Chapter 10
Aadilah Ajlal
Short Story
This is a fictional story based on my imagination.
Dedicated To Maimuna Abdallah🥀♥️
~ * ~
10
~ * ~
AJLAL'S DIARY
16th March 1921
12:30am
~ * ~
Take maganganunta suka fara dawo mata "I hate you so much you are a witch,monster." wata irin kara tafara mai firgitarwa idanunta gaba daya yakoma fari fat babu koh alamun baki a ciki mikewa tafarayi akan iska tana fadar wasu magic words.. Take farcenta yakara girma da tsayi idanunta yafara zubar da hawayen jini wata irin guguwa aka fara gawani irin gurnani yana fitowa daga cikin guguwar.. Take wasu irin dodanni suka fara fitowa siffarsu kadai idan mutum ya kalla take zai haukace saboda tsananin muninsu kallonsu Ajlal tayi cikin wata irin murya tace "destroy them all." saidai kafin tayi wani yunkuri taji wata irin iska ta dagata sama duk iyakar kokarinta takasa fitowa daga cikin iskar....suma wadannan dodannin iskace tayi sama dasu gaba daya suka bace.
Ahankali take bude idanunta gabanta ne yayi wata irin faduwa ganinta kwance akan gadonta amma duka hannayenta da kafafunta adaure da katuwar sarka, bata gama tunani ba taji alamun bude kofa Daadah ne ranshi a matukar bace kallon tsana yake jifanta dashi karasowa yayi cikin dakin yace "wato abin naki harya kai haka koh? Bakisan cewa tsakaninmu da mutane babu cuta ba cutarwa ba?meyasa kodayaushe burinki ki batamin rai? Saboda wani banzan tunaninki zakije ki kashe wadanda basuda laifi Ajlal haryau ke yarinya ce naga alamun bakisan komai ba akanki dakuma zuri'arkiba bari nabaki wani dan labari wataqilan zakigane abinda nike nufi." Zama yayi gefen gadon yafara cewa
~ * ~
"Shekaru kusan dubu dari bakwai dasuka wuce anyi wani takadarin boka maisuna Zankas a lokacin kaf duniya babu wanda yakaishi karfin sihiri saboda tsananin karfin ikonsa hatta mu aljanu a karkashinsa muke baisan mene tausayi ba babu abinda yafiso irin yaga mutane da aljanu nayi masa biyayya....yanada mata guda 15 saidai kaf cikinsu babu wacce ta taba koda bari ne gashi a lokacin yana tsananin bukatar haihuwa saidai yayi bincike yagano cewa bazai taba samun haihuwa ba harsai ya auri aljana kokuma wata halittar daban wannan dalilin ne yasa yashigo cikin Island dinmu wanda a tarihi shine mutum nafarko daya fara shigowa shima saida yashafe kwana arba'in yana yunkurin shigowa amma yakasa,daga karshe dai yayi nasarar shigowa lokacin daya shigo kowa mamaki yakeyi take wasu samarin aljanu su 10 sukayo kanshi da niyar kasheshi saidai kafin su karaso yanuna su da hannunsa take wani irin farin hayaki yafito wuta takama jikinsu suka fadi kasa matattu bayan sun kone kurmus,ganin wannan abinda yafaru ya firgita duk wata halittar dake cikin Island din...kananun halittu suka fara guduwa domin tsira da rayuwansu."
Dariyan mugunta yafara ganin duk sun tsorata kallon su yayi cikin tsawa yace "banzo da niyar cutar dakuba saboda ni daku inason mu kulla alaka mai karfi suma wadannan samarin aljanun fusata ni sukayi kodan suna tunanin cewa sukadai ne masu karfi koh to ni nan nafi duk wani aljani iya sharri ina mai tabbatar muku da cewa duk wanda yaki bin umarnina kamar ydda wadan nan suka zama toka kuma haka zaku zama daga karshe ina neman duk wani shugaba acikin halittun dajin nan suzo zamuyi magana ta fahimta idan kuma kunki tabbas fushina zai tabbata akanku" yana gama fadar hakan ya fara tafiya akan iska bai sauka a ko inaba sai wani tsauni wanda ko su aljanun bakowane yake iya zuwa ba saboda hadarin wajen.
ganin abinda yafaru yasa kowa jikinsa yin sanyi take aka yanke shawaran kawai aje aji dame yazo don daga ganinsa anga shaidanin mutum sunsani indai sukace zasu bishi ta karfi lalle asaran rayuwa zasu jama kansu..
