Chapter 18

Aadilah Ajlal
Short Story

This is a fictional story based on my imagination.

Dedicated to Maimuna Abdallah🥀♥️

18

~ * ~

Ammieh taci gaba da cewa
"Bayan kwana bakwai da rasuwan Aadilah ina cikin gyara kayan Ajlal naga diary dinta kuma tunda nike bansan tana dawani diary ba, dauka nayi na karanta take jikina yayi sanyi jin irin abinda data rubuta a ciki gaba daya nadama nikeyi saboda na fuskanci soyayyan gaskiya suke ma junansu,

Anan nagane cewa......"Love doesn't have eyes, it doesn't go by race or gender. Love goes by how the person makes you feel. love is love you can't always help who you fall in love with.."

"Saboda ita kanta Ajlal batasan zata fara son Aadilah ba kuma destiny ita ta hadasu saboda sam sam Ajlal batason shiga duniyar mutane amma ranan sai gashi ta shiga,, kuma anan tafara ganin Aadilah."

Bayan na share hawaye na ina kokarin maida diary din naga wani irin duhu ya mamaye dakin zuwa lokaci kadan kuma komai yadawo normal ganin wata tsohuwa nayi rabin fuskanta a rufe da gashi kanta Hannunta ta miko min tace nabata diary din,

Cikin alamun rashin fahimta nace "akan wani dalili zan baki? kuma naga bakida wani hadi dani bare kice kema karantawa zakiyi?" cikin nutsuwa tace "nikaidaice zan iya kare diary din nan ki yadda dani saboda Aljanu da dama suna son mallakar wannan diary din bincike yagano cewa duk wanda ya mallakin diary din nan..." Girgiza kanta tayi tacigaba da cewa"bazan iya fada miki komai ba yanzun idan lokaci yayi zaki gane abinda nike nufi... "

Ganin yanda take magana cikin nutsuwa yasa Ammieh yadda da ita mika mata diary din tayi, tana karba tafara wata irin dariya take dakin yahau girgiza kallon Ammieh tayi tace "hakika kinyi kuskure saboda a binciken danayi nagano kina dauke da juna biyu kuma wannan yarinyar Ajlal ce zaki sake haifanta saboda tanason daukan fansa kuma tanason ganin ta mallaki abar kaunarta,kiyi sani cewa wannan cikin naki zai dau tsowan shekara ashirin kafin nan zaki haifo ta,saidai zata manta duk abinda yafaru a rayuwanta harsai ta karanta wannan diary din ne zata tuna komai,sannan wutar son daukan fansa zai ruru a zuciyanta,,tsananin son abin kaunarta zai karu zataji zata iya komai don ganin tayi wadannan abubuwan guda biyu... kin riga kisani soyayyan Ajlal forbidden love ne sam babu shi a al'adanmu hakama a addininmu."

Ita kuwa Ammieh kanta ya kulle tunanin shine ya akayi tasamu ciki? Alhalin rabon data haihu anfi  200yrs?

Kamar matar tasan me take tunani tace, "kibar wahalan dakanki wajen tunani domin kuwa kafin Merida tarasu ita tayi abinda za a sake haifan Ajlal kuma ta mallaka mata duka fairies dinta, idan har nayi wannan Ajlal bazata iya tabashi ba amma wadda takeso din zata iya saidai ita banida tabbas din za a sake haifarta kamar yadda zaki sake haifo Ajlal, amma tabbas wannan muradin shi zai sa kisake haifota" tana gama fadar hakan ta fice daga dakin.


Ammieh taci gaba da cewa

"saidai wannan matar ta shafe tsawon kwana dari  tana magic akan diary din Ajlal wanda saboda tsananin magic din datayi harsaida itama kanta bazata iya tabashi ba,, abinda nike nufi anan babu wani mutum ko aljanin dazai iya tabashi"

kuma tundaga ranan data gama magic akan diary din wani abun mamaki yafaru,

"Kamar yadda tace tabbas akwai masu bibiyan diary din saboda wannan tsafin datayima diary din angano cewa duk wanda ya mallaki diary din harkuma yasamu damar karanta wani page daga ciki zai shahara a duniya mutane da aljanu zasu zama karkashin Ikonsa,"

