Page 30
*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_
Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHARJAY* @wattpad
Page 30
Bayan ya fita daga ɗakin mommy wurin aikin sa ya wuce direct yana tunanin maganar da sukayi da mommy, furzar da iska yayi akan labbansa yace "Allah ya zaɓa min abinda yafi Alkhairi"
Haka kawai yau da don zuwa gida Afeefah ta tashi sai dai baza ta iya cewa mommy tana so ta koma ba amma tana son ganin yan uwanta tayi missing dinsu sosae, ɗaukar Ammi data gama saka ma kaya tayi suka fice cikin shirin su da alama dai fita zasu yi a parlour suka tarar da mommy itama ta shirya cikin atamphar data sha ɗinkin doguwar riga. Kallon ta ta maida kan Afeefah dake fitowa yanzu haka kawai taga ta mata kyau har ta kasa rufe bakin ta sai data furta "wow daughter kinyi kyau sosae" dariya Afeefah tayi tace "kema haka mommy baki ganki bane kamar ba bake kika haifi yah Fu'ad ba kin ganki Kamar waheedah" dariya mommy tayi tace "wane waheedah kuma zaki maida Ni yarinya"
Dariya Afeefah tayi tace "Allah kuwa mommy"
Fu'ad dake tsaye bakin ƙofa yayi sallama basu ji ba ya saka shi tsayawa yana kallon su sai dariya suke jin abinda Afeefah tace wai kamar ba mommy ta haifeshi ba sai abun ya bashi dariya ya ɗan yi murmushi ya samu guri ya zauna, sai a lokacin suka kula dashi Afeefah tayi ƙasa da kai mommy ta kallesa tace "kaji Abunda Kanwar ka ke faɗa ko?"
Murmushi kawai yayi mommy tace "Afeefah duba ki gani me su waheedah ke yi har yanzu basu fito ba zan fa tafi na barsu"
Ajiye Ammi tayi tace "bari na duba" bedroom ɗin su ta nufa Fu'ad kuma ya dauki Ammi yana mata wasa yarinyar tayi kyau sosae cikin atamphar ta irinta Afeefah sai dai ita a jikin white vest ɗin ta aka jera pattern ɗin atamphar mai zanen flowers aka kawata sa da stones Sai dan wando karami shima na atamphar da ribbon na butterfly Shima duk na atamphar sai kamshi take zubawa.
Fitowa waheedah tayi tana saka wrist Watch dinta tana mi ta "wlh dai Adda Afeefah da kin bari na ƙara sa shirya wa kalli fa ko fuskana ban duba ba dana yafa game" Afeefah ta tabe baki tace "kanki ake ji haka akwai ku bata mana lokaci har da wannan yarinyar" ta faɗa tana nuna Husna dake turo baki dankwali a hannu sai da waheedah ta gama saka wrist Watch din ta ta Saka breatles dinta Husna tace "Adda wahee dan Allah ɗaura min" karɓar tayi tace "ai duk Addah Afeefah ce" ita dai Afeefah bata ce komai ba ta zauna kusa da mommy dake duba wayar ta bata kula zancen su waheedah ba kara sowa cikin parlour sukayi suka gaida Fu'ad kana suka zauna waheedah ta kalli mommy tace "mommy Nikam Sai yaushe ne Habeebah zata dawo gidan nan Allah na gaji ga wannan hutun coroner din daya ƙi karewa"
Mommy ta maida wayar ta a jaka tace "soon Ai kun kusa resuming Dan Naji ana cewa 5th October"
Waheedah tace "yafi ma"
Kallon ta ta mai da kan Fu'ad tace "ita siyama bazata je bane?"
Yana saɓa Ammi a kafaɗar sa yace "ehh sai gobe wai"
Tabe baki tayi tace "toh Allah ya kaimu" mota suka karasa Husna ta shiga gaba Mommy waheedah da Afeefah kuma a baya. Gidan wata cousin sister din mommy dake zama Abuja ake bikin suna hakan yasa suka shirya gaba ɗaya banda siyama data ce baza taje ba.
Ashe siyama na bakin window tsaye daga party ɗin ta tana kallon lokacin da su mommy suka fito ga Ammi a hannun Fu'ad sosae ranta ya sosu gashi Afeefah tayi kwalliya tayi kyau sai kishi ya rufe mata ido taji kamar ta shaƙo Afeefah a gurin sai da suka fice kana ta bar bakin window ɗin tana tsaki.
