Chapter 5
Aadilah Ajlal
Short Story
This is a fictional story based on my imagination.
~ * ~
The whole book is dedicated to MaimunaAbdallah🥀
5
Special Thanks To Aadilah Ajlal Fans Club's 1&2 ....Your Comment's Are Highly Appreciated...❤️
~ * ~
"Wake up please Kitashi Dan Allah karkiyimin haka" haka Aadilah taci gaba da cewa jijjigata take iyakan karfinta amma koh alamun numfashi batayi..... Dakin ne yafara girgiza nan take Ammie ta bayyana dafa kafadarta tayi tace "Aadilah ba kuka zakiyiba tunfarko bata hakan zaki bude diary din a ka'ida saikinbi wasu sharudda nafarko dai yakasance kinajin tsananin sonta a lokacin, kuma hannunku yazamana yana hade ne sannan kuma shi wannan diary din ba a zuwa dashi koh ina acan inda yake ajiye tun farko zaki karantashi abu na karshe kafin kibude saikin tabbata kinyi kissing dinta...Yanzun dai hanya daya ce wadda zaki iya ceton ranta shine ta hanyar karanta diary din saboda haka yanzun kidauketa kuje can garden din acan yakamata ki karanta." hawayenta ta goge tace "Amma tayaya zan karanta alhalin tana cikin wanann halin? Nasan babu abinda Ajlal tafiso irin ta karanta diary din nan.." dafa kafadarta tayi tace "karki damu duk abinda kikace zatajiki ki hanzarta babu lokaci komi zai iya faruwa idan bakiyi sauri ba" daga haka ta bace bat.
Sosai Aadilah ke mamaki ganin garden din babu duhu saima wani babban gado wanda duk an zagaye gefensa da candles masu kyau sai kuma red flowers da aka zuba akai,,gefe guda kuma gawasu irin fairies kala kala suna shawagi asaman gadon, baki bude take kallonsu sosai hakan ya birgeta bata gama mamaki ba saida taga dukansu fairies din sun taso sundauki Ajlal sun kwantar da ita kan gadon...gefenta ta zauna sannan ta ciro diary din daga bag inta budewa tayi saidai wannan lokacin babu wannan hasken..kyakykyawan rubutu ne ya bayyana kamar haka:
AJLAL'S DIARY
22 October 1920
10:00pm
Dear Diary
"A person's destiny is everything that happens to them during their life, including what will happen in the future."
"Two soul's don't find each other by accident,They are meant to be..."
~ * ~
"Hakika duniya cike take da halittu mabanbanta kuma kowace hallita akwai yanayin datake rayuwa kamar dangin aljanu yanayin yanda suke rayuwa yana shige dana mutane tunda suna aure su haifa,kuma suna iya shiga cikin mutane suyi rayuwa saidai babu wanda zaice ga yanayin siffarsu saboda suna iya sanja kama zuwa mai kyau,muni dama sauran halittu,,kamar yanda bil adama suke soyayya suma sunayinta kuma wani lokacin ma harsuji sun kamu da son bil'adama wanda hakan ya sabawa tsarinsu,,, Kamar yadda acikin aljanu akwai masu tausayi,karamci,taimako,tsoron Allah,yawan ibada dakuma shaidanu suma haka a cikin mutane akwaisu."
"Kaddara ita ta hadani da bil adam wanda hakan bakaramin bazarana bane ba arayuwatah......"
"Duk da cewa duniya da dama da abubuwan mamaki ke faruwa a cikinsu batareda dan adam ya fahimci dalilin hakan ba Themyscira Island waje ne da mutane keyimin kallon manyan abubuwan mamaki ke faruwa a island din saboda tsananin hadarin wajen indai mutum ya shiga baya fitowa waje ne mai kunshe da hallitu iri iri waje ne daya ke dauke da mugayen bakaken aljanu, aliens, serpent, Island ne mai abubuwan ban mamaki wannan island mai abin al'ajabi tasamo asaline daga nahiyar kudancin africa(south Africa),"
"Ajlal Mahmoud Muhammad Shine cikakken sunana iyayena fararen aljanu ne kuma musulmai nikaina nasani inada tsananin kyau wanda kaf ciki nahiyar babu kamar ni wanann dalilin ne yasa dan sarkin aljanun lokacin yace yana sona yanzun haka ansa ranan aurenmu nanda wata uku bikin mu.... Acikin jinsin serpent akwai wata maisuna Malak itakuma tana tsananin son Yasar wanda shine sunan wanda zan aura saidai shikuma nikadai yakeso wannan ne ya haddasa gaba mai tsanani tsakanin familynmu da nata."
Tunda nike bantaba fita daga island dinmu ba kwata kwata banda sha'awar shiga cikin bil adam saboda sunada rauni basa ganinmu mu kuma da wanann damar muke amfani wajen cutar dasu...Hakan nan yau naji inason shiga cikin mutane naga yanda suke rayuwansu kozan dauki wani darasi akansu da wannan tunanin ta bi iska ta shiga can cikin sararin samaniya tana keta hazo...
Present Day
2:00am
~ * ~
FOUNTAIN ESTATE 2:00am
Dare mahutar bawa lokacine na kusantuwa zuwa ga Ubangiji amma fah ga wanda Allah yaso yayinda dawasu suna can suna aikin bacci.
"Wayyo Amah" haka kyakkyawar budurwan tace saikuma tayi saurin rufe bakinta da hannunta kwata kwata ta manta tsakiyan dare ne yanzun kara maida idonta tayi kan Laptop din dake gabanta gaba daya a tsorace take hannunta duka tasa takara rufe idonta THE NUN shine film din datake kallo.
ta shagala sosai wajen kallon dif wutan dakin ya dauke, saurin kunna torch light tayi amma taki kawowa, "wayyo Amah kitaimakeni" tace a hankali, dariya taji a gefenta cikin tsananin tsoro ta kalli wajen amma bataga kowa ba itakam Ajlal batasan ma tayi dariyan ba tunda take bata taba tunanin haka bil adam sukeda tsoro ba ita mamakintama saikace dole gshi tanajin tsoron amma kuma bata daina kallon ba dama haka mutane suke? gashi wani irin dadi takeji duk lokacin data kalleta matsawa tayi dab da ita ta hura mata iska take bacci yadauketa.
Washegari late ta tashi cikin sauri tashiga bathroom tayo alwala sannan ta gabatar da sallan asuba bata ko tsaya yin addu'a ba ta tashi ta cire hijab din sannan takara komawa bathroom din brush da wanka tayi a kalla ta shafe 40mns tana kallon kanta a madubi....
"Aadilah" Haka dattijuwar matar tace bayan ta shigo dakin cikeda bacin rai take magana "Wannan wani irin rayuwane kika zabama kanki anya kuwa kinada hankali? bakyajin tsoron kijama kanki matsala koh" turo baki tayi cikeda shagwaba tace "to Amah yanzun kuma wani laifi nayi?"
"Mene ma bakiyiba, Aadilah kinga kece kallon horrors film kuma dan balai sai tsakiyan dare natabbata jiya bakiyi bacci da wuri ba ga shegen kallon mirror anya lafiyanki kuwa?" Kara turo baki tayi tace "haba Amah ni wallahi nadauka ma wani abun nayi kawai fiction story ne babu wani abu makamancin horror a gaske Kuma nibanajin tsoron su ai"
Amah kanta ta girgiza "kedai ina rabaki kiwuce kije ki breakfast" fita tayi tana kunkuni.
~ * ~
Manage It Please
Thank You For Reading My Story
Khushi💘
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top