Bayan kowane shugaba yazo nan aka tafi wajensa baki bude suke kallonsa ganin shiba a sama ba kuma ba a kasa ba kafafunsa suna lankwashe hannunsa kuma yadaura akan cinyarsa idanunsa a rufe...yana fadar wasu magic word... Saukowa yayi ya kallesu saiya kara kecewa da dariya saida yayi mai isarsa sanann yayi shiru...Kallon Ajlal yayi yace "kinsan abinda yafaru kuwa ranan?" Kanta ta gyada kawai saboda ta matsu taji cigaban wannan labarin dama a cikin mutane akwai hatsabibai wanda har zasu iya juya aljani..? Tambayan datakeyima kanta kenan.
Daada yaci gaba da cewa "bayan yagama dariyar saiya kallesu daya bayan daya yace nasani halittu iri daban daban ne har guda dubu daya a cikin Island din nan amma ya akayi naga baku cika hakan ba babu mutum daya ina shugaban jinsin Fairies???" kallon kallo aka shiga saboda kowa tsoron bada amsa yake..ganin shirun yayi yawa yasa Zankas daka musu wata irin tsawa wanda saboda tsananin karfin tsawan saida Island din gaba daya tayi girgiza ruwan daya zagayeta yashiga ambaliya wanda a tarihi tun kafuwar Island din ruwan kogin bai taba irin hakan ba...wani dattijon aljanine daga cikin jinsin serpent yafito "yakai wannan hatsabibin bil adam kayi sani cewa duk irin karfin ikonka tofah wannan ya fika yace bazai zo ba bazai yiwu ba ace wani karamin bil adam ya shigo har cikin duniyarsu yayi masa izgili ba...yace indai harkai ka isa Kuma kana takama da tsafi saidai kaje ka sameshi." ran Zankas ne yayi balain bacci lalle zai nuna masa cewa shi acikin aljanun ba komai bane ba baiko kalli inda sauran suke ba yatafi wajen shugaban fairies din..
~ * ~
Lokacin daya shiga wajen a zaune ya tarar dashi kan kujera amma hankalinsa baya jikinsa shikuma da wannan damar Zankas yayi amfani cikin sanda yake tafiya harya isa bayansa take ya dauke magic wand dinsa sannan yafito da wata knife baiyi wata wata ba ya caka masa daidai lokacin ita kuma Marah tashigo dakin wani irin gigitaccen ihu tasa jefar da akushin hannunta tayi ganin babanta kwance cikin jini da gudu tazo tafada kanshi tana wani irin kuka mai ban tausayi...shikuwa Zankas tunda ya dora idanu akanta yaji duk duniya babu wadda yakeso sai ita kuma zaiyi komai don ganin yasameta...itama daidai lokacin ta fuskanci akwai wani a wajen dagowa tayi ta zuba masa ido binsa take da kallo saboda yau ne rana ta farko data fara ganin irin wannan halittar, idanuntane ya sauka akan knife din dake hannunsa wani irin ihu tasa sannan ta shakeshi tana cewa "you..you killed my father, and now I'm going to kill you..beast.." ganin tana neman jimasa ciwo yasashi kwace hannunta da karfi shikanshi yayi mamakin irin karfinta juyawa yayi ya fice daga dakin wajen sauran jama'ar yafita yace musu abinda yazo nema yasamu wato matar aure kuma yar shugaban fairies zai aura shiru wajen yayi saboda kowa yasani saura kwana biyu bikinta tsawa yadaka musu yace "shifa ba amincewarsu yake nema ba kota halin yaya saiya aureta koda kuwa ace gawarta za a kawo masa."wani jibgegen aljani ne yafito yace "kai bil adam karya kake baka isa kazo har cikin mu kake juyamu son ranka ba,ni nan dakake gani nizan auri Marah kuma duk duniya babu wanda ya isa hanani aurenta saboda kafin nasamu damar aurenta saida nayi fada da aljanu dubu bazai yiwu ba kana karamin kwaro kace zaka rabani da masoyiya taba karyan aljani bare kuma kai bil adam bar ganin ana raga maka bawai tsoro bane ba." Wata irin dariya Zankas ya busheda ita kallon shi yayi yace "Kai aljani karka cika baki domin ni nan dakake ganina nawuce duk tunaninka idan kuma kana musu kazo mu fafata idan yaso sai a fidda gwani." Nan aka basu fili yayinda wasu suke cewa karyayi fada dashi domin rasa ransa zaiyi a banza.
~*
Feel free to leave your comments! Don't be shy😂💔
Khushi💘
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top