Babi na biyu (02)

A hankali ta ke tafiya kace dawisu, Dam! Ta ji gaban ta yayi wani irin bugawa sai dai tana dago idon ta su kayi four eyes dashi Yana zuba Mata harara ta gane dalilin faduwar gaban nata. Sum sum ko Kara Kallon shi ba tayi ba ta sa Kai ta wuce abinta domin in ma miskilanci ne to tabbas ita ma A ce. Ba Wai Mai Mata kwarjini bane kaman yanda ya kewa sauran Aa ta yadda he is charismatic sai dai Kuma ita ma self confidence inta ba zai bar ta taji tsoron shi ba.  Ko Kara Kallon sa ba tayi bata SA kanta cikin gidan bikin aiko ta ci karo da Suraj kanin shi yana ta faman Mata smiling. "Suhaila wannan irin kyau haka" murmushi tayi Mai kayatar

wa ko Bai fada ta San ta kwaso kyau domin ko Daman ita in Mai kyaun ce. "Thanks Suraj Mami na ciki ne?"
"Ehmm tana verandan Baffah (Alhaji Abdullahi)
  "Bara naje ta aika a kirani ne"
  "Emhmm Naga mutumin naki Hala ko gaisawa ba kuyi ba"
"Harara na fa ya dinga yi niko na dauke Kaine nayi shigowa ta nasan yanzu haka magana zai min akan gyale na"
"Ke dai da ya Muhsin rigiman ku sai ku, bara na bashi sako" ya fadi sannan ya karasa wurin Muhsin in da ke tsaye Yana Kallon su.

    Suhaila ya' ce a gun babansu Muhammad na dakin Uwargida Hajjah fati. Ita ce Yar fari tun wurin haihuwar ta Allah yayi ma Mahaifiyar ta rasuwa. Da Baba Muhammad da Yayan shi Abdulrahman gabadaya a kano su ke da Zama don Haka bayan rasuwar matar shi sai ya bar ma Mami saudah matar wanshi Suhaila, tayi farin ciki ba kadan ba Saboda Allah Bai taba Bata haihuwar Ya' mace ba gabadaya maza ne. Muhsin, Suraj, Yusuf sai auta Sabir.

  Ana gama daurin aure aka fara Shirin tafiya da Amarya gidan ta da ke Kaduna. Karfe Daya dai dai motocin Kai Amaryan su ka bar katsina cikin ikon Allah karfe hudu dai dai suna Kaduna, sai da aka fara zuwa gidan Yayarta Safiyya da ke zaman garin su kayi Sallan la'asar kafin aka wuce da ita gidan surukan ta sannan daga bisani ta karasa gidan ta da ke kinkinau. Baiwar Allah ta Sha kuka tare da Yan uwanta da su ka Taya ta. Da dare aka shirya dinner da ya samu halittan manyan mutane sosai da ke angon ma Dan manya ne, shima asalin shi dan katsinan ne su ke Zama a Kaduna.

Ranar Sunday gabadaya aka watse kowa ya Kama gaban shi aka bar Amarya daga ita sai halin ta.

Fadila matsawa tayi sai ta je gidan Ya Najib don da mamaki taji shiru haka bai Zo bikin ba. Da farko su Meema kin zuwa su kayi sai da tayi ta rokon su sannan su ka tafi. Anty Sumayyan ce kawai a gidan sai babyn da Yar wata bakwai sannan masu aiki. Ba yabo ba fallasa ta tarbe su ta sa aka kawo musu abin Sha sai dai ba wanda ya dauko sai Fadila, Kuma ita ma fadilan kawai ta dinga ja da Hira "Fadila kwana biyu ko waya Koh?" Murmushi kawai fadilan tayi don da suna yawan waya daga baya abin ya yanke. Shiru ba ta ga Ya Najib ya sa ta kasa shiru ta yi magana "Anty Sumayya ya Najib fa?"

"Najib ba ya Nan yayi yafiya Yana Dubai kwanan sa Uku kenan a can"

"Au Allah sarki ai ko ba mu ji labari ba"

"Ehmm da ke tafiyan ta zo a kakkauce ne"

"Arif fa?"

