ke Mata yayi yawa ne wlh"

Sai a sannan Suhaila ta ja tsaki sannan ta yi magana "Da safiyar Allah Kun ishe mu da maganan Wato Dan Allah haba, ta je tayi mana is her life Kuma hakan ta tsaba. Its a free life kowa yayi abinda ya ke so" ta fada hade da shrugging shoulders inta.

Meema ce ta galla Mata harara "Dallah Malama kar ki ishe mu in zance bai Miki ba ai sai ki kyale mu ko? Ke kowa duk abinda yayi dai dai ne lifestyle in shi kenan kar a Mai gyara ko?"

Tabe baki tayi "Karya ne to, kowa fa ya San daidai sai dai yaki ta so you can't change everybody. Whatever ma dai spare us the talk please" tana gama zancen ta jawo ear piece inta ta makala a kunne.

A tare su ka ja tsaki "in kin San kina da solution daman me ye sa kika tsaya kina magana" Asmau ta Fadi hade da galla Mata harara . "Mutum shi kullum makale da ear Piece" Fadeela ta amsa. Meema ko shiru kawai tayi saboda ta San wacce su ke da ita ma ba ta San ma suna yi ba so its of no use.

Sai dai su ka shirya tsaf su ka karya sannan su ka nufi dakin da Amarya da kawayen ta su ke...

A/N: and here it is as promised. Hope you will like it?

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top