Manyan aljanu da bokaye sama da mutum dubu sun rasa rayuwansu a kokarin mallakar diary din,,,

Yau a cikin Island dinmu mun wayi gari cikin Al'ajabi saboda iyakar zaman mu a Island din Millions years ago babu hasken rana amma yau gari yayi haske sosai ga kuma rana kowa yana gani hakan ba karamin mamaki yabamu ba,nan akaje wajen chief na wancan lokacin domin kowa hankalinsa ba a kwance yake ba,
nan fah aka zauna ana neman mafita saidai hakan bai faru ba saboda wasu irin guguwa ne suka dinga fitowa cikin kankanin lokaci suka fara daga aljanu sunayin sama dasu,,,, nan fah kowa yahau gudun tsira da rayuwansu,, take ruwan daya zageje Island din yafara ambaliya nan ma aljanu da dama sun rasa rayuwansu,,

Bayan ruwan ya lafa saikuma aka fara ruwan kankara nan fah aljanu sukayi ta zama kankara...kuma a lokacin ne Ammieh ta dauki wannan dutsen da Merida tabama Ajlal tana daukan shi fairy's suka fito zagayeta suka farayi nan take idanunta ya rufe gaba daya.

Lokacin data bude idonta cikin wani daki ta tsinci kanta akan lallausan gado take mikewa tayi da sauri sam takasa tuna abinda yafaru jin muryoyi tayi daban daban mikewa tayi window ta bude nan taga mutane birjik kowa yana sha'anin gabansa.

wata pink fairy ce ta fito hannunta rikeda roban ruwa mikama Ammieh tayi bayan tasha ta zauna tana maida ajiyan zuciya sannan tace "nan kuma ina kuka kawoni mene yafaru da Island dinmu?"

"Nan duniyar mutane ce kuma Island dinmu babu wanda yayi rai saboda abinda yafaru shine.."  "A cikin bil adam akwai wani hatsabibin boka wanda yaje da niyar daukan diary din saidai hakan bata samu ba wannan dalilin shiyasa yayi amfani da magic don ganin ya tsarwatsa Island din  saboda yana ganin cewa gara kowa ya rasa ranshi tunda bai samu biyan bukatan shi ba."

Ammieh tayi kuka sosai jin yanzun batada kowa kaf danginta babu tarasa mijinta da yarta da yan uwanta da iyayenta.

Tundaga ranan yazama cewa wannan fairy's din suke dawainiya da Ammieh kuma tasake sosai suna muamala da mutane bata taba nuna masu ita ba mutum bace ba har tsawon shekara ashirin sannan ta haifo kyakkyawar yarta saidai batada niyan samata sunan Ajlal amma ga mamakinta lokacin da wata neighbor dinta tazo tana tambayanta ya sunan Baby saitaji bakinta yace "Ajlal..."


Kallon su Aadilah Ajlal tayi tace "to kunji ta yanda nasake haifo Ajlal..."

Maida kallon ta tayi kan Aadilah tace "yanzun kuma zan sanar dake yanda aka sake haifanki...."

"Kunsani dama cewa tsakanin mutane da aljanu shekarun mu ba daya bane ba, kuma munfi mutane tsawon rai nesa ba kusa ba...bayan wasu shekaru Ajlal ta girma sosai saidai har zuwa lokacin bata nuna wata alaman cewa tasan abinda yafaru d ita ba shekarun baya da suka wuce wannan dalilin yasa nasama raina cewa Ajlal ba sake haifanta nayi ba wata daban ce kawai kamanninta ne irin na wancan Ajlal din."

Aadilah tace "Ammieh kinada pictures din su Ajlal?"

Diary din ta dauka rufe idonta tayi tafara karanta wasu magic words take pictures din su ya bayyana guda uku, guda biyu daga ciki a Island din ne dukkansu suna dariya saikuma wanda Aadilah tayi hugging waist din Ajlal amma ta juya bayanta sai kuma na karshe wanda dukkan su ranan anyi musu tattoo.... mika musu diary din tayi tace "ga Aadilah Ajlal nan saidai tsohon pictures ne"

Pictures din suke kalla cikeda da mamaki right now they're speechless...

~*
Hello lovelies hope everyone is doing just fine...don't forget to vote and drop your comments!

KhushiAblahNMJMssCEO💖

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top