TAKWAS
Dakyar Zeenah ta samu ta lallaba ta koma cikin daki, kukan ma kin zuwa yayi tsabar yadda zuciyarta ke mata ciwo kamar ranta zai fita. Bakin ciki ne tarin takaici, ji take inama taje ta samu Bilal ta zageshi tas ko ta rage radadin abunda ke damunta. Amma kuma bata shirya shanye wata bulala hamsin din ba, dan Badarun can ko digon imani babu a tattare dashi. Gara Baba, duk balai idan ya mata sha wani abu yake kyaleta.
Dole taje tayi wanka tana fitowa ta dauko kur'anin ta ta fara karatu, dan ta yadda cewar babu babbar asara a duniya daya wuce mutum yayi hadda amma ya nemeta ya rasa. Duk rintse duk wuya zaka samu Zeenah na muraji'a. Ko aya biyar lafiyayya batayi ba bacci ya dauke ta, a nan yadda take zaunen. Sai can cikin dare ta farka ta gyara kwanciyarta.
Haka rayuwa ta cigaba da zuwar masu. Sai tayj sati biyu bata ganshi ba, bawai kuma dan baya cikin gidan ba, Aa fitowa ce kawai ma bai cika yi ba. Wani lokacin idan takaici ya isheta saidai tayi tsaki tace, "Allah ya wadaran naka ya lalace. Wai ace anyi namiji amma kamar mace?" Tasan yana jinta, duk yadda zatayi ta janyoshi yazo suyi rigima ta sani, amma koda a gabanshi zata furta wata maganar kallon banza bata isheshi ba balle na arziki.
Ita duk wannan al'adar ta zuwa gaida wata Fulani bata yinta, saboda har yanzu tana nan rike da abunda ta mata, duk ita taja aka daura mata aure da wannan mugun mutumin, ai da hanzu tana gidansu, kuma tasan kila da yanzu Mama baya mutu ba, tunda bakin cikin abun ne yaja har zuciyar Mama ta buga ta rasu. Kuma dadin dadawa ko Allah ya gafarta batace mata ba. Duk kallonsu take daya bayan daya.
Wata biyu kenan da zuwanta gidan har an shiga cikin sati biyu. Wata biyu kenan da sati biyu. Zata iya irga zuwan da tayi bangaren Fulani baifi ukku ba. Shima kuma duka sakawa take ana kiranta. In taje babu umm babu umum. Indai ta gaidata saidai su gaji da zaman haka Zeenah ta taso ta taho bangarenta.
Yamma nayi ta shirya ta nufi bangaren Fulani, zuciyarta fes, amma kuma kiris take jira ai mata ta zazzage mutum da masifa. Kamar kullum taka ta iske Fulani zaune a haraba tana shan iska. Zama tayi saman faffadan carpet din ta gaidata. Yau daga gani Fulani yan wulakancin takeji dan saida ta dauki mintuna kafin ta amsa ta. Daga haka kuwa koya yayi shiru sai can Fulani ta gyara zamanta.
"Malama Zeenah, rashin yawan shigowar da bakyayi yasa bakisan duk wasu dokoki na masarautar garin nan ba. Yau wata biyu da sati biyu da aurenku da Yarima Bilal, banji labarin ance kinada juna biyu ba. Kuma mu a ka'idar gidan nan idan so samu ne to washe garin ranar mukeso ki nuna mana cewar kefa ba juya bace." Da isa da takama da kuma igzilanci Fulani take magana.
Shekeke Zeenah take kallonta har ta dasa aya. "To sannu Fulani, inace dai kin gama ko? To bari kiji, aidai sai ka kwanta da namiji zai iya maka cikin ko? To bamu kwanta ba balle naga ko zan iya daukan cikin wancan murmudadden mutumin. Idan maganar kenan ni zan wuce, dan wannan maganar bata da amfani a wajena. Idan haihuwa kukeso ga mata nan da yawa a auro mashi."
Wani murmushin mugunta Fulani tayi, "Ke Zeenah ni kike fadawa wannan maganar?"
Tsaki tayi ta mike tsaye, "To bazan fada maki ba, Fulani? Kina magana kamar wacce take cikin duhun jahilci? Idan ma ace Allah ne bai kawo haihuwar ba fah? Sai ku dora karan tsana a kai na ko? Ni ba yarda zan ba, nace maki ku aura mashi wata indai a matse kuke da haihuwar." Tana fadin haka ta saka takalmi ta juya tabar bangaren baki daya.
Sallar maghrib tayi tana zaune tana jin haushin kanta, meyasa ma bata gayama Fulani maganganun da suka fi wannan zafi ba? Wannan abun ma ai iskanci ne. Taya zaace wai wata biyu aka baka kayi ciki? Ashe ma a ruwa ake sha. Salama taji, da kamar bazata amsa ba sai kuma ta mike ta nufi bakin kofar. Dogarawa ta gani su biyu fuskar nan babu imani.
"Ranki ya dade, umurnin Fulani zamu bi. Tace a tafi dake gidan yari tsawon kwana biyu sannan a miki horo mai tsanani." Wata shewa Zeenah ta saki tana kallonsu.
"Wa zaku taci dashi gidan yarin? Uban wani na kashe ko dan wani? Kai dallah ku fita ku bani waje." Har ta juya zata koma ciki taji an rikota, ashe tare suke da mace dan dama sunsan tabbas sai Zeenah ta basu matsala.
"Kiyi hakuri ranki ya dade, amma babu wanda ya isa ya tsallake umurnin Fulani a masarautar nan." Daga haka Zeenah tanaji tana gani suka fara janta waje, ko kafin su karasa bakin kofa sai ga Bilal ya shiga kanshi a kasa ko kallon inda baiyi ba.
"Barka da shigowa Yarima. Umurnin Fulani ne akan mu tafi da ita gidan yari har tsawon kwana biyu tare da horo mai tsanani. Ayi mana aikin gafara." Ya tsaya yaji abunda suka furta, amma kuma daga nan tafiya ya cigaba dayi ko kallo daya baima Zeenah ba. Tunda taga haka ta sadakas, dama tana saka ran kodan darajar auren dake tsakanin su yasa a saketa amma taga ko kallo bata isheshi ba.
Dan azaba kuwa tasha ta har illa masha Allah. Duka babu irin wanda ba'ayi mata ba. Da ruwan zafi ake tadata da safe, aiki taci aiki kamar jakar kano. Cikin kwana biyun nan saida Zeenah ta rame tayi baki kirin kamar ba ita ba. Gashi Fulani ta hana abata koda kwayar shinkafa saidai ruwa. Duk burinta bai wuce kwana biyun nan su kare ba dan tasan hukuncin da zata dauka akan Fulani. Dan wallahi bazata kyaleta haka ba.
Bilal ne da Isma'il zaune cikin wajen shakatawar dake bangaren Bilal. Isma'il ne yake masifa kamar bakin shi ya fadi kasa. "Abunda nakeso ka gane Bilal ba fa wai dan waccan yar iskar yarinyar zakaje ba, Aa saboda matsayinta na matarka. Fulani nema take ta tozartaka. Ta gidan ubanwa aka taba kai matar Yarima gidan yari tare da horo mai tsanani? Kashe rai tayi ko me? Dallah malam in zaka tashi kaje ka nuna ka isa da masarautar nan ka tashi!" Ran Isma'il yakai kololuwa wajen tashi, shi dan ta waccan yarinyar a ajeta sai shekara ta zagayo, amma lura da yayi da Yariman akeso a tozarta.
"Laifi ta mata, kafi kowa sanin rashin kunyarta." Abunda ya furta kenan ya dauke kanshi ya mayar kan waya.
"Da tayi mata laifin sai akace ta kaita gidan yari. Kai nifa damuwata ba waccan yarinyar ba, mutuncin ka da aka zubda cikin masarautar nan. Kai ka sani wallahi, ka barta ma tayi sati. Indai an tashi ba Zeenah za'ace ba, saidai ace matar Yarima Bilal." Isma'il yana fadin haka ya tashi ya fita daga bangaren gaba daya. Shi har ya hango shi Fulani tama wannan iskancin, wallahi koda bai san matar sai anyi bala'i.
Yarima yana zaune a wajen yaga shigowar Zeenah, har wani tangadi take kamar zata fadi, saida ta kawo karshen inda bango yake ya zama dole tayi tafiya ita kadai ta fara wani luu tayi can tayi nan. Yana kallonta har tazo zata fadi, kamar wanda aka tsikara haka ya mike cikin hanzari ya karasa inda take, rigib kuwa ta fada a jikinshi.
Dukda zai iya kirga kallon da ya mata a rayuwarshi, amma yasan ta chanza. Har fatar jikinta tayi duhu sosai. Ta rame kuma daga gani horo mai tsananin da aka mata hada mugunta ciki. Daukarta yayi ya nufa dakinta da ita. Dakyar take numfashi, iyakar galabaita ta galabaita. Doctor din da yake duba gidan sarki ya kira, ba'afi minti talatin ba ya shigo gidan.
Duba Zeenah yayi sannan ya saka mata drip. Magunguna ya bawa Bilal akan ya tabbatar tasha sannan kuma a bata abinci mai gina jiki. Tunda ya fita Bilal yake tunanin ina zai samu wani abinci shi kam? Shi bai iya girki ba, kuma duk kuyangin dake masarautar nan bai yarda dasu ba. Karshe dai Isma'il ya kira ya saka akayi girkin mara lafiya ya bawa driver ya kawo.
Sai can wajen goma na dare ta tashi, a hankali take bude ido tsabar azaba. Drip din dama guda daya ne har ya kare, dagowa tayi tana kallon Bilal. "Zan shiga toilet," ta furta a hankali da muryar marasa lafiya. Tunda yake bai taba jin muryarta can kasa ba idan ba yau ba.
Drip din ya cire mata kafin yada tanada niyyar mikewa, shi baisan ya akayi ba kawai dai tausayi ta bashi. Zuwa yayi ya mikar da ita tsaya har saida ya kai ta bakin toilet din, "Kiyi wanka, doctor ya bada ointments din da zaa shafa maki a jiki." Daga kai kawai tayi ta shiga toilet din.
Yasan yadda ake warming abinci, dan haka kitchen ya nufa yayi warming abincin. Shi tunani yake yadda za'ayi da shafa magungunan nan, dan kuwa jikinta duk yayi rodi rodi alamar duka, idan ba' shafa ba abun zai zama tabo. Shidai a yadda yaga yanayin ta bata iya komai. Ya zaiyi?
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top