"Wai Arif ai yayi 2 weeks a gidan sister da ke Abuja na Kai shi ya ga yan'uwa ne wlh kinsan in yaro bai shiga cikin yan'uwa sai kiga ya taso bai San su ba to me aka yi kenan"

"Ehmm gsky da ke wasu basu dauki Yan uwa da mahimmanci ba ai bayan Manzo Allah sosai yayi magana akan zumunci. Duk wanda ya yanke zumunci ba ya tare dashi ko. Sai kiga wasu sun yi preferring wasu akan wasu alhalin duk Dan uwanka ne" Da biyu meeman ta yi maganan Kuma gabadayan su sun gane.

Ba su wani Dade ba su ka tashi za su wuce kasa shiru Asmau tayi "Anty Sumayya ba ki tambaye mu biki ba ba ki samu zuwa ba" maimakon ta ji kunya Aa Sai Fadila ma ce ta ji Mata. "Ehmm fa Aminatou ta yi aure ance Nan garin aka kawo ta ko?"

"Ehmm" kawai Asmau ta amsa.

"Kinga ita ma sai a dinga Kai Mata Arif ya ga yar'uwar shi tunda tana kusa" Meema ta Kara Fadi. Ita dai Suhaila magana daya tayi "a gaida Arif na kawo mishi chocolates baya nan baby Kuma she is young Dana bar Mata"

Da jimamin halin ta su ka wuce. Sai dai ita ko a jikin ta ma.

•••

    Katsinan Dikko dakin Kara.

Mukhtar ne zaune da Mahaifiyar shi yana nuna Mata tsaraban da ya kawo ma kowa sai faman sa mishi albarka ta ke. Wasu hadadden laces ya fito dasu a leda da bakan riga hade da takalmi sai sarka da dan kunne fashion masu mugun kyau.
"Wannan fa?" Ta bukata
"Wannan na Asmau ne Ummi" girgiza Kan ta kawai ta yi "Kai dai da Asmaun Nan na ka sai godiya, wato tsaraban nata ma daban ne ko in auren ta ya taso Mai zaka Mata"

"Habawa Ummi Wannan ai nawa ne Kuma sai inda karfi na ya kare" Yana murmushi ya tashi ya bar wurin ba tare da ta gane me yake nufi ba. Dai dai Lokacin motar su ta iso daga Kaduna. Ba dadewa ba Ummin ta nuna musu tsaraban ta su Nan fa su ka hau murna suna godiya shi ko gogan ko Kallon su Bai ba balle ya tanka sai ma barin wurin da yayi. Asmau Nan ta ke ta Kira Mahaifiyar ta Mami Aisha ta sanar da ita kyautan da MK ya mata ita ma godiyan tace ta mishi.

Da dare yana zaune yana Kallo a system in shi ta shiga dakin shi da sallama rike da tray in abinci a hannun ta.

"Shigo Mana Asmy" ya fada still hankalin shi na Kan Kallon da yake yi. "Sannu" ya ce Mata bayan ta ajiye tray in.

"Me kake kallo haka Ya Mukhtar gabadaya ka bawa attention Haka" ta tambaya ganin yanda gabadaya ya mikawa Kallon hankalin shi.

"Wani American series ne The hundred kin San shi?"  Tabe baki tayi kafin ta girgiza kanta in annoyance "ni ban Kallon American series sai dai irin Desiny Haka da Kuma science fiction"

"Kar ki damu Zan koya Miki..." Saurin katse shi tayi "Ni Ya MK ban so na fi son Indian films da Koreans, Philippines ma sun iya film"

"Okay let makes a deal, ki ka kalla favourite ina Nima Zan dinga Kallon naki"

Tabe baki tayi alaman she is not ready to comply "Ya MK forget kawai food is ready"

"Waya dafa?"

"Fadeela ce"

"Then am not eating"

  "Ehm ehm Ya Mk ka ci Mana" turo bakin ta tayi cike da shagwaba.

"Okay, in kina son inci meye sa baki min preparing da kanki ba?"

"Am sorry next time Zan ma Allah" ta fada in a sorry voice.