.................. 🦋
An sallami Sulaiman daga asibiti dan yaji sauƙi sigar ba abinda ke damun sai a fili sai dai a baɗini damuwa ce fal zuciyar sa bai san cewa yana son Afeefah son da ko kansa baima irin sa ba sai yanzu yasan wane mataki Afeefah ta taka a cikin zuciyar sa ya yanke wa kansa shawarar zaije gidan su ya bata hakuri ya nuna mata yayi nadama koda zata taimaka masa ta dawo garesa.....
Hmmm malam sule anya Afeefah zata yarda kuwa🤔⛹️♀️⛹️♀️
..............💜
Bayan kwana biyu mommy ta kuma yima Fu'ad maganar Afeefah sai dai bai ce komai ba abinda ya sani ya barma Allah zabin sa though yana jin abu game da Afeefah sai dai san ko menene ba yasan dai yana tausaya mata amma shi bai shirya ma auren ba bai san how will Siyama react ba Dan yaga alamun bata son Afeefah basa shiri, furzar da iskar bakin sa ba ya mike yana addu'ar Allah ya zaɓa masa abinda yafi Zama alkairi.
Yau kam ta yanke shawarar zuwa ta samu mommy dan gsky tana so taje gda idan yaso bayan kwana biyu sai ta dawo, a parlour ta samu mommy tana gyaran zogale Fu'ad da siyama kuma suna duba abu a laptop ɗin sa sai dariya take shi kuma yana smiling jitayi Ina ma bata fito ba yanzun ma kawai dan sun ganta ne data koma.
Zama tayi kusa da mommy tana faɗin "mommy sannu da aiki zogale zamu ci yau?". Ta faɗa tana murmushi mommy tace "ehh yayan ku ne ke so" bata ce komai ba ta saka hannu tana taya ta gyara kamar zatayi magana kuma sai tayi shiru lura da hakan ne yasa mommy tace "Lpy kamar bakin ki da magana" .
Ɗago da kansa yayi ya mata kallo ɗaya ya maida kansa Afeefah tayi murmushi tace "dama mommy ina so naje gida ne kwana biyu nayi missing aunty"
Dariya mommy tayi tace "kice soyayyar mahaifiyar ki ce ta motsa"
Dariya tayi tace "mommy kenan kawai ina missing gida ne nasan Abbana ma nason ganina"
Mommy tace "iyye kaga daddy's girl" dariya tayi siyama dake jin su kuma ta taɓe baki tana addu'ar Allah yasa ta tafi a ƙasar zuciyar ta. Fu'ad kuma baice komai ba yi yayi ma kamar besan abinda suke yi ba, mommy ta kalli Afeefah tace "yaushe kike don tafiya" tace "within this week Dai mommy"
Mommy ta kalli Fu'ad tace "yayan su sai ka saka ranar komawar ta idan yaso sai ka Naya bucking flight" Sai a lokacin ya ɗago da kansa ya kalli mommy tare mai da kallon sa kan Afeefah da farin cikin zuwa gida ke shimfeɗe a fuskar ta kasa daina kallon ta yayi hakan yasa tayi ƙasa da kanta Siyama kuma kamar ta kama da wuta tsaki kawai tayi ta fice daga parlour fuuuuu kamar iska da kallo suka bita gaba ɗaya mommy ta girgiza kanta kawai Afeefah kuma ta ɗauki bowl din zogalen ta tafi dashi kitchen bata san me Fu'ad din ya cewa mommy ba ta shiga haɗa masa zogalen ba jimawa sai gata ta fito daga kitchen din hannunta dauke da bowl sai plate da spoon kusa da mommy ta ajiye ta koma ɗauki dan ta fara jin kukan Ammi maybe ta tashi daga bacci ne.
Da dare Waheedah ta taya ta haɗa kayanata dan ranar Laraba zata wuce kuma yau Monday Sai farin ciki take zata je gida..........
*Sorry guys zanyi rushing due to resuming din da za'ayi Skl but I promise you that still my book will be so sweet and Romantic. I need your prayers Dan Allah ku tayani da addu'ar ku yan uwa sbd exams zan fara i seriously need it prayers plssssssssssssss*
#TeamFu'ad
#TeamAfeefah
#TeamSulaiman
Vote
Comments
Share
*Lioness👑*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top