Chapter 13
Aadilah Ajlal
Short Story
This is a fictional story based on my imagination.
Dedicated To Beautiful Soul Maimuna Abdallah🥀
13
~ * ~
AJLAL'S DIARY
20th January 1923
12:00am
Dear Diary
"Let us run away, somewhere far"
I want to run away with you.
where there is only YOU and ME.
Tu me manque mon bébé ,d'amour je t'aime fort fort fort."
~ * ~
"Aadilah meyasa bakyajin magana ne? Yanzun kenan kinason nunawa mutane cewa ban isa dake ba koh? Yanzun abinda kikayima yaron nan Sadiq kin kyauta anaki ganin koh? wallahi ko mutuwa zakiyi saikin auri Sadiq kinji ma nafada miki gara kicire komai aranki bari kiji ko gawarkice sai an kaita dakinsa rana ita yau.. Babu abinda zai sa afasa auren nan saboda na lura don kinga ina biye miki shiyasa kikeyin yanda ranki yaga dama to nina haifeki bawai kene kika haifen ba.. maza kitashi yanzun nan yana can dakin baki yana jiranki saura idan kinje kimasa rashin kunya nikuma zakiga matakin dazan dauka akanki."
Mikewa tayi tadauka hijab tasa sannan ta nufi dakin bakin...ciki ciki tayi sallama yana zaune akan daya daga cikin kujerun parlourn fuskanshi dauke da murmishi ya amsa mata gawani sassanyan kamshi yana tashi a jikinsa yau ne karon farko da Aadilah tafara kare masa kallo yana sanye da jallabiya royal blue sai fuskanshi datasha gyara kyakkyawa ne ajin farko yanada nutsuwa da kamala duk lokacin dayake magana murmishi yakeyi wanda hakan yake kara masa kyau......saidai kassh duk wannan abubuwan daya tara ko sau daya bai taba birge Aadilah ba,,, Yanzun ma wani kallon banza take masa bata ko gaidashiba tace "Mallam kayi sauri kafadi abinda ke tafe dakai saboda inada abin yi kowani minutes na rayuwatah yanada muhimmanci bana bata lokacina a banza."
Murmishi yayi wanda Aadilah ta lura halin sane hakan maimakon ya birgeta take takarajin tsanarsa a ranta tana cewa munafuki sai wani murmishi yakeyi kodan ba laifi ya hadu kadan..saurin kawar da zancen tayi...Daidai lokacin yafara cewa "Haba gimbiyatah aiyakamata kibari mugaisa koh,,,,Gashi ko ruwa baki bama bakon nakiba." Tsaki taja tace "lalle kuwa zaka mutu baka sha ruwa ba indai harsaina baka sannan zakasha Mallam bari kaji nifa bana sonka kuma bazan taba sonkaba saboda tunda kashigo rayuwatah aka rabani da farin cikina koda munyi aure bazaka taba samun kwanciyar hankaliba ina rokon Allah yadauki rayuwatah kafin auren nan saboda babu kyau mutum yakashe kansa amma da tuni nadade da aikata hakan Sadiq idan har kanada zuciya ka hakura da aurena kace kafasa." kukane yaci karfinta takasa karasa abinda zata ce..
Shikuwa ido kawai ya zuba mata.
Duk da wani bangare na zuciyanshi yayi masa nauyi saboda maganganunta amma aiyaji ana cewa ita mace duk yanda takaiga kin mutum indai yana kyautata mata,wata rana wannan kyautatawar zata danne wannan kiyayyar amma bashida tabbas akan wnn zancen saboda zai iya zama gaskiya kokuma akasin hakan.
Smile yakarayi yace "Aadilah duk naji abinda kika ce amma kisani bazan iya cewa nafasa wannan auren ba saboda inasonki kuma ina kaunarki sannan banason abinda zai bata zumuncin iyayenmu kuma banason mutumcinki ya zube saboda duk macen da akace anfasa aurenta ana saura sati daya tabbas mutane zasuyi tunanin wani abu daban Aadilah kije ki tunani nidai nasan ina sonki tun ranan dana fara ganinki kuma inason kizama abokiyar rayuwata wadda mutuwa ce kadai zata rabamu sannan nayi miki alkwarin cewa zan koya miki sona zanbaki kulawar dake kanki zaki soni wanda hakan zaisa duk wasu lokuta na rayuwanki zakiso kiyisu atare dani my last word shine you'll definitely fall in love with me." yana gama fadar hakan yafice yabarta nan baki bude.
Tafiya takeyi amma sam hankalinta baya jikinta kwata kwata batada kwari dakyar takai kanta dakinta kuma tunda tashigo parlourn mutane akafa fara tsokananta ga amarya ga amarya wani irin bakin ciki taji ya rufeta da sauri ta nufi dakinta bayan tasama kofan key kan gado tafada taci gaba da kukanta.
