Chapter 19

Aadilah Ajlal
Short Story

This is a fictional story based on my imagination.

Dedicated To Maimuna Abdallah🥀

19

~ * ~

"Haka dai mukaci gaba da zama cikin mutane kowa muna zaune dashi lafiya bamuda abokin fada."

"Saidai makociyar mu tana yawan fama da rashin lafiya ta bari sunyi magani amma duk a banza yarinyan ta daya mai suna Ummi kuma har yau bata kara haihuwa ba."
Ganin yanda tadamu da son haihuwa yasani yin bincike anan nagano cewa matar kanin mijin tace take sata barin amma shiru nayi ban fada mataba saboda ba karamin mutumci sukeyi ba.

Yau ne ake bikin yar makociyarmu mai suna Ummi kasancewar gidan su yayi kadan shiyasa Maman Ummi tazo har gida ta sameni tace "idan babu damuwa zata kawomin wasu bakin su kwana a gidana ganin irin mutumcin da muke da ita yasa na yadda ashe dai wannan shine silan rabuwanmu dasu"

Aadilah Ajlal suka kalleta cikin fargaba sukace "shin menene yafaru dasu haka? Ammieh kaddai ace suma sun rasu?"

Kanta ta gyada tace "Aa ba rasuwa sukayi ba,bari kuji abinda yafaru a wannan daren."

"Kamar yadda kuka sani mu aljanu cikin dare muke sha'aninmu,bayan bakin sun kwanta nan fa nafara sabgogina saidai nagama komai sannan naje dakin da suke na kwanta ina kwanciya aka fara iska mai karfi saboda lokacin damuna ne hakan yasa kofar dakin da muke ciki budewa nikuma a lokacin nagaji sosai banson mikewa kawai saina mika hannu na take yayi tsayi haryaje ya rufe kofan sannan yadawo jikina ashe abinda bansaniba daya daga cikin bakin mai suna Maman jiddah ta farka kuma akan idonta komai yafaru."

cikin tsoro takoma ta kwanta jikinta yahau bari tana Allah Allah safiya tayi taje tafadama Mamn Ummi abinda yafaru.

Aikuwa washe gari kiran sallar farko ta mike wani irin kallo takemin mai cikeda tuhuma ina mata magana amma sam taki amsawa daga karshe ma da gudu tafice daga gidan ta shiga gidan Maman Ummi tana ihu da kururuwa nan fa yan biki suka fito suna tambayarta "lafiya wanene ya rasu?"

zama tayi tace babu wanda ya rasu nan fa wasu suka fara tsaki suna cewa "gaskiya Maman jiddah kinada matsala wallahi saboda Allah kawai ki shigowa mutane gida kina ihu da asuba din nan gaskiya kisanja hali sam wannan ba dabi'a tagari bace ba"

Itama tsakin tayi tace "to iyayen mita aisaiku tsaya kuji abinda zanfada wanda na tabbata idan kukaji saikun shiga rudani kamar yadda nima na shiga"
Zufa tagoge ta kalli Maman Ummi taci gaba da cewa "nikuwa Maman Ummi kinsan suwaye Maman Ajlal kuwa?"

Kallon rashin fahimta tayi mata tace "kwarai kuwa sama da shekara ashirin muna tare dasu mutane ne masu mutumci da karamci mene yafaru naganki duk a birkice"?

Hmm gyara zama takarayi tace "to gaskiya bakisan ainahin su suwaye ba wallahi jiya da idona naga hannunta ya mike yayi tsayi yaje ya rufe kofa lokacin da hadari yataso jiya kwata kwata banyi bacci ba saboda tsabar tsoro"

Gaba daya dariya suke mata suna cewa "Lalle Maman jiddah wato haryanzun kina nan da wannan karyan taki"? Maman Ummi tace ku tsaya kutsaya "Mekike nufi Mamn jiddah wato saboda kinga ina zaman lafiya da makotana shine zaki hadani dasu? to ni tunda nike basu taba nuna min wata alama ba don haka bazan taba yadda ba" kallon sauran mutanen tayi tace "kowa yaje yayi abinda zaiyi karya ce kawai irin ta Mman Jiddah."

Wani irin bakin ciki ne ya mamaye mata zuciya wato har ita za ayi disgracing a cikin mutane? Duk da tasan tanada karya amma yanzun ba karya take ba da idonta tagani tsaki tayi tace "gaskiya karya batayi ba saboda indai akayima shaidan makaryaciya to fa koda ace kafadi abu babu wanda zai yadda dakai" a fili tace "indai haka ne daga yau bazan kara yin karya ba"

Nan ta shiga tunanin hanyar daza tabi domin ganin ta tonawa Maman Ajlal asiri,ko babu komi mutane zasu yadda da abinda tace.

Wani murmishi tayi ganin tasamu mafita mikewa tayi taje ta kwanta domin sam jiya batayi bacci ba.

~ * ~

Da yamma gidan ya cika sosai ana zazzaune kowa yana harkan gabanshi nan fa Ajlal ta shigo gidan hannunta rikeda wasu kaya a cikin karamin akwati Wani murmishi tasaki ganin cewa abinda take shirin yi zaiyi nasara dama tun dazun take zuba idon ganin Ammieh ta shigo amma babu alamunta da sauri ta mike ta shiga kitchen karamin kasko ta dauko sannan taje inda ake girki ta debo garwashi cikin sauri ta ciro kullin magani tafara zubawa a ciki bangaren yan biki kuwa babu wanda ya lura da abinda takeyi saboda kowa harkanshi yakeyi.