"To sauko muci" ba musu ta sauka ta zuba musu jollof in a plate, a hankali ta ke ci ta dinga Mai wayau kusan shi ya ci 90% in abincin kafin ya kare.

"Ya Mukhtar i shall get going"

"Shkn tunda ba za ki tsaya muyi Hira ba"

"Bayan kallo kake"

"No na ajiye system in, biochemistry Kika cika right?"

"Umyuk ko alqalam?"

"ABU Mana Yaya na fa ci jamb Ina Kuma waec Ina ma is good sosai"

"Great! Why not kizo muje Florida in saki makaranta Mai kyau, as brilliant as you are in Nan" dariya ta kwashe dashi don duk a tunanin ta Wasa yake.

"Nine abun dariya ko Asmeey?" Ya fada bayan ya Bata Rai.

"Sorry ka fa San ba Wanda zai Bari ai"

"Zasu bari Asmau your opinion matters first" ya fada Kan shi a kasa Yana Kallon wayan shi, har cikin ranshi ya nufin abinda ya fadan sai dai ita kwata kwata ba ta dago zancen nashi balle ta gane inda ya nufa.

"Yauwa! Kasan me ya mk? Naji Goggo Fulani na cewa ta maka Mata sai ka ganta so beautiful fara doguwa ga hanci Kuma tana da gashi ga..."

"Ya Isa Asmeey" hannu ya sa ya dakatar da ita "ta fada min ai am not interested infact ma ni ban son farar mace"

Zaro idanu tayi tana Kallon cike da mamaki "Daman farare naki Yan uwansu? Kaga fa ni tsoron fararen maza na ke gani nake Yan uwansu su ke so"

Shafa sajen shi yayi kafin ya gyara Zama don ko an tabo inda ya ke so "wa ya gaya Miki? Ni dai nafi preferring bakar mace they are more beautiful, da kike maganan maza ma kin fara kula samari ne?"

Saurin rufe bakin ta tayi "au ban fada maka ba? Ko ma da yake ummi ko Goggo fulani za su fada ma Amma please ka yadda ka auri ya Shaheeda she is so fine Allah ga ta da kirki." Hade rai Yana binta da harara "nace Miki ban so ko? Kuma ma wa ya gaya Miki Banda wacce na ke so" bude ido tayi in a dramatic way "Kai ya Mk da gaske, shine ba Ka taba fada min ba, I will like to meet her or her picture will even do" murmushi yayi Mai kayatarwa "karki damu kanwata za ki Santa kinji"

As clueless as she is sai washe baki ta ke tana ta zaro zance "Allah ya MK ban ma San kana kula Mata ba shiyasa fa da Goggo fulani tayi maka suggesting ya Shaheeda na amince da ita Ashe da naka. Am happy for you yaushe za a kawo Mana ita? Wait a Ina ma take, is she beautiful?"

"Wanne Zan amsa toh? A katsina take Kar ki damu soon za ki Santa and yes she is beautiful to me she is better than any other lady I used to know, she is just unique in my eyes."

"Lah lah lah Ya Mk in love, the lady is damn lucky"

"Sure?" Murmushi ya ke sosai har da rolling eyes in shi ita ko tsabagen murna squatting tayi tana Kallon shi. Nodding Kan ta tayi.

"Am lucky too Asmy, I will show you her picture so what about you are you ready to start a relationship?"

Kulle idon ta tayi cike da kunya ta tashi ta zille daga dakin Nan fa ta je tana sanar da Su Nabeela Ya Mk na da matar da zai aura. Joining inta su kayi akayi ta murnan za a Sha biki even though they are all clueless.

Shi ko gogon tana fita jawo katon hoton budurwar nashi yayi da ke cikin frame. Wani annashuwa ya ji na ratsa shi hade da farin ciki Mara misaltuwa idon shi har wani lumshe wa su ke yi. "I soo much love my lady" ya fadi Yana shafa Kan fuskan ta na hoton kace ita ce a gaban shi. As usual magana ya fara yi wa hoton Yana sanar Mata irin son da yake Mata, ba zai iya rayuwa ba tare da ita ba domin ko ita ce jigo... Weird isn't it?

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top