Babu abinda datake cewa sai "Ajlal kizo gareni kekadai nike bukata a yanzun,please Ajlal kizo I need you!" saboda a lokacin kwata kwata ta manta da wannan zoben na hannunta kwanciya tayi a haka bacci ya dauketa.
~ * ~
Wedding Préparations
Sosai gidansu Aadilah yacika da mutane yau saura kwana daya daurin auren kuma kullum cikin kuka take duk wani events da Amah ta shirya gaba daya yatashi a banza tunda sam Aadilah taki zuwa kuma koda anzo anayi mata make up kuka takeyi saidai mai kwalliya tagaji tadaina saboda hawayenta yaki tsayawa yanzun ma tana kwance zazzabi ya rufeta,Amah ce tashigo dakin hannunta rikeda fresh milk da P.C.M (paracétamol 😂😜nasan Halinki Neesha nah saikice baki ganeba)
"Aadilah tashi kisha magani"...
"uhm uhm Amah bazan iya shaba." cikin nutsuwa tace "haba Aadilah kintaba ganin marar lafiya yaki shan magani? Oya tashi yanzun nan kisha wannan nasan bakici komai ba idan yaso saikisha maganin" babu yanda ta iya haka ta amsa tafara sha bata wani sha dayawa ba ta mika mata tace ta koshi maganin ta bata tana kuka tana komai haka ta karba tasha dama haka take batason magani ko kadan...
Kallonta tayi tace "yanzun Aadilah bazaki saki ranki ba ko...kinason nunawa duniya cewa auren dole zanyi miki koh?" Hawaye taci gaba dayi tace "Amah ki hakuri nima kaina bansan meyasa nakasa sakin raina ba amma nayi miki alkwarin zansaki raina daga yanzun bazan kara kuka akan wannan auren ba."
hawayen Amah tashiga goge mata sannan tace "haka nikesonji Aadilah kuma da sannu zaki fara sonshi ninasan Sadiq zai kula dake zaibaki farin ciki kawai abu daya nikeso dake kisaki ranki ayi bikin nan lafiya kinji" kanta kawai ta gyada domin jitakeyi kamar zuciyanta zai tarwatse "yawwa Aadilah Allah yayi miki albarka" murmishi ta kirkiro tace "amin Amah nagode sosai kuma ina rokon Alfarman kiyafemin duk wani abu danayi miki kinji" hugging dinta tayi tace "babu komai na yafe miki.."
Washe gari karfe takwas Amah tashigo dakin hannunta rikeda wasu kaya mikawa Aadilah tayi tace gashi wannan sune wanda zakisa yanzun saiki hanzarta saboda mai kwalliya tazo gashi kuma 9 daidai za a daura auren kinsan dai anason amarya ta shirya da wuri kallon sauran yanmatan dakin tayi tace su koma daya dakin saboda tafi sakewa wajen shirin....wasu daga cikinsu ba haka suka so ba domin sunfi son ta shirya agabansu badan ransu yaso ba suka fice aka bar Aadilah ita kadai...Amah ce tace ta tashi tashiga wanka zata dawo damai yin kwalliya din...
Daure da towel ta fito tana tsaye gaban mirror tana goge jikinta kamar ance ta dago taga Ajlal tsaye a bayanta da sauri ta taho wajenta gani tayi taja da baya cikin alamun damuwa tace "Ajlal lafiyanki kuwa yau kuma gudu na kike" kallonta tayi tace "sam bana gudunki Aadilah saboda a kullum burina shine nakasance taredake...Aadilah muddin kina tareda wannan zoben a hannunki bazan iya matsowa kusa dake ba inason ki cire wannan zoben daga hannunki saboda ko yanzun ba karamin daurewa nikeyi ba jinake kamar zan kone." Kallon zoben tayi kuma yau shine karo na farko dataji tanason cirewa batareda tunanin komai ba ta cire ta bude wata karamar jaka tasa zoben a ciki da sauri ta matsa kusa da ita tayi hugging dinta tana cewa "I missed you so much sweetheart"......I missed you more darling,zame jikinta tayi tace "Aadilah Let's run away somewhere far."
Aadilah:"Are you crazy Ajlal..?"
Ajlal:"I'm in love with you,can anything be crazier Aadilah?"
Aadilah:"I want to run away with you,where there is only YOU and ME,,,amma Ajlal bazan iya ba yau ne ake daurin aurena..mekikeson mutane zasu daukeni wani irin hali kike ganin Amah zata shiga Ajlal musamu wata hanyar amma banda wannan sabod." bata karasa ba taji tace "Je suis désolé" sannan aka sa mata abu a hanci a hankali taji idanunta sunyi mata nauyi tun tana ganin dishi dishi har tadaina ganin komai.....
~*
Enjoy reading!☕️📖
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top