Page 27

*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_

Written by *NEESHAR.JAY*

*NEESHEJAY* @wattpad

Page 27

#Accident

Da sauri mutanen dake kan titin suka fara zuwa gurin motar sa rolling kawai take bata tsaya ko Ina ba sai daya daki wata bushiya nan aka fara kokarin taimaka masa ganin ya fito duk da wasu na cewa kila ma ya mutu haka dai suka ciro sa gaba daya ba kyan gani gaba daya fuskar sa tayi damage ga jini sai zuba yake kamar an bude tap jikin Sa kam ba'a cewa komai dakyar ka gansa kayi tunanin bai mutu ba idan ma yana raye to dakyar yayi tsawon rai sbd raunin daya ji. Kowa sai tofa albarka cin bakin sa yake akan wannan lamari wasu suce kila shaye shaye yayi wasu kuma ba haka ba kowa da abunda yake cewa da kyar aka samu wani bawan Allah ya dauke sa sai asibiti saboda irin jinin da yake zubarwa Emergency aka shiga dashi drs na kokarin ganin sun bashi taimakon gaggawa .

Da sauri ya daga ta cak ganin bata numfashi fitowar Waheedah kenan daga part din Hajja ta gansu a haka da sauri ta karasa tana tambayar Lpy ko kallo bata samu ba ya saka ta a mota ya zaga ya shiga itama Waheedah da sauri ta shiga gaba ya tada motar ya fita in a high speed bai tsaya ko Ina ba sai hospital da kansa ya kuma daukota zuwa cikin asibitin nurse ta kawo bed aka dora ta suka shiga ciki da ita, doguwar suma ce tayi hakan yasa Bayan ta farfado suka kara mata ruwa a lokacin har Waheedah ta kira yan gidan su ta sanar masu kan kace kwabo sun kwaso sun zo ganin haka yasa Fu'ad tafiyar sa Bayan ya bama Waheedah sakin da mommy ta basa ya kawo dama abunda ya kawo sa gidan kenan.

Bata farka ba sai kusan magrib sbd allurar baccin da aka mata dr da nurse ne suka shigo dakin nan kowa ya fita dr ya shiga dubata Bayan ya gama rubuce rubucen sa ya fita a kofar daki ya tarar da Ukasha yace one of them ya same sa a office aunty da Ashir ne suka bi Bayan dr din da suka isa office ya fara masu bayani Bayan sun zauna "hjy kuna aikin me ciwon zuciya yake neman hallaka yar ku?" Zaro ido tayi cike da tashin hankali tace "ciwon zuciya kuma dr" yace "yes" yah Ashir yace "toh dr me yayi causing wannan cutar" a takaice yace "damuwa" jinjina kai Aunty tayi yace "damuwa ta mata yawa wanda hakan yake neman hallakar da ita sai dai alhmdllh da sauki sosae sannan kuma idan har zata kiyaye shan drugs dinta insha Allah zata samu Lpy yanzu bari na muku prescribing sannan kuma dan Allah ku sakata a gaba ta gaya maki abunda ke damunta kuma tana bukatar kulawa sosae dan haka sai kun dage duk abunda zai bata mata rai a gujesa hjy" Aunty tace "insha Allah" prescribing yayi masu ya basu suka fita suna masa godiya.

Fu'ad Bayan ya koma gida ya gayama mommy abunda ya faru ba shiri ya fara shirye shiryen tafiya asibiti itama driver ya kaita.

•••••••••••••••••••••••🦋

Sulaiman gaba daya baka gane hallitarsa ko shiga gurinsa ba'ayi sai dai ka gansa through glass din jikin kofa or window yan gidan su gaba daya sun zo haka ma Atika kallo daya zaka masu su baka tausayi especially Atika data fice hayyacinta lokaci daya gaba daya an rufe kansa da bandage haka ma kafarsa da hannun sa sosae zai baka tausayi sannan kuma idan ba wani ikon Allah ba da wuya ya tashi irin wannan ciwo haka.

Washe gari dr ya bama Afeefah sallama suka kwasa suka koma gida aka cigaba da jinya dukda Ba wai zaka gane akwai cuta a tare da ita ba sai dai ta rame gashi duk ta tuna ita bazawara ce sai kuka ya kwace mata har cikin ranta take jin zafi a yan shekarunta har ta zama zaura duka duka shekararta nawa ne haka yake shan kuka har ta koshi Aunty tayi tayi da ita amma kamar kara tunzurata take ga abinci da bata ci sosae duk ta kara komawa wata silent yan gidan su kowa son yake yaga ya sakata Farin ciki suna kokarin kyautata ma haka ma mommy data ki komawa acewarta sai yarta taji Sauki sosae sai su dawo tare tuni Waheedah suka koma sbd fu'ad yace bazai zauna shi kadai a gidan ba idan ya fita aiki matarsa fa harda kuka Waheedah tayi sbd sunyi hutu a skl sai dai suyita zaman gida gashi ba wani shiri suke da seeyama ba har dai yanzu da mommy bata nan bata San ya wannan zaman nasu zai kasance ba.

Bayan sati biyu mommy ta kada kan Afeefah ta tasata a gaba suka tafi Abuja tare acewarta maybe damuwa zata rage mata haka suka tafi ita da Ammi cike da kewar yan gidan su.

Sulaiman kam har yau bai San inda kansa yake ba kullum cikin allurar bacci drs suke masa sbd karya farka zai fama ciwon sa gashi brain dinsa na bukatar hutu sosae dan ta sanyi cracking kadan.


Manage🥺🤧

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top