Page 26
*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_
Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHEJAY* @wattpad
Page 26
#Neeshar😂
Shigowar Afeefah tare Ammi a hannunta ne ya saka shi sauke boyayyar ajiyar zuciya ya mike tare da talkies har gabanta ya saka hannu zai karbi Ammi tayi saurin kaucewa tare da daga masa hannu tace "dakata malam abinda kafi tsana da kyankyami a duniya ne zaka taba" ajiye hannun sa yayi tare da sunkuyar da kansa kasa ya koma ya zauna zama tayi itama cikin kosawa tace "Lpy? what do you want from me again?" Cikin cool voice yace "am sorry" ajiye Ammi data fara bacci tayi tace "you're too late to say so just go directly to what brings you here" kallon cikin ido yake mata gaba daya tsantsar tsana kawai yake iya hangowa daga idonta duk son da take masa ya rikide ya koma zallar kiyayya har wata wutar masifar dake cikin zuciyarta yake iya hangowa cikin ransa ya tambayi kansa anya Afeefah zata yafe masa kuwa irin wannan rigimar da bai shiryawa zuwanta ba yake hangowa cikin idonta, kawar da Kanta tayi gefe tana daukar Ammi tace "sai anjima" da sauri ya tare ta ta hanyar kire mata hannu wani irin uban kallo ta wurga masa daya saka shi sakinta ba shiri yace "dan Allah kiji kaina wlh na tuba" wani murmushin takaici tayi tare da girgiza kanta tace "Ka manta lokacin da nake rokonka wannan kalmar a lokacin ko kallon rahama ban samu daga gareka ba ballantana na saka ran zaka min afuwa ka manta lokacin da kake dukana kamar jaka Ka manta irin walakancin da Kamin a baya lallai zuciyar ka Sakarya ce dahar ta iya yaudarar ka akan zan yafe maka ko makiyana kayi wannan abun bazan bashi shawarar ya yafe maka ba ballantana ni daka aikata a kaina na tsane Sulaiman bana sonka bana son ganinka jin irin wannan suna tada min hankali da nutsuwa yake yi me yasa kane ma ka kuntata ma baiwar Allah da bata ji ba bata gani ba badai ku maza kuna ganin mata ba abakin komai suke a gurin ku ba hmmm idan ka shirya bani takarda na daga nan zuwa jibi ina jiranka" juyowa tayi ta watsa masa idonta da suka nemi zautar dashi saboda canza launin kalar da sukayi zuwa ja saboda wutar dake cin zuciyarta tace "idan ba haka ba ka kira kiran alkali na barka lpy" tana fadin haka ta fice abunta wani marayan kuka nason kwace mata tayi saurin saka hannu ta rufe bakinta bata karasa cikin part din Aunty ba ta tsaya gurin flowers sai da tayi kuka mai isarta kana ta wanke furkarta a tap din gurin ta shige ciki.
Sulaiman gaba daya ya rasa idan zai saka nutsuwar komai ya kwance masa ba abunda kwakwalwar sa ke tunano masa irin kalmar tsana data fito daga bakin Afeefah dakyar yaja kafafunsa ya fice daga gidan a wannan daren ikon Allah ne kawai ya kaisa gida, gaban Atika ne ya fadi ganin sa a birkice kamar wanda ya tabu jijiyoyin kansa sunyi rudu rudu sun fito idon sa kamar garwashin wuta.
_______________________🦋
Washe gari da safe da wani matsanancin ciwon kai gaba daya Afeefah da sulaiman suka tashi dashi shi akan rashin samun baccin da baiyi bane ga zuciyar sa dake barazanar faso kirjinsa ta fito.
Afeefah kuma kukan data yine kafin ta kwanta ya sakar mata ciwon kai sai dai tana shan magani ta dan samu relief.
Kiran yah Ashir ne ya shigo wayarta hakan yasa ta ajiye shafa man da take tana tunanin Lpy ya kirata as early as this morning picking call din tayi ta gaida shi ya amsa cike da kulawa yace ta fito yana parlon Abba tace toh ta kashe wayar.
Bata bata lokaci ba ta shirya ita da Ammi suka fice zuwa parlon Abba batayi tsammanin ganin Sulaiman ba hakan yasa mamaki ya kamata sai ta shanye mamakin ta ko a fuska bazaka gane ba ta samu guri ta zauna tana gaida yayyinta yah Ashir ne ya fara magana da cewa "Ba wani abu bane ya tara mu anan sai nemarwa yar uwar mu yan cinta da take nema a gurin mijin ta fatan kuma za'a bata wannan yancin nata" sosae hankalin Sulaiman ya tashi Afeefah kam ko a jikinta saima gyara ma Ammi gashin kanta da take Adda Maryam tace "gsky ne Ashir toh Sulaiman kaji dan haka ya paper da biro idan kuma a gaban alkali ka shirya rubutawa duk you're wlc" gaba daya ya daburce cikin sarkewar harshe yace "amma ita Afeefah haka ya zaba" da sauri ya dago kanta tace "ehh" wani murmushi yayi yace "idan har hakan zai saka ki farin ciki zan barki Afeefah amma dan Allah ki yafe min duk abunda na maki wlh na tuba karkiyi sanadiyyar jefani wani hali kinga ko Allah muna masa laifi ya yafe mana na rokeki dan Allah ki yafe min" a karon farko da dingon tausayinsa yaso tasiri a ranta da sauri ta kawar da tunanin bata ce komai ba Ukasha ya Mika masa pen and paper din hannunsa na rawa ya karba yana kallon Afeefah ko zai ga ta chanza ra'ayinta sai dai irin kallon data ke binsa da shi ne ya saka shi dauke kai ya rubuta mata sakin ta daya yana sharar kwallah.
Duk da ita ta nemi sakin da kanta amma hankalinta yayi mugun tashi da gudu ta mike tare da fice daga parlon tana kukan da yayi sanadiyyar daukewar numfashin ta ta tafi luuuuuu kasa zata fadi yayi azamar tare ta ta fada a hannun sa.
Sulaiman kuma mikewa yayi gaba daya baya gani sai hada hanya yake yi kamar zai kifa tsabar duhun da yake gani a idosa yana shiga mota ya mata key da gudu ya fice daga gidan kadan ya rage bai bugi gateman ba badan yayi saurin kauce masa ba. Sharara gudu kawai yake yi mutane na basa hanya ganin irin gudub da yakeyi bai kula da wata trunk dake zuwa ba gashi driver din sai uban horn yake amma Ina gaba daya hankalin sa baya jikin sa kalamar tsanar da Afeefah ta furta masa kawai ke masa yawo a brain jikake kiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiittttttttttttt.
*Table don shake o* 🥂
Bari nayi nan kar #TeamSulaiman suyi sama dani a nameni a rasa😂🏃🏻♀️🏃🏻♀️
#TeamAfeefah
#TeamSulaiman
Vote
Comment
Share
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top