Daidai lokacin Ajlal tafito daga dakin Maman Ummi shakar turaren tayi nan da nan taji kanta yafara juya mata sannan ga wani irin zafi datakeji tamkar ana zuba mata ruwan zafi wata kara tasaki nan ta zube a kasan tana ihu nan da nan sauran mutanen sukayo kanta Maman Ummi ma fitowa tayi tana cewa "lafiya Ajlal mene yasame....?" Saidai magananta ya makale ganin Ajlal kwance tana ta wani birgima gashi kamanninta sunfara sanja wa.

Maman jiddah kuwa wani irin farin ciki taji ganin cewa tabbas zata samu nasara,matsowa takarayi ta faki idon mutane ta kara zuba garin maganin a ciki..

Ajlal kam ganin irin azabar data keji gashi kuma ainahin siffarta zata bayyana hakan yasata bace wa bat... Ganin abinda yafaru yasa yan biki watsewa suna ihu da kururuwan neman taimako nan fa aka hau rige rigen fita daga gidan kowacce a kidime take gashi kofa tayi musu kadan... Maman jiddah kuwa kafin ta mike tuni jama'ah sun bi ta kanta duk anji mata ciwo.

Lokacin da Ajlal ta bayyana gaba daya jikinta ciwo ne nan ta zube a kasa tana maida numfashi Ammieh ce tace "Lafiya Ajlal naganki haka?,menene ya faru dake" duk cikin rikicewa nake maganan.. Cikin karfin hali ta fadamun duk abinda yafaru kaina dafe Ina maimaita kalman "Innalillahi wa inna ilaihir raji"un yanzun abinda zasuyi mana kenan? Ashe dama da gaskene mutane basuda Amana?  Nidai nasan duk iya zaman mu dasu bamu taba cutar dasu ba bari naje gidan" hannuna Ajlal takama tace "Aa Ammieh kibarsu karkije bazasu taba fahimta ba"

Batace komai ba tajuya ta fice daga dakin.

Bangaren yan biki kuwa ana can ana maida zance wasu suna cewa a kira mazan unguwa suzo su fitar dasu don zama dasu akwai hadari sosa.

Kallonsu Maman Ummi tayi tace "Hmm wannan abu da mamaki yake wallahi kuma fa tunda nike dasu basu taba nuna min wata alama ba ashe dai ta ciki na ciki gaskiya mugu baida kama"

Maman jiddah tace "keda waya gaya miki ana zaman lafiya da makota? Aeduk yanda kuke tabbas ta ciki na ciki yanzun badan Allah yakawo ni ba Allah ne kadai yasan irin abinda zatayi miki, ni nafi tunanin duk barin da kikayi kwanaki sune sila waya sani ma ko mayu ne"

Nan fa sauran yan uwanta suka shiga cewa "ba shakka zata iya yiwuwa tunda dama mai magani yace na kusa da ita ne suke yi mata hakan"

Daidai lokacin Ammieh ta iso wajen fuskanta cikeda bacin rai ta kallesu tace "Maman Ummi gaskiya kin bani mamaki ashe har zaki iya gani a gabanki a cutar da Ajlal amma ki kasa magana? Yanzun abinda kikayi kin kyauta kenan? Ni bansan me aka ce miki akaina ba amma kisani ni da zuciya daya nike zaune dake bantaba tunanin cutar dake ba"

Wata mai suna Umma tace "dama ta ina zakice hakan? Ko ji kike bamusan komai ba baiwar Allah nan kene kika kashe mata ya'ya sannan yanzun kinzo kina wani cewa da zuciya daya kike zaune da ita"

Wani banzan kallo Ammieh tayi mata tace "Hmm yaro yaro ne wallahi amma ina baki shawara ki iya bakinki don zakiyi nadama sannan a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe"

Cigaba tayi da cewa "Kekuma Maman Ummi kisan dawa kike zaune domin kuwa makashinka yana taredakai" tana gama fadar hakan ta juya.

Cigaba sukayi da hanayi.

Tana shiga takama hannun Ajlal nan tafara fadar wasu magic words take gidan yafara girgiza nan fa jama'ah suka bude baki suna kallon Ikon Allah domin kuwa gaba daya gidan ne yatashi sama tamkar wanda akasa hannu aka daga nan yafara tafiya a cikin iska...

AMDAZ MODEL INTERNATIONAL SCHOOL

2:00am

Kallon Su Aadilah Ajlal Ammieh tayi tace "dare yayi sosai yakamata kuje ku kwanta."

Cikin shagwaba Aadilah tace "Dan Allah kici gaba tunda nike bantaba jin labari mai tsuma zuciya kamar na Aadilah Ajlal ba"

Hannunsu takama duka su biyun tace "bazai yiwu nakarasa muku labarin yanzun ba saboda dare yaraba gashi kunada test gobe karku damu kunji yarana zan karasa muku"

Badan sun so ba suka mike bayan Aadilah takama hannun Ajlal saboda har yanzun bata dawo normal ba tana jin ciwo a kafanta, hanyar fita daga garden din sukayi saidai akwai duhu kasantuwar farkon wata ne gashi sam babu hasken farin wata, kafin su gama tunani sai ganin fairy's sukayi farare tass nan suka ci gaba da haska musu hanya har zuwa cikin hostel din nasu.

Lokacin da suka isa hostel din yayi shiru babu motsin komai haka dai sukaci gaba da tafiya har suka isa room dinsu  bayan sun kulle kofa sannan suka sa sleeping dress suka kwanta..

Aadilah ta kalli Ajlal tace "Ajlal kina ganin mune Aadilah Ajlal DIN DA AKA SAKE HAIFA KUWA?"

Thank you so much for reading my story.❤️

Please allow me to apologize for my late in update😂😂😂I'm so sorry lovelies....

💖

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top