Page 33
*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_
Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHARJAY* @wattpad
Page 33
Washe gari haka ta yini sukuku kamar Mara Lpy Bayan Ba komai ke damunta ta ba sai damuwa maganar Sulaiman da Faty ta mata jiya duk itace ta saka ta cikin wannan yanayin tabbas idan tace bata ji tausayin Sulaiman ba tayi karya sai dai bata so zuciyarta ta kai ta zuwa ga abunda bata yi niya ko kuma tace baza ta taba iyawa ba hakan yasa ta yakice abunda take ji a zuciyar ta ita kanta bata San wane irin so ne take ma Sulaiman ba sai dai duk da haka zata hakura dashi ta cigaba da addu'a Allah ya zaba mata abunda yafi alkairi.
Gaba daya a gajiye suka fito daga exam din da sukayi na Bio 402 karkashin wata bushiya suka samu suka zauna a gossip chair Faty tace "ki wuce kawai ni zan shiga exam din Chem 210"
Afeefah ta sauke ajiyar zuciya tace "toh shikenan dama wlh na gaji amma dai kin shirya ko?"
Dariya Faty tayi tace "hmmm bazan ce ehh ba dan ban San ya abun zai kasan ce ba kawai kimin addu'a dan wlh bana son spilled over"
Afeefah tace "insha Allah bama zaki samu ba ai ba wahala indai kinyi kara......" maganar ta ta makale ganin Sulaiman a gaban ta in non second bugun zuciyar ta ya Kara karfi fat fat kawai yake da kyar ya rufe bakin ta tayi kasa da kanta gaba daya jikinta rawa yake kamar mazari duk sai ta rude ganin haka yasa Faty kamo hannunta dai dai kunnenta tace "clam yourself pls" mike wa tayi zata bar gurin yayi saurin shan gabanta tare da dukawa sai kawai kuka ya kwace mata, gaba daya Sulaiman sai yaji wani iri sai yaji dama bai zo ba da ace yasan zatayi kuka idan ta ganshi sai dai ba yanda ya iya dole ce ta kama dole yazo ya nemi yafiyar ta kodan samun sassaucin abunda yake ji a zuciyar sa.
Cikin murya mai matukar rauni da nuna tsantsar dama ya fara magana "Afeefah" yanda ya kira sunan ta ya saka ta yin shiru tare da dago da kanta dai hawaye ta gani suna zuba daga idon sa kawar da kansa yayi daga kallon ta ya cigaba "nan dan da Wace kalma zanyi amfani gurin neman yafiyar ki ba hakika ni azzalumi ne kuma macuci tabbas na cancanta a kira da wannan sunan badan komai ba sai dan abunda na aikata maki wanda a sanadiyyar haka nima Allah ya jarabceni Afeefah wlh nayi nadamar abunda nayi miki har cikin zuciya ta dan girman Allah badan hali na ba ki yafe mun na kasa samun nutsuwa a zuciyata na zama mai rauni bana iya yin komai gani nake kamar Allah fushi yake dani Afeefah a sanadin abunda na aikata maki Allah ya jarabce ni bazan sake haihuwa ba sanadin accident din da nayi ranar dana baro gidan ku."
Share hawayen sa yayi yace "ina mai neman yafiyar ki dan Allah karki ce aa badan halina ba dan Allah"
Girgiza kanta ta fara yi tana matsawa baya tare da nuna sa da yatsan hannun ta tana son yin magana amma ta kasa bakin ta ya kasa furta ko kalma daya Faty ta riketa cikin sanyin murya tace "karki manta ko Allah muna masa laifi ya yafe mana Afeefah kar shedan ya yaudari zuciyar ki ga aikata aikin lada kar abunda ya faru yasa ki kasa yafewa bawan Allah ki kalle sa har kasa ya duka cikin nuna nadamar abunda ya maki yake neman yafiyar ki ban San ki da wannan zuciyar ba Afeefah ban sanki ba karfa ki manta shine mahaifin yar ki idan ta girma ta San abunda ke faruwa da wane ido kike tunanin zata kalle ki zata ji zafin ki na rashin yafe wa abbanta da bakiyi ba kiyi tunani a kai" tana kawai nan ta sake ta tare da nufar kujerar ta dauki Jakarta ta wuce abunta.
Share hawayenta tayi cikin dakiya tace "Allah ya yafe mana gaba daya" wata irin rahama yaji ta saukar masa ajiyar zuciya ya sauke da karfi har Afeefah ta juyo ta kalle sa hawaye ne ke bin kuncin sa fuskar sa dauke da murmushi wanda ke nuna tun daga cikin zuciyar sa yake fitowa "ban San da wane irin baki zan gode miki ba wlh kin gama min komai sai dai kawai na biki da addu'an gamawa da duniya Lpy hakika ke ta dabance ko a cikin mutane Allah ya maki albarka".
Wani sanyi taji har cikin zuciyar ta ko mai ta tuna kuma sai ta wuce da sauri tana share hawaye mike wa yayi yana smiling har cikin ransa yake jin wani dadi na lullube shi a hankali ya furta ""at long last ta yafe mun dis girl is just different......uhhhhh" wani huci ya fitar sai kuma yaji bai ji dadi ba yanzu mata kamar wannan ya saka gaskiya ya tafka babban kuskure a rayuwar sa.
Motar sa ya shiga ya mata key ya bar skl din.
Afeefah kuma Bayan SLT ta samu dama gurin shiru ba mutane zama tayi a gurin sai da tayi kuka har sai da kanta ya fara ciwo kana tayi shiru ta ciro pure water a Jakarta ta wanke fuskarta, sai yanzu ma ta tuna bata karba key a hannun Faty ba dan haka she has no option din da ya wuce ta bi skl bus.
.....................🦋
Fu'ad kuwa sosae Siyama ta tada rigima ganin da gaske yake auren zaiyi dan gashi nan har an fara gyara part din da daddy ya ajiye wa Faruk akan shima idan ya girma sai ya zauna a nan har ya samu nashi idan kuma baya ra'ayin tashi daga gidan sai ya cigaba da zama haka ma har a birnin kebbi an fara gyara gida. Shi kuwa ba dan komai yaji ya Kara son auren ba sai dan abunda Siyama ta masa duk da dai yasan ba son Afeefah yake ba amma yanda mommy ke gaya masa halinta yasan tasu zata zo daya kuma bai San me Allah zaiyi nan gaba ba wata kila ya fara sonta..................
Kuyi hakuri kunji ni shiru kwana biyu abubuwa ne sun saka ni gaba ga skl preparation da exams and insha Allah page kadan ya rage mu gama just keep praying for me dan Abinda nafi bukata kenan a yanzu.
#TeamFu'ad
#TeamSiyama
#TeamAfeefah
#TeamSulaiman
*Lioness